Chapter 41
Chapter 41
tarin abubuwan dake faruwa da kasarmu uwarmu...... Wani irin zafaffen numfashi ya furzar tuno yadda ƙanwarsa ƴar shekaru uku a loƙacin take kuka tana dukan ƙirjinsa tana ƙiran mommy na daddy na. Gaba ɗaya jininsu ya ɓata jikinta. Wasu hawaye Masu zafin gaske ne suka zuba masa a lokacin daya tuna sadda mahaifinsa ke faɗin. "Ka gudu! Ka gudu kai da ƙanwarka ka tabbatar kun rayu ABDOUL-MAJEED, ka reni zuciyarta akan gaskiya da gaskiya ka tabbatar ka kulamin da RIYYERNERTOU, ka zama gatan ta,haskenta, ita kaɗai ce danginka ƴar uwa ɗan uwa ku tafi ka tafi wata duniyar kaje zaka rayu tare da tsarkakkiyar zuciyar da zata reni taku zuciyar da irin tashi zuciyar da ɗabi'arsa.kamin alƙawarin zaka zamo mutum na farko da ƙasar sa zatayi alfahari da shi... Wadannan sune kalaina na karshe da suka tsaya masa cakkkk acikin tsakiyar ƙirjinsa. Mahaifiyarsu kuwa ta mutu ne ba tare data iya furta masa komi ba sai idonta dake kan Riyya. "Ka gudu karsu dawo su sameku domin a zatonsu kuna makaranta ne, yanzu haka sun tafi ne da niyar su dauko ku kuma su kashe ku. Wannan kuma shine babban zunubi mafi girma da zasu aikata idan har suka taɓa lafiyar koda ɗaya daga cikin kun!........... Be ƙarasa maganar da yake shirin faɗar ma rai yayi halinsa haka ya ɗauki RIYYERNERTOU akan shoulder nashi ya gudu da ita. Sun sha matuƙar walahar gaske har tsawon shekaru uku a lokacin yana shekara na goma sha biyar ita kuma riyya tana da shekaru bakwai. A haka wani baƙin dare ya riski rayuwarsu shida ƙanwarsa. Daga nan babin sabuwar rayuwarsu ta fara shida ƙanwarsa ta hanyar keta mata mutuncinta ta hanyar mata fyaiɗe Anyi Raping ɗin. Masu iya magana sunce ko wacce ƙaddara tana da nara madubin,sudai nasu madubin Ak ne domin a lokacin da yake tsaka me wuya cikin mugun yanayin makauniyar ƙaddarar data riski ƙanwarsa. A daidai lokacin Allah ya kawo masa Ak shine ya shige masa gaba akan komi! Shine yake amsa sunan UWA UBA a gare su shida ƙanwarsa har kwanan gobe da safe. Ya basu tarbiyya ya inganta rayuwar da tarin ilimin addini da na boko. Ya shige musu gaba wajen ganin sun zama wani abu A koda yaushe Har abada abadan abada ABDOUL-MALEEK KUWAIT shine kashin bayansu. Hawayen tausayin gwagwarmayar rayuwarsu da suka fuskanta ya share ya nufi entrance door ɗin da yake da tabbacin anan Ak ɗin yake. Shima ɗaya daga cikin room din ya fada yana kokarin ganin ya kawar da tunanin dake kokarin zeroying maid nashi. Duk kokarinsa nason ganin ya kawar da tunanin dake neman addabarsa abin yaci tura, kansa ya jingina da jikin kofar tare da lumshe Idonsa. Numfashi yake fitarwa Ahankali yayinda yake furta kalmar. " Innalillahi wa'inna ilair raji'un,² Ya hayyu ya qayyum" daga cikin zuciyarsa domin kuwa tsabbb komai din da yake gudun ya faru ya rigada ya farun. A take kwakwalwar kansa ta nemi juyewa amma ambaton sunan Allah da yake hakan ya sanya. Ahankali nutsuwa ke saukar masa acikin zuciyarsa yayinda yaji tarin damuwarsa na gushewa.sosea yaji sanyi da cikakkiyar nutsuwa da salama acikin zuciyarsa. Gaban fridge bottle water ya nufa kai tsaye tare da ɗauko bottle water ya ɓalle murfin, ya kafa bakinsa Saida ya tabbatar ya shanye ruwan dake ciki tsabbb kana yayi wurgi da gorar. Wata iriyar ajiyar zuciya yake saukewa tare da sanya hannu ya ya dafe kansa. duk yanda zuciyarshi taso sanya shi dogon nazari yaki aminta da hakan haka kuma yaki bama brain nashi daman yin tunani kamar yanda ya saba a wasu lokutan. Ya jima a tsayen da yake kafin ya nufi bathroom, ya sakarma kansa ruwa Ya ɗebi mintoci kafin ya fito jikinsa na faman ɗigar da ruwa, mini towel ɗin dake rike a dayan hannunsa na aikin tsanewa. Wani farin trouser ya zira da t-shirt ita ma farar directly ƙroom din daya tabbatar da ak din na ciki ya nufa, tare da danna door belt din bedroom din yana jiran a bashi umarnin shiga. ★★ÆK★★ Yana shiga bedroom din kayan jikinsa kadai ya cire tare da daura fari tass din towel wanda ya ma wani irin lago lagon dauri kafun ya wuce bathroom. Kai tsaye cikin bathtube ya shige wanda ya hada ruwa me dumi da fresh out din wankan daya zuba. Aqalla sai da ya shafe mintuna masu dama kafin ya fito,tamkar wanda yake sauya fatar jikinsa. Fatar nan sai uban daukar ido da walainiya take ta kota Ina Ak namiji ne tsayayye da babu abinda yake masa shamaki da cikar zatinsa. Lafiyayyar fatarsa dake daukan idonsa ya kalla ganin wato shi Hutu da jika cikin arziki da nutsuwa Wani abu ne na daban da idan Allah yayika cikinsu basa taba boyuwa ko yayana. kauda idanunsa da suka dan canza launi sakamakon shigar ruwa cikinsu ya mayar ga madubi yana qoqarin tsane sumarsa data jiqe da ruwa,abu guda daya tak da zai fara gaya maka AK din ba asalin bahaushe bane, kodan yadda farar fatar jikinsa take da kuma tulin gashin kansa da yake amsar kudade masu gwabi wajen gyaranta. Tamkar babu wanda yake jiransa haka ya kammala shirinsa a nutse cikin wasu Ash din riga da wando Armless marasa kama jiki.wasu tausassan flip flops ya zura dogayen qafafunsa wadanda kamar basa taka qasa dan tsabar laushi da kuma taushinsu. kana ya kwashi wayoyinsa tare da daukar rimot ya danna kofar bedroom din ya bude. Waya ya fito yana yi cikin yanayin sakewa kadan. Gaidasa Arms yayi tare da fada masa an shirya dining. Bai ajiye wayar ba ya dan dago ya dan kalle shi kadan tare da amsa shi da kai, bai kuma janye wayan ba har zuwa lokacin. Cikin ishashshen takunsa ya nufi dining din har kuma lokacin yana manne da woyarsa, Ba wasu abinci masu nauyi bane junk food ne kasancewar babu restuarent a kusa ga kuma a wannan gidan babu kuku's. Idan ka dauke sikuriti babu kowa dake rayuwa a gidan. Wannan kamar gidan horo yake. A nutse ya jagali food din bame yawa ba yaci ya tashi har lokacin kuma woyarsa yake hankalinsa kwance. Kai tsaye coumpaund na gidan ya nufa da jikin railer ya jingina yayi crossing kafafunsa. Rigar nan da bata kama shima iska sai dade kwantar da ita a jikinsa take kan babu yar gadon fcarp. ★★★ ★★★ A dab plat din me napep ya sauke ta kamar kullum yauma sanye take cikin dogon shijjab har kasa, yau ba nikap ta sanya ba nose mark kadai ta sanya sai idonta data rufe da bakin glass. Rolex din skmee 2/1 din dake daure a hannunta ta sake dubawa da kyau don tabbar da nan din ne inda na'urar biyayar ta kawo ta. Tun daga kan uban tight security'n dake zagaye da get din ta tsorata. Amma kasancewarta mutum bame nuna sarewarta a fili bane ya sanya ta nufar katon get din. Cikin rashin tsoro ta tunkari get din baki daya kawunansu a sama yake hakan ya sanya ta yin sadab sadab taje a sukwane zata shige suka farga da ita. Ko kafin su dago kuwa wata farar kwalbar dake rike a hannunta ta musu fesar turare da ita ji kake "fessssss" yuf tayi ta fada gidan. Sadalaf, satalaf haka ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54