Chapter 45
Chapter 45
sautin sarkar shine ke sanarda tahowartatahowarta tun daga yarinta harzuwa yanxu data manyanta saboda mulki a jinin jikinta yake. Macece me takukar izza dajin kai kagata yar zafin kaice ba komi ake mata ya burgeta. Tana da wani irin boyayyen hali na tsananin jin dausayi, idan akace kowa ya tsani abu to ita kuma zai kasance tana yi ma wannan abun ko maye wala mutum wala sabanin hakan. Idan kuma aka daukaki abu to kuwa zaka tarar ne sammm wannan abun beyi mata ba koda kuwa kyansa ace yakai zinare kyaune. Tana karasowa hanyar dazata shigarda ita bangaren mai martaba sarki ta tsaya cak batare da tace kala ba saima juyowa da tayi ahankali tadan kalli gefenta. jakadiyar dake gefen tace tayi saurin matsowa tareda juyawa takalli kuyangin dake take musu baya kusan su shida, kallo daya tayi musu suka ja baya ahankali suna tsaya tareda sunkuyarda kai domin sun san ma'anar hakan... *BY AMMEY LAYLERH* *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page 43&44 # ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # Hope # courage # Survival # Humanity # Inspiration 🤍🔥✅✅✔✴✳❇ Boyayyar ijiyar zuciya tasauke ahankali saida nu'ura ta tantanceta kana ta sanya kanta zuwa kayataccen parlon. jakadiyart na mara mata baya Parlour ne mai wani irin girma da tsari dayaji adon royal chairs gold and golden kamar zinari sai kyalli da daukar ido suke. sai komai daya kawata parlourn yazamto shima gold and golden colour dinne splits aircon kusan guda biyar sai aiki suke sanyi yakama parlourn tako ina sabida wata irin dukiyace ta musamman aka narkar a parlourn. Wanda tsabar haduwa da girman parlourn yasan ya sammm alkalamina yayi kankanta daya rubuta muku irin kayatuwar parlour kuyi emaging kawai aranku yadda parlourn zai kasance. Babu kowa parlourn kasancewarsa parlourn farkone dazai sadaka da palon sarauta harzuwa turakar sarki. Saima wani irin shiru da parlourn ya dauke. Sake tsayawa cak tayi tareda sake sakin wata nannauyar ijiyar zuciya akaro na uku zuciyarta na harbawa batareda tajuyo bangaren da jakadiyar ke binta ta mata alama data dakata. Ajiyar zuciya ta sauke a karo na ba adadi kwawan idonta sun rikide sun koma jajaye. Hakan na sake bata tabbacin jikin Mahaifin nata ya matsa kenan da gasken?. Adeenerh ta fada acen kasan makoshinta kafin ta tattaro duka jarumta da karfin gwiwanta. Ratsa dogon palon tayi kai tsaye kofar da zata kaita ainihin parlourn mahaifin nata ta tunkara zuciyarta na neman karyewa. Saida ta runtse jajayen idonta kana tayi kundunbalar tura kofar bedroom din. Wani bedroom ne na alfarma babu kowa sai qarar ac dake tashi ahankali. Zaune yake cikin shiga ta alfarma saidai Kallo daya zaka masa kasan bama ya a hayyacin sane, jin motsin shigowane ya sanya Zaid dago da kansa kallo daya yayi mata da idanuwansa masu tsananin kwarjini da firgitarwa ya dauke kansa. Duk da taso rudewa tayi saurin daidaita kanta ta tattaro nutsuwa da karfin halinta baki daya. Duk da kasancewar Zaid kani yake gareta amma ba karamin kwarjini yake mata, kasancewar kwarjin mahaifinsa ne ya dauka reality shida Biyuninsa Maleek. Karasowa tayi cikin sanyin jiki da fargaba ta kallesa ta rufe idanuwanta dasuka fara canxawa tana durkushewa gaban zaid din. murya na rawa tace "Me martaba! Paapana zaid Ya abana" Idanuwan daya sake watso matane yasan ya jikinta sake daukan mazari ga shirun daya mata shi kansa babban tashin hankali da azabtarwane wa zuciyarta. Sake dukar da kanta tayi saboda gudun ganin yanayinsa. ko dagajin yanda ya dauke wuta yaki ya magantu ya sanyata rushewa da kuka wai ko zai magantun, domin ita wllh tsoro take! Tsoron dunkarar dakin sirrin me martaba take gudun abinda ka iya zuwa yaje. Gudun kar tayi gamo da abinda zai sanya zuciyarta bugawar lokaci guda. A kalla sai da dauki tsawan wani lokaci tana rairai kukanta nan ma shiru yaki kulata. Kamar daga sama taji dakakkiyar muryarsa cikin ikon mulki yace. "Me martaba me mutuwa paah yana nan da ransa, domin mikiyansa ba zasu taba iya kaishi kasa ba. Kimin shiru anan domin wannan kukan naki sake fusata zuciyana yake, ki sani Sarki HASSAN AL-HASSAN EMAAR dashen Allah ne hadari ne shi malafar duniya duk wanda yace zaiyi dashi yaja da ikon Allah ki shiga idonki ya kalla miki shi. Dole wannan karon dan zaki ya bayyana akan mikiyansa. Lokacin dawowarsa yayi Masu gudu su gudu domin kowa yasan karon ba dadi!!!" Ya karasa fadar maganan nashi a fusace. Dagowa tayi takallesa idanuwanta na canxawa zuwa kalar tausayin dan uwan nata. Tare da zubo da wasu kwallar zafin da zuciyarta ke mata, tana jin tsananin kaunar yan uwanta a ranta duk da kasancewar ba uwa dayace ta haifesu ba. Adeenerh itace babbar yar me martaba mahaifiyarta ta rasune a lokacin tana yar shekaru shida xuwa bakwai. Ba tare data sake kallon inda zaid din yake ba ta mike tana nufar daking room din data tabbar anan me martaba yake. Tamkar yadda ya bata umarni haka ta ratsa ta shige cikin parlourn. Duka wadanda suka dace ne a cike tare da dakin kowa rannan bace babu me alamar sassauci. Kowa ta shiha bi da ido anan ta itama nata idon suka kallar mata Mutanen dake ma paah dinta kallon ka mutu kawai muhuta din nan. Zaune takai ta bangaren da Oummey ke zaune, shiru ne yaci gaba da wakana a dakin zamanta da kamar mintuna biyar MOH JIDDOH ta dubi Oummey tare da furta. "Wannan karon saiki kira lalataccen dayan dan naki, dan wannnan jinyar tasha banban da sauran, mebi ta ajalinsa ne tazo kuma ta gaskiya da gaskiyar kenan. Wani irin mikewa tsaye Adeenerh tayi cikin furyar fusatar zuciya da dacin murya ta furta. "Wannan kalmar marar kan gado fa JIDDOH! Ki sani gudun hatsaniya ne ya sanya mutanen da suka kasance mugwaye a cikin zuriyarki ya sanya mutumin daya kasance shiru shiru ya fusata!. Inason ki sanarma azzaluman cikinku cewar idan har akaci gaba da fusata shi to ki sani tarwatsa masarautar zaiyi kinsan da hakan?. Uwa uba kuma Zakin da kika dade kina ikirarin ya dawo to ki sani yau sai adda'arki ta karbu dole ya dawoooo........ Kowa da yake daking room din babu wanda jinsa da ganinsa basu tafi hutun wucin gadi ba. Kai tsaye Adeenarh ta zari wayar Oummey directly numbern da tayi lakabi da *Willion gargalion* ta dokama kira tare da manna woyar da kunnen oummeyn "kima danki magana a gaban kowa ki sanar dashi ya isa haka paah dinsa da kasar shi na bukatarsa suma, har wadan da ba'a gayyata bama na muradi da dawowarsa mahaifarsa EMAAR's kai tsaye ABDOUL-MALEEK HASSAN AL-HASSAN EMAAR's take da bukata!” Tana fadar hakan ta juya a fusace tabar dakin. ★★NIGERIAN/ LAGOS★★ Fitowarsa kenan wayarsa ta fara ringing ransa adagule yacirota da nufin kashewa gaba daya. Domin tunda yayi waya da zaid komai ya gama kwance masa. Saiya sami kansa da tsurama woyan nashi ido ganin sunan dake yawo akan screen na woyan *_Sweet Oummey_* wani iri rintse idanunsa yayi ransa nakuma dakulewa. Saida woyar ya katse kana ya sake calling nata againt. "*GARGALION*" Kai tsaye sunan ya tafi ya ratsa har cikin tsakiyar zuciyarsa. "Paah! Dinka EMAAR's na bukatar Tsayayyen matashin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54