Chapter 44
Chapter 44
gaba, ki sani rayuwar ma da kikai dani costa risca ba ason raina bane. Don dai kawai muna gida daya ne kuma babu wata beb din a kusa shi yasa ma har na nemaki nayi maleg dake". Yana fadin hakan yay haurawansa upstsaid nashi.da wani mugun kallo umma mariya ta bishi kafin da dubi mam ta mike a fusace tace aidai kina jin abinda wannan watsatstsan yaron naki yake fadi a gabana, amma kikai shiru to wllh idan har ina numfashj a duniya babu wanj shegen daya isa daura wannan auren alkawarinane wannnan kuuma kinfi kowa sanin daukan alkawarina daidai yake da bi takan kowanne shege ne, koda kuwa za'a zan bada da kisa ne to kuwa saina cika wannan alkawarin..... Fuuuuuuhhh taja hannun yarta suna fucewa a gidan Zeey dake kitchen a lafe ta share wasu hawaye tana jizar labbanta. Tare da fadin "ai wallh inda numfashina na gangar jikina ahalin wannan gida kuda kwanciyar hankali kuma kunyi sallama". Tana fadan maganar tabar kitchen din tare da laluben wata number a wayar da kawai wata jar alama ta mata babu suna. Woyar na shiga ta zube akan gwawowinta tare dayin sujjada daga inda take.ta furta "Ran uwar gijiyata ya dade". Daga cikin woyar kuw wata kakkarfar tsohuwa ta wagaje wargajejen bakinta ta hakwaran sukayi tsatsa ta kwashe da wata dariya me kama da kukan jaki. Kafin ta shiga fadin "An gaida kura me dauke da fatar akuya Birinya baki jelen banza kedin kamar hadari kike malafar duniya ba shirgi maganin bari ta wajena, meke tafe da wushuwatu na?" "Alfarmar kamar ba alfarma bace a badini da za'a juwa gabansu zuwa bayansu bayansu ya koma gabansu nake ga hakan kawai zaifi, domin naga kamar ba masu ganewa da fahimtar bane" "Hhhhhhhhhhhhh Hhhhhhhhhhhhhhh Hhhhhhhhhhhhhhhhh Rainon shegu karki damu dumuwasi na tare dake yar shegiya uwar tsinannun, jaraba a cikin jarababbu makata a cikin makatattu annoba a cikin al'umma hinge kike babu me iyawa dake wushuwatu, dan daukar fansa aka yiki" Wata iriyar dariga zeey data koma wushuwatu ta barke dashi tana saisaita yanayinta ya koma normal daga na mummunar halittar data koma zuwa zeey din asalin da muka sani.. Shi kuwa salman saman lafiyayyan gadonsa ya fada tare da fiddo wayarsa kai tsaye data ya kunna tare da kiran dolly video call. Fitowarta daga wanka kenan tana daure da wani guntun towel ga wani bature kwance akan lafiyayyen gadon hotel din, ya tukun kune jikinsa da tattausan farin duvet daga shi sai wani transpared pyjamas. Woyanta da dama alread datanta yake a bude ta dauka, ganin me kiran saida ya sanya tadan bata fuska kana ta dauki woyar zama tayi akan stool na mirror'n. Kallonshi tayi yana kwance daga shi sai longsleev pant sleek wani irin numfashi ta sauke cikin muryan yar shogwaba ta furta. "Ohhhh my babyna I miss you somuch mua" ta bashi wani kyakykyawan kisses ta cikin woyar. "I miss you so much dee" ya fada yana gyara kwanciyarsa yana dan lumshe ido domin tunda ya baro poland bai sake mu'amulantar wata mace ba, domin shi ba da kowacce mace yaje iya mu'amularsa shi ne ma dalilin daya sanya ya ware dolly ita kadai dinta. A hankali ya shiga bude idonsa sai ya hango wani kakkarfan bature yana nufo dolly'nshi, Wani irin shafarta baturen yayi wanda hakan ya zoma dolly a bazata domin ita har tama manta cewar tare take da wani.da karfin masifa ya rumtse idonsa yana jin jijiyoyin jikinsa na tashi na tsantsan bacin rai. Me kenan?Amananshi dolly taci kenan kome? Meye wannan yake yi a tare da bai karasa maganar zucin saba wannan baturen ya finciki mitsil towel din dake jikin dollyn tare da wani irin hugging nata. Wata kara salman ya saki cikin tsawa ya mike tsaye a fusace tare da ambatar. "Dolly!!!" Wani irin mikewa tsaye dolly tayi babu wata² ta dauke fuskan baturen nan da mari cikin tsawa tace "I hate yhu Vham I hate that" Salman kuwa tuni ya datse kiransa wani irin dafe kansa da hannuwansa yayi kansa na wani irin sara masa lokaci guda, bathroom ya fada ya sakarma kansa ruwa kozaiji dan sausauci jin zuciyarsa yake tamkar yankar naman kirjinsa take tana zazzabowa kasa. Da bathrobe ya fito sanye a jikinsa sai kamshin shower gel yake da sauri sauri ya shirya ya fito da nufin xuwa club haka ko park,don ragema kansa takaicin dolly..... Mom nashi ce zaune a parlon har lokacin laptop ne a gabanta dana famar sarrata cikin kwarewa, sai zeey dake dan matsa mata kafafunta sama sama. Har yakai gab bakin kofa mom bashi ta tsayar dashi ta hanyar ambatar sunan shi. Cakk kuwa ya tsaya tare da juyowa yana kallonta "Dawo inason magana dakai ne" ta fada cikin rashin wargi. Dan yamutsa fuskarsa yayi yana fadin ta jira yanzu zai dawo cikin muryan no nonsense ta furta "Dawo nace" Dan dole ya dawo yana zama tare da tankwashe kafafunsa a gabanta yana fuskantar cikin yanayin jin haushi. Kallan shi mom nashi tayi tana ajje laptop din dake kan cinyart zuciyarta na quna tace. "Se yaushe ne zaka daina kuntamin da rashin daukan maganar mahaifinka fiye da nawa, sai yaushe zaka me amfanin dazanyi alfahari dakai amatsayin dana Salman? Kullum mahaifinka shine a samana akan dukkan wasu lamuranka!. Menene yake faruwa acikin kanka ne da kwata kwata babu ranan da zakasa nayi alfari dakai a matsayin dana? Ban isa dakai ba ban isa sakaka abu ka yimin shi ba cikin dadin rai.... Hannuwanta ya kama yana hadewa cikin nasa tafin sai kuma yadan rausayar da kansa yana sakar mata murmushi. " Mommah me yasa kullum kike ganin tamkar baki isa sani abu nayi ba? Kullum maganar kenan sabanin ra'ayine kawai muke samu dake. Shi kuma daddy so tari ra'ayinmu kanzo daidai dashi so shiyasa zakina ganin kamar bana bin umarnin, pls my mommanah kimin afwa Ina matukar son Meerah ne har zuciyata wllh" Wani irin rumtse idonta tayi tare da zare hannunta dake cikin nashi zuciyarta na mata daci kalamansa na kona zuciyarta. Ya zama dole tayi wani abu akan wannan auren da har cikin zuciyarta taji bata kaunarsa kwata². Tashi tayi tana barin parlon da kallo ya bita domin tsaff ya gama sanin so take taga ta dakatar da auren nan kota halin kaka, ficewarsa shima yayi a parking space ya dauke daya daga cikin manyan motocin dake shake da wurin ya cilla saman kwalta tare da daukar hanyar hotel din Asas rayallerh. ★★KUWAIT★★ Duk inda ka wulga bayine da kuyangi bila adadin akowace kusurwa ta cikin babbar masarautar. kowanne da aikin daya duqufa yanayi wasunsu kuma a kakkame suna gadin hanyoyin wucewa da kowace qofa ta cikin masarautar. Musamman entrance din da sashin me martaba sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR KUWAIT yake, Wasu mahaukatan Samudawane kewaye da sashen baki daya. Kallo daya zakama dukkaninsu ka gane ko wannensu yana cikin yanayi na tashin hankali ne. Wani irin shiru ne ya ziyarci wurin tamkar wanda mutuwa ta gimla ta wajen.Kowa a take ya shiga nutsuwarsa Wanda suke a daidai hanyarta suna rabewa gefe tareda sunkuyarda kai kasa don bata hanya saboda takun tahowar gimbiya ADEENERH. Wanda sautin anklets din zinarin dake kafarta shine yake ankarar ma duk wani hadimi isowarta ko tahowartar tundaga nesa. Wannan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54