Skip to content

Chapter 12

Chapter 12

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
Download Book

ɗin da kuma pen tsaye tayi akanta, ba tare data damu da tsaiwar data mata a kai ba ya ta fara aiwatar da abin da zuciyarta ta gama tsara mata, kyawawan idaniyarsa masu kama dana mage ta shiga zanawa a pepper ɗin, exactly tayi zanen full face nashi sai dai iyaka eye nashi ne a bayyana ne. Ita kuwa wannan police ɗin har wani sake karkatar da kai take wajen hango zanen. Tana kammala zanen ta miƙa ma police ɗin text book in, jiki na mazara ta fice ta text book in a hannun ta kai tsaye babban office ɗin d.p.o RT Atya ta nufa. A lokacin d.p.o na tare da Isa Manu Atya ta ajje text book in gabansa. ”What are you doing to say?" "Sir. Meryam yebdullahi goni meerah!" "What?" D.p.o ya faɗa a zabure tare da miƙewa yana nufar hanyar woje, har da ƴar sassarfa yake haɗawa ganin ya cimma ɗakin da take. Hasken daya sake haske idonta a karo na biyu ne ya sanya ta sakin wani lalataccen kill smile dama tasan za'a rina, samm ta rasa mine ma ya hanata aiwatar da hakan tun a juya. Zanen fuskar da tayi aka d.p.o ya tura gabanta, "muna buƙatar ƙarin haske akan zanen da kika bamu!" (Anzo wajen) ta faɗa a cennn ƙasar zuciyarta. A zahiri kam ɗan duban wanda ake da d.p.o tayi a kai kaice ba tare da shakkar komi ba ta furta. "AK kenan! Inda har da gaske kuna kan aikin ku, ga Ak nan ku baza yaranku su fara farauta iyaka idonsa ne kawai nima na sama gani" jikin d.p.o har tsuma yake ya furta "da gaske kina da tabbacin wannan face ɗin na Ak ne?" Noding kanta tayi alamar tabbatar wa. A 380 suka bar ɗakin tsabar sauri hular d.p.o har faduwa take. Cikin ƙanƙanin loƙaci aka baza fuskar Ak da ake nema ruwa a jallo. Kanka ce me matasa sunyi caaaa a media game da fuskar Ak da aka ɗora. ★★★ Wani irin kafirin murmushi Ajmaal ya saki a lokacin daya kalla zanen fuskar Ak ɗin shishar daya ke zuka ya feso da hayaƙin matashiyar budurwr ko nace ƙaruwar da yake tare da ita ya sake mannata da jikinsa, a bayyane ya furta. "AK muje zuwa da dukkan alamu wannan wasan me zafi ne!, Lallai na yarda da tauraron ki yana haske ƴar jarida meerah, kece tsanin Ni! Kuma nine mahayin" sai kuma ya sheƙe da wata iriyar dariya ta marasa hankali. Tare da hade bakinsa dana wannan budurwar, ita kuma cikin kwarewa a fannin ta wani shiga sarrafa gangar jikinsa tana karasa fitar dashi daga ɗan hankalin daya saura a gareshi. ★★★ Safa da marwa kawai yake famanyi a karo na ba adadi ke nan sai yana dab da cimma burin sa. Sai wannan ɗan gaba da fatihar yazo ya rugaza masa aiki. Baki ɗaya ya gama jigata kansa gumi sai kwaranye masa jiki yake. Idan bai manta ba governor da kuma minister suna hannunsa,kenan target ɗin Ak na gama dole shine. "Inaaaaaaa hakan ma bazai taba yiyuwa sammmm" ya faɗa da ƙarfin masifa haɗi da kaima bango iska nashi, sai huci yake saukewa. (Kai wannan yaro uwarka ta haifo mana masifa da bala'i wllh) ya faɗa a cikin zuciyarsa. "Dole na dakile duk wata hanyar da nasan wannan ɗan shegiyar yaron da nasan zai ganni, kafin na gama samun mafita" ★★★ A bazata murmushin ya subce daga fuskar Ajmaal (dole na fara nuna maka ba kai kaɗai ne teterors ba Ak) ya ayyana hakan a cikin zuciyarsa tare da ciro wayar sa yana dialing wata number. "AK! AK!! AK!!!, Da kyau tsohon abokina sheɗanin sheɗanu, kuma tsuntsu me wayo" "Kwarai kuwa haka ne sabo da mun saba sheƙe sheɗanu tare da kai ba Ajmaal" "Uyummmm naji daɗi dake fashimce haka Ak baban shadanu a yanzu haka dai nasan ka girgiza ba?" Jin Sautin lalataccen murmushin Ak ɗin da yafi natsa a kaff cikin duniyar ne ak ya sakar masa. Ɗan zame wayar yayi tare da kallon screen ɗin sai kuma ya sake manna wayar da kunnunsa, still Sautin fitar murmushin ya kuma ji daga Ak ɗin. dip dip dip yaji sautin katse ƙiran da akayi ba tare da an sake furta masa komi ba. Shima murmushin ya saki domin wannan loƙacin yaci alwashi akan Ak ɗin sosai, shi kaɗai yasan shirin daya danajama hakan ciki kuwa harda ziro meerah acikin tafiyar. To ai shikenan kooooo saimu gimtse🫰 *By AMMEY LAYLERH ✍️* *🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀} *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 11&12 #KIDNAPPING *DRUG TRAFFICKING #AGGRAVATED ROBBERY 🤍🔥✅ __________________ ★★★ *Police station* Zaune farin dattijon yake gaban d.c.o bayan gama koro masa jawaban sa akan meerah ɗin,duba da uban kuɗaɗen daya zube masa wanda dama already yau za'a sallames, ganin tsuntsu daga sama gashashshe ne yasa jikin d.p.o har mazari yake wajen bada umarnin a kawo meerah ɗin. Cikin ƙankanin loƙaci sai gasu da meerah ɗin, shi kuma ya miƙata ga wannan dattijon. A kamilance ya musu sallama yana ma Meerah nuni da suke, saida ta ɗan yi dammm na alamar mi hakan ke nufi.kana dai tayi gaban, bata sani ba ko duk cikin aikin ne hakan. Gaban wata arniyar bakar mota suka tsaya shi da kansa ya buɗema meerah ɗin ta shiga domin kuma zuwa yanzu ta fuskanci kamar gida ne za'a maida ta. Uban gudu yake tsalawa a cikin motar wanda gudun har ma ya kusa tsorata meerah amma dake zuciyarta a dake dake sai taƙi barin tsoron nata baiyanuwa. Sunzo daidai round about wata kafurar Mota ƙirar Mercedez Benz tazo tasha gabansa, sai kuma yaji tsaiwar wata ma da bayansa hakan ya sanya zuciyarsa tsinkewa, amma sauya dake yana kawar da hasashen da zuciyarsa keson bijiro masa. be gama tunanin me ke faruwa ba ya ji ana ƙwankwasa window'n Motarshi da Bindiga daidai saitin kanshi kululu cikinsa ya kaɗa hanjinsa ya ɗuri ruwa nuni suka mishi da ya fito. hannu na rawa ya fito ganin wasu uban samudawan da yasan kuskure kaɗan zai musu su aika shi inda in aka tafi ba'a dawowa, yayi ɓeshi dukkaninsu suka yi suna sanye da facial Mask. Umurnin da suka sake bashi ne a karo na biyu ne ya sa shi tunanin wannan wasu irin ƴan fashi ne? Inda ɗaya daga cikin wannan samudawan ke ce mai "Take off your clothes" da sauri yace "What?" sauƙar wani abu me ƙarfi yaji a gefen fuskarshi, da sauri yayi ƙara tare da dafe gefen kanshi yaji danshi danshi Alamun jini, cikin ɗaga murya yace "take off your clothes,i wont ask again" da sauri dan farin dattijon yayi yanda sukace, ya rage daga shi sai gajeren wando da guntun singileti, hatta takalmanshi zobe da Agogo, sai da ya cire, bai dawo daga duniyar daya tafi ba na wuccin gadi yaji sauƙar Bindiga a kanshi. Ɗaya daga cikin samudawan ne yama na kusa dashi alamu da ido. Gaban motar ya nufa kai tsaye Sleeping powder'n dake hannun sa ya shaƙama Meerah, Kafin ta samu damar cewa komai ne taji abu a fuskanta. Yuuuu taji kanta ya fara mata, Cikin zabura tai yunƙurin dira daga cikin motar ɗin, sai

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54