Chapter 40
Chapter 40
suke saboda tsananin kyau da tsafta, Saida ya sake ɗaukar wasu sakannin kafin ya zuro dukka jikinsa zuwa waje. Zara zara yatsun hannunsa ya sanya yana qoqarin cire wayar dake maqale a kunnensa,kyakkyawar fuskarsa mai cike da wani irin kwarjini haiba da cikar zati a dinke tsaf babu alamun fara'a ko kadan tattare da ita. Kyakkyawar soft fatar jikin san nan me murjajjen jiki da babu wani waje da yake a rame ko ya nuna alamun qashi,saima kakkarfan siffarsa da cikakken zatinsa daya nuna kansa da kansa ta jikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na combat Reva net. Sai wani haɗaɗɗen luxury Rolex watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa. Lallausan sumar nan kuwa da tasha uban gyara daure a kasan ƙeyarsa ya kwanta yayi luf luf saboda wani irin gyara na musamman da akayi masa, Baqar sumar da baƙaƙen kayan dake jikinsa suka haɗu suka sake haskaka farar fatarsa tarrrr tamkar fitowar rana a farkon wuni. Shade ɗin daya toshe idansa dashi shine ya sake saka kyawawan qwayar idanunsa dake da wani irin shape mai matuqar fusgar hankali,idanun dake cike da wani irin kwarjini mai tarin yawa kwarjinin da a kullum yake lullube da fushi da kuma fusata. Sai nose mark daya sanya wanda kai baka isa gane waye shi ba. Wani irin daddaɗan ƙamshine ke tashi a jikinsa irin me ɗaukar hankalin nan. Ko yaya ka qara taqi kaɗan kusa dashi kana iya shaqar daddaɗan ƙamshin turarensa da ba lallai ka gane ainihin wanne irin turare bane,saidai yakan sanya nutsuwa ga duk wanda ya shaƙeshi ya kuma ƙara kwarjini ga ma'abocin ƙamshin. Kyawawan fararen hannuwansa zube cikin aljihun tsadaddun riga da wandon dake sanye a jikinsa,Sake gyara zaman bindugunsu security'n sa suka sake yi a tsare cikin shirin kota kwanar karbar umarni daga gareshi. Wata zazzafar Iska ya ɗan furzar kafin ya taka zuwa gaba. Arms tare da wasu mutum biyu daga ciki sukayi gaba kamar masu masa jagora,sauran kuma suna biye dashi. Cikin takun cikakken gwarzon namiji yake takunsa har zuwa cikin ƙayataccen Royal parloun da yake ƙawace da wasu irin Italian Wikipedia chair. Daga nan duka bodygourd nashi suka tsaya a parloun shida arms ne kaɗai suka nufi entrance door ɗin da sai sadasu da duka sassan gidan. A gaggauce suka wuce zuwa lipter da zai sadasu da dakin da zai sauka,cikin mintunan da ba zasu wuce 5 mint ba ya tsaya a parlou 3. Saida yayi scanning card a bakin qofar tayi qaramar qara alamun samun izinin shiga. Palace tenpor room ɗin suka nufa kai tsaye Wanda ko ina na gidan Gellary odyssey ke walainiya tako ta ina. Saida ya buɗe deep freeze ɗin dake makale da dab shiga asalin living room ɗin ya ɗauka kwallar wine ɗin sa. Nan ma Saida Gellary odyssey dpy ɗin yayi on locking up nashi kana ya suka shige Mahaukacin katon parloun da ma'adanar cctv footage ɗinsa yake. Wani irin matakan tsaron na'urori ne kawai ke magana a wurin. Tanbuwal da tun da aka jeho hi aka garkamesa jiya be kuma sake jin motsi ba sai yanzu. Da wani irin sauri ya sanya hannunsa yana kare Mahaukacin hasken daya kusan ɗauke ganinsa, jikinsa rawa ya fara na tsabar azabar yunwar dake kwakular cikin sa. Zaune yakai kan Chiar silinder caution ɗin dake facing da wannan mutumin. Ƙafarsa ya sanya tare da mirza ƙafar tanbuwal babu shiri ya saki wata ƙarar azaba cikin tsananin wahala ya furta. "Pls kuɗin su waye ku? Me kuke nema daga gareni?, Kuɗi!?, Suna?, Mulki?, Ko kuwa ƙarfin Iko kuke da buƙata?" Ya faɗa cikin muryan jigatuwa da wahala. Shiru babu alamun amsa hakan ya sanya shi sake faɗin "please let me know waye kai?" ”Makwamishin guba! Mashekin rayuka matunzirin ruhi. Sannan kuma mai kare mabuƙata! Ni dabaibaiyi ne me harɗe duk kan wani azzalumi na kaishi har kasa ÆK” Ya furta a fusace tare da kwance ɗaurin da akama tanbuwal ɗin. Wani irin mugun shock ne ya ziyarci ƙwaƙwalwar tanbuwal, AK AK AK haka sunan shi ya shiga masa amsa kuwa a tsakar kansa. Cikin Wata iriyar jarumtaka tanbuwal ya sheƙe da wata mahaukaciyar dariya kafin ya dakata. Cikin Wata irin dangerous voice ya furta. "Ai baka cika cikakken NAMIJI ba tunda Saida ka hada hannu da mace kafin kawoni i zuwa gare ka,karkaga ina karkashin ikon ka ka zata zaka iya min wani abu. duk da cewar zaki shine sarki a dokar daji amma karka manta damisa itace gwana wajen iya farauta" Wani irin lalataccen kallo Æk ya wurgama tanbuwal tare da Crossing ƙafafunsa yana kora kwalbar wine ɗinsa. Cikin wani irin hosky voice ya ce. "Ko wanne mafarauci garzone har sai sanda ya fuskanci ingarman zaki. Wannan haushin ƙaramin kuykuyon kare kake! Ka sani haushin ɗan ƙaramin kuykuyon kare kuwa ba gurnanin damisa bace! Ammah Ka jira hasalin yadda gurnanin ta yake. Ka sani ABDOUL-MALEEK ba kamar sauran sharar daka saba takewa bane, wannan Asalin Cikakken fusataccen damisar daya fito domin farauta ne a gabanka" Ya fadi tare da rotsa kwalbar wine ɗinsa kwalbar tai ratsatsa ta baje a wurin. Zuwa loƙacin babu komi a tare da Ak sai asalin fusatarsa kawai ake iya hangowa. Armstrong dake tsaye ne ya tunkari inda tanbuwar ɗin yake tare da soka masa allura a gefen yuwansa Yana bin bayan Ak ɗin shima. Bai tarar dashi a main sequence parloun gidan ba, wayarsa ya fidda tare da tambayar su Boss ya fito ne?, Tabbacin be fito ba suka bashi hakan ya sanya shi sauke wayar tare da bin ko wanne entrance door da kallo. Wani irin zafaffen numfashi ya fesar tare da tsananin tausayin uban gidan nasa. Kabar ƙasar ka kabar gidanku kabar danginka kazo ƙasar daba taka ba kana musu aiki da dukkanin zuciyarka da rai da ruhinka. Ko dan wannan abin ma bai ci ace gurɓatattun cikin ƙasar Nigeria'n sun sauya ba da kunya ma ace an rasa gwarzo zakwakurin da yake tsaye akan ƙasar sa. Kodan sun riga sun sanya tsoro ne a zukatan al'ummar OHO? Duk wani namijin da yake jin kansa da zafin kansa ta kawo akan ƙasar to kuwa Insha Allah sai an san yadda akayi aka kawar da wannan mutumin. Shin me masu kuɗin duniya da masu mulkarta suke son zama ne???. A kullum shine tambayar dake bisne cikin zuciyar Armstrong. Shi kikakken ɗan Nijeriya ne amma baya alfari da hakan saboda gurɓatattun cikin ta da ɓata garinta suka kewaye ko ina na cikin ta. Kasar data zamo koma baya ko lissafinta ba'ayi a cikin duniya. A cikin gidanku ma babu adalci bare akai ga wani wuri me nisa, a gaban idonsa dangin mahaifinsa da suke ƴan uba suka sanya wuƙa suka yanke makogwaron mahaifinsa sa!, Akan dukiyar da guminsa ne shima ya bashi ba sata yayba ba kuma haram yabi wajen tara taba. To taya muke tunanin duniyar mu zata gyaru a cikin gidajenmu babu adalci? Sai tsananin azaba yakai tsanani mu dinga ƙiran Allah gyara. Tofa baya gyara ba dole muma sai mun gyaro ɓarnar dake cikin gidajenmu. Bawai Ƙasarce a ɓace ba mu al'ummar cikin ta mune a ɓacen mune ɓatattun dole kuma dama gyara ta cikin gidajenmu yake farawa. Idan muka gyara halayenmu sai Allah ya gyaramu Amma muma muna da kaso mafi girma akan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54