Chapter 30
Chapter 30
shine dalilin da yasa muke nan din ba?, muna kamasu mu gurfanar dasu a kotu domin karbar hukunci daidai da abinda suka aikata_ _Tsawon wanne lokaci ake dauka kan a kammala yallabai?_ Wannan matashin ya fada cikin sigar tambaya shima. _muna Iya kaiwa tsawon wata biyar ko kuma ma shekara_ _Kafin xuwan wannan lakacin taya kake Iya bacci?,No bana Iya baccin to yallabai_ Yayi maganar cikin tsananin fushi. _Nima wannan shine dalilin da yasan nake ta bibiyar Tanbuwal, duba wadan nan duka sun aikata manyan laifiku!, duk kuma Wanda ke a cikin wannan kundi suma a kashe su kenan?_ Ye jefawa matashin alamar tambaya. _Kashe sun shine daidai yallabai idan har muka kare ADALCI to daga nan ne shima ADALCIN saiya zama me bada KARIYA a garemu!_ Daga nan Video'n ya yanke. ”Inspector KAMAL RANO kenan, matashin dake aiki da dukkanin rai da zuciyarsa a jihar kano!. Shi din marayane A karamar hukumar kano yake a garin RANO baya da uwa baya da uba dangin duka mahaifansa sun wofantar dashi. Yanzu haka yana zaunane a garin kano anguwar sharada” Wani dan banzan murmushi ak ya saki kafin cikin muryar nan na no nonsense ya furta. ”ina bukatar ganinsa a cikin week din nan” Daga haka ya mike yana barin wurin, bedroom ya shigee shi kuma zayd ya bar dakin baki daya. Bayan sun tattauna wasu muhimmam abubuwa daga baya. *LAGOS* ~Meerah~ Sanye take cikin shigar atamfa chiganvy coffee colour ta ɗora dogon shimar din ta har kasa. Sake kallonta salman ya yi a karo na biyu ganin yanda ta haɗe rai. "Meerah" Ya kira sunanta batareda ta kalleshi ba ta amsa da ”na'am” Wani gauron numfashi ya sauke sai kuma ya furta. ”Naga kamar baki saurarena ai a irin wannan lokacin kamata yayi ace zallar farin ciki kadai za'a gani tattare dake, amma da dukkan alamu ko saurarena ba kiyi bare ki fahimceni ma” kallonsa tayi da manyan idanunta masu cike da wani irin kwarjini sai kuma ta dan tabe baki tace ”Ai naga kunnene ki ji kuma ina jinka ko ihu kakeson nata yi kwararo² titi² ina fadin ina jinka?” numfasawa ya sauke kafin ya furta ”shikenan na baki lokaci kije kiyi tunani da kanki ina fatan za ki yanke shawara mai kyau, kasancewar saura nan da watanni mu zama Ma'aurata” Wani shegen kallon ta wulla masa yi tayi kamar zata yi magana sai kuma kawai tayi shiru ta juya tabar wajen kawai, domin a ganinta wannnan tsayawa ja'in jar ma aiya sami arzikinta kenan. Domin a ranta take jin Wannan auren ba tabbatacce bane. Gefen lips Inshi yadan ciza kadan tare da furzar da numfashi yasan ya shige ajin yarinyan, Bama don ya kadaitu da ita ba har ita wacece da zata dinga wulakanta shi....... *BY AMMEY LAYLERH *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page 31&32 ”Amma dai ba har kin dawo daga firan ba Meerah ba?” Disha ta tambayeta ganin har ta dawo ga ran nan haɗe babu ko sassauci. Rabuwa da ita tayi taki tanka mata, ita kuma ganin ta mata banza ne ya sanya fadin. ”Haba meerah bakison mutumin nan kawai ki fito fili ki fadama su baffa fine!, amma shi haɗe ran na mene kinsan dai ba maganin damiwa zaiyi miki ba?" Wata yar karamar kwafa taja tare furta ”wlh idan har bai yi a hankali ba sai na yi masa rashin mutunci nifa banson irin haka, na gaji da wannan takurar haka nan haba!” ta karashe maganar a tsawace. ”So sorry meerah kiyi hakuri kici gaba da kaima Allah kukan ki, Insha Allah zai duba lamuran” Nooding kanta tayi tana jingina da jikin duguwar kujerar palonsu. Nan suka ci gaba da firansu amma sama sama, domin meerah bata jin kanta a cikin mood me dadi. Washe gari da misalin karfe Biyar da Rabi na yamma Meerah da disha ne zaune jingune da roiler din dake harabar wurin. Meerah ta dan dubi Rolex watch din dake hannunta ganin shida na kokarin karasawane. Ya sanya ta mikewa tana fadin. ”Inaga lokacin tafiyana yayi zan wuce bye Sis” ”Laaaa kinga ma motar ya Ayaan ta shigo kizo saimu sauke ki gida!” Cewar disha, Tafiyanta taci gaba dayi ba tare data dakata ba tana gyara zaman bag din dake rataye a shoulder nata cikin muryan no nonsense ta furta. "I m so sorry Sis to kar kice wani abu please zan fita bakin gate na tara napep then nasan ma Wannan uban yan nacin na dab da shigowa." Saurin juyowa disha tayi ta kalleta tabbas idan da sabo yaci ace ta saba da halin meerah, saidai ta gaza sabawar har zuwa yanzun. Parking car din da ayaan yayi a gabansu ne ya katse maganar da disha take shirin yi. ”Yen mata barkanku da hutawa ku shigo mu wuce” ya fada yana sauke glass na motan. Gaba kawai ta wuce ta bar disha tsaye, domin meerah bata magana biyu kuma dama ta tsani ayaan din Sabo da masifar kallonta da yake yawan yi. Dan bata fuska disha tayi tare da shigewa cikin motar ta rufo murfin da karfi. Ta gaban ta suka wuce bayan ayaan ya sake mata tayin shiga amma ko kallo be isheta ba. Idanunta ta dan lumshe a hankali kuma saki wani dan murmushin da ya bayyana akan fuskarta. Ganin yadda fuskar mutuniyar ta tayi taki ko kallar inda take lokacin da suke wucewa. Tasan cewar hakan da disha tayi alamane dake nuna cewar tayi fushi da ita kenan. Ci gaba tayi da tafiyanta har takai bakin gate din fita daga gidan jaridar, haka ta ringa ratsa manya manyan motocin dake wurin. Tafiya takeyi amma gaba daya duk bata jin dadin yanayinta amma ko a fuska baka Isa gane yanayin da take a ciki ba. Hango wani me napep yana zuwa ne kuma yasa da sauri ta soma daga hannu tana son tare mai napep din. Cikin sa'a kuwa ya tsaya cikin yanayin dan hanzarinta ta yunkura da niyar shiga napep din.wata arniyar Rolls *R* Rayce ta danno kanta, wacce kiyastin kudinta a dalar amurka yake daidai $25,000. kamar ance daga idonki sukayi 4 eyes da duk da yau din ma idonsa rude yake da blue shade. Wani dan banzan kallo ta cilla masa tare da murguda bakinta, kafin can cikin kasan muryarnta irin na tsiwan nan ta furta. {MARA GASKIYA DAI KO A RUWA GUMI YAKE}. Fadawa cikin napep din tayi tayi sai kuma ta shiga furta kalmar ”La ilaha illa anta's subhanaka inni kunti minazzalin!” A bayyane domin zuwa yanxu dai tasan wannan mugun wani abun yake sake nufi da ita.... ”Malam nace don Allah kuwa kasan wancen mutumin na cikin motar cennnnnñ?” Ta fadi da kokarin nuna masa motar, saidai me? Sama, kasa, haka ta nemi motar ta rasa. ”Hajiya wacce motar fa?” Muryar dan sahun ya farkar da ita. Ijiyar zuciya ta sauke tana fadin ”muje kawai anguwar dadin kowa zaka sauke ni farkon layi!” Ta fada tana me sake kallon inda taga motar da yake ciki. "To Hajiya zaki biya 400" Me napep din ya fada yana kallonta. Nooding kanta kawai tayi batare kuma da ta nemi ya rage mata ba, ta bude bag
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54