Skip to content

Chapter 6

Chapter 6

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

anan cikin garin Lagos, ta fara aiki da gidan jaridar zamani tv watanni shida da suka wuce, tana da tsayayyen saurayin ta wanda za'a yi bikin su nan ba da jimawa, tun ranar da rahotannin ya fita na bibiyi ita kanta yarinyar, don nasan dole zaka buƙaci sanin wacece ita, yanxu haka md ɗin yana ƙoƙarin buga jaridu akan hakan, umarnin ka kaɗai muke jira wajen daƙile faruwar hakan, A yadda nayi kyakkyawarn bincike game da Md ɗin yana da masifar son kuɗin masifa, shi ba ruwansa da inganci abu burinsa kawai kuɗi ɗaukaka sune kaɗai yaren daya fi fashimta" Axton ne duka me wannan maganar kuma tun a ranar da rahotannin suka fita yabibiyeta, harya samu cikakken tarihin ta. Saida ya kuma zuƙar cigarettes ɗin dake hannunsa, kafin ya ɗago rikitattun idonsa ya zuba su akan axton, shi yasa ahar kullum yake kuma alfahari dashi acikin yaran nasa, duk abinda ya kamata kafin yace shi kuma ya aikata. Miles ne ya kuma daidai ta nutsuwar sa cikin gurɓatacciyar hausar sa da baya fita ya furta. "Boss ni kuma bayan na bibiyi rahotannin ta na shiga duka kafofin sadarwarta, kamar yadda ta umarta tabbas tauraronta na haskawa a wannan tashar dama duniya baki ɗaya, duba da yadda take da tarin masoya tako ta ina hakan yasa cikin ƙanƙanin loƙaci wannan ruhotannin ya baza garin Lagos harma da ƙetare, a yadda ma na samu cikakken bayani daga cikin headquarters na A F S, aka bama shi MD ɗin bayanin dukkan abinda ya faru a safiyar juma'ar, kana Saida suka yi duba da yanda tauraron yarinyar yake haskawa kana sukayi amfani da hakan don son cika burinsu, zasuna amfani da ita ne kawai don..... Ɗaga masa hannun da Boss In nasu yayi ne ya sanya shi dakatawa, wani irin killet murmushin gefen baki ya saki tare da faɗin. "A barta taci gaba da buga wasan da dukkan alama zai yi armashi, zai kuma kawo nishaɗi, Nazari muke da ƙwaƙwalwa karku manta!, Sadaukai ne mu tamkar mafarauta!, ba'a taɓa nasarar yaƙi sai in da mayaƙa, don haka ina son a buga wannan game ɗin tare dani" Wani mugun waro idanu sukayi suna bin boss in nasu da kallo Lallai Boss rigimarka yawa gare ta da ɗaukar abu me muhimmanci da rashin muhimmanci. Kai komai da zuciyarka ta raya maka sai kace ayi baka tuna abinda zai iya zuwa ya dawo,in banda taryan Aradu da ka taya ma zakace a bari a buga jaridu akan ka, kana kace a barsu kana son buga wasa akan mutanen dake farautar rayuwarka. Sune kalaman da da axton ya shiga nanatasu cikin zuciyar. Tsammm ya miƙe cikin tafiyar nan na ƙasaita da kuma izzar da yake da yabar main Parlourn tare da nufar upstairs nashi, yana barin su da wasuwasai falll zuciyarsu. Shi kuma Boss In saman sa ya nufa zaune yakai gefen bed nashi tare, da janyo system nashi me ƙirar campanyn apple, engine machine ɗin sa ya jona tare da jan glass cup yana siyanyar coffee tare da fara dan sipping nashi a Ahankali, kana ya shiga wasu ƴan sarrafe sarrafe kafin ya janye ta tare da ɗaukar wani ɗan kit box,, buɗeta yayi a take wata ƙaramar waya ta bayyana irin nokia ɗin nan ta da. A take ya shiga loda Numbern daya gama haddace abarsa ya lodata tare da shiga ɓangaren messages, ya koma yana ajje wasu short mess tare da switch na wayar yana jefata cikin wannan kid box ɗin. *Zamani tv* Jikin MD har mazari yake wajen amsa saƙonnin dake ta famar shigo musu, tun a daren shekaranjiya da da suka bayyana rahotannin babban criminal ɗin, kamar daga sama kuma yaga wani ɗan short mess ya faɗa masa, cikin rawar takashi ya shiga cikin message ɗin, _ Amatsayina na babban masoyin wannan tasha ina so ayi fira dani da misalin 11:15Am na safiyar gobe tare da MEERAH ABDULLAHI GWANI🫨_ "Yesss!" MD ya faɗa da masifar ƙarfin daya sanya sauran ma'aikatan dake dab da Ofishin sa fitowa, dama abinda yake fata da kuma buri kenan ayi ta jan maganar wannan AK ɗin, gashi Alkhairuka suna ta samunsa a sanadiyar iyaka yaɗa labaran sa kawai. Loƙaci ɗaya tashar sa ta kara zama shahararriya kuma yasan duk ata sanadiyyar MEERAH ne. "Kai wannan ƴa kin zama Alkhairi na iyayenki sun iya farar haihuwar ƴar baiwa!" Haka dai Md yaci gaba da zabga surutunsa kafin yasa a ƙira masa mera ɗin. Zaune take gaban me girma Md wanda ya shiga koɗa ta da mata kirari kala daban daban, kafin ya shiga sanar mata da buƙatarsa na wannan bawan Allahn da yake son yin fira da ita. nooding kanta kawai ta yi tare da zuba masa ido tana binshi da wani irin kallo wanda kai tsaye zamu iya ƙiransa da najin haushi. Ganin ba haƙura zai yi bane ya sanya ta miƙewa dare da barin office ɗin, kai tsaye coumpaund na gidan jaridar ta nufa tare da barin gidan baki ɗaya. tana fita kuwa taci Sa'a ta haɗu da me napen, shigewa kawai tayi shi kuma yaja kanta ta kife saman cinyarta, tsananin ciwon kan da take ji na ƙara tsananta, "Hajiya ina muka nufa?" Ɗan adedeta sahun ya tambaye ta. "Daɗin kowa" ta bashi amsa ba tare da ta ɗago kanta ba, babu wata tafiya me zurfi sai gasu har sun ƙaraso, handbag ɗinta ta buɗe bayan ta fita tare da zaro dari biyar ta bashi, canjin ɗari da hamsin ya bata tace ya barshi tana faɗawa cikin gidan nasu. ________★★★________ Cikin wasu haɗaɗɗun riga da wando na campanyn Dior saddle Brook yafito brown se ɗaukar ido yake baƙaramun amsar jikinsa kayan suka yi ba, abinka da cikakken namiji me jini a jika da ɗan sassarfa yake saƙƙowa daga stair ɗin, Zazzaune ya samu su axton suna ƴar firan su , ganin sakkowa Boss In nasu ne ya sanya suka miƙe zumbur tare da rusunar da kansu. Kai tsaye motocinsu suka nufa suna mata key dake dama already sun riga da sun san da fitar. katafaren unguwar Banana Island suka nufa wadda take nan da manya manyan ƙerarrun gine gine na zamani duk inda ka kalla zaka so kara kallar wurin, tamkar ba'a nigeriyarmu ba, ko ina ka ɗaga idanu ka kallah sai ka ji baka son kawar da kanka daga wannan wajen, tsaruwa iya tsurwa, haɗuwa iya haɗuwa kammm anguwar ta gama haɗuwa. Tun da motocin suka hau saman titin babu abinda kakeji sai suuuuuu suuuuuu suuuuuu shine kaɗai sautin dake tashi, har suka nufi wani ƙayatacce fitaccen gini na alfarma, da remote suka yi amfani wurin buɗe ƙaton jibgegen get ɗin. Kai tsaye suka danna hancin motocin nasu zuwa cikin gidan a jere, nan suka ci gaba da tafiya a jere a saman kwaltar, a ƙalla dai Saida suka wuce wajen get huɗu kamin su isa gaban wani ƙaton parking space ɗin da ya gaji da haɗuwa, wasu shegun tsadaddun motoci ne maƙare a parking space ɗin, tamkar companyn kera motoci , kowani mota ka ɗaga idanu ka kallah sai ka sake kallah saboda tsabar tsananin kyau da tsadar motar, kallo ɗaya zaka ma dogon ginin da yafi kama da masarrafin kera motoci. A jere waje guda motocin nasu suka yi parking, ɗaya daga

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54