Chapter 31
Chapter 31
din ta kudin ta bashi yaja suka tafi. So kawai take taga sunkai gida don Anne'nta tace mata zata aiketa gidan hajiya umma,amma intai dare ba zata aike tan ba ko kafin ma ta dawo ta aika Raiha. Wani irin kyakykyawan murmushin daya sanya me napep din kallonta ta tayi.Tuno da Anne da tayi Ita kanta batasan iyaka adadin son da takema Annenta ba, Kawai dai tasan Wani irin so takeyi mata na musamman, son da yake tafiya da tausayi mai tsanani bata da kowa aduniyar nan daya wuce mata Anne'nta itane komai nata Garkuwanta haka kuma farinciki agareta ita da Raiha dinta. Hannuwanta da suke hade wuri guda ta sake dunkulewa, tana matukar tausayin Anne'nta sabo da ta tashi ne ba uwa uba Yar uwa Dan uwa wani nata a tare da ita.. Ahankali kuma ta jingina bayanta da jikin kujeran motar. *{INASONKI ANNE NA}* Ta fadi hakan acikin zuciyarta tana mejin tsananin shaukin son mahaifiyar nata na ratsata. Uwar da takejin babu irinta a fadin duk duniya, Uwar da take fatan faranta mata akoda yaushe, Uwar da take matukar son farincikinta fiye da kowa da komi na cikin duniyar. Aikuwa basu wani debi lokaci ba suka iso gidan kuma babbar sa'arta data ko shirin tada sallah ba'aiba. Da sallamarta ta shiga kota kan mutanen da suke zazzaune bata biba, Da Anne'nta ta fara cin karo a palo tana duddura humrarta me azabar kamshin gaske. Gaida ta tayi dama kuma al'adar tace hakan, duk idan ta dawo a wurin aiki takan gaida Anne'nta. Amsata annen tayi da Yar fara'arta tana fadin. ”Ai kuwa da baki zo ba saidai ki tarar Raiha ta tafi!” Anne ta fadi da dariya a saman kyakykyawar fuskarta me kama da bata yan Nigeria ba. ”Ai kuwa da kuka zanta miki Allah Anne!, kinsan na dan kwana biyu rabo na da gidan hajiya umma ” Ta fadi cikin muryan shigoba tamkar wota baby. ”Crying Mumu gurl ey kuwa da har videoing dinki zanyi na dora a media with caption ” Dan micilon bakinta ta turo gaba tare da fara Mirza kafa a palon. ”Yowwa Anne dakko min eyken kinga gudu na tayi, daga gidan su maman Mujaheed din. Aysha CE ma ta tsayar dani na mata wasa, badon haka ba Ina ba mummy Hafsah aikar zan dawo!” Duk Raiha CE me Wannan maganar ba tare data bari ko numfashi tashaka ba. Da sauri Meerah ta mike tana ma Raihan hararan wasa. ”Anne dakko saimu tafi tare kafin a shiga sallah” Da to Anne ta amsa tana shigewa uwar dakan ta babu jimawa ta fito hannunta rike da laida. Harta mikama meerah ta tuna ko abinci bata Ciba. Dauke wani wargi a idon ta tayi cikin kamewa ta furta. ”Zauna sai kinyi dinner tukunna” Fada fuska tayi kadan sai kuma ta furta. ”Ayya Anne kinga fa naci tare da disha” Gyara zaman ta Anne tayi cikin no nonsense ta furta ”Ashe baki shirya fita ba kenan okay?” Tana gama fadar ta mike tayi tayo tsakar gidansu. Haka ba don taso ta janwo plask din abincin gabanta, washe baki tayi ganin dan waken fulawa ne. Ai a tamanin ta janyo gabanta Raiha tace suci tace mata ta koshi. Sai kuma ta dan matso kusa da meerah din tana fadin. ”Kwai da Kwai Maman Mujaheed ta bani, Ashshalle kuma ta bani rufaida yoguht” Ta fada tana kyafkyafta ido kamar wata mara gaskiya,domin tasan idan Anne taji kashinta ya bushe. Dan dole suka tsaya sukayi sallar magriba kana suka amshi sakon suka tafi.... Tana fitowa tafiya kadan sukayi ta hadu da Fatima kawarta da suke layi daya, A cikin wata hadaddiyar motar ta prado. rashin kyawawan halin da fatiman bata da shine ya sanyata meerah din yakice ta a jikinta, Amma ita fatiman sosae take kaunar kwayancensu da meerah din, rashin fuska ya sanya itama janye mata amma duk inda suka hadu tamkar tasa zani ta goye meerah din haka takeji. Tun kamin su karaso tayi parking motar ta. Fitowa tayi cikin fara'arta ta fito tana ma meerah din magana. ”A ahhh kawata wannan fa ba girmanki bane kina tafiya da qafa zuwa wani wuri, gaskia bakyama kanki daidai ace kina mace cikakkiya da acikin matan make Ishasshiya ce meji da tashen kyau da cikar zatin halitta da haiba fara kyakyawa ga diri son kowa qin maqiyin Allah zaki zauna kina yawo a kafa,Dubeni koni da banbkaiki kyauba dubi irin motar da nake hawa bare ace 500 hundred ta gagareni na hawa napep. bareke kyakykya son kowa kin wanda ya rasa kullum ke fuska kwakume da niqab kina cutar kanki, wllh meerah kullum bazan gaji da gaya miki gaskiya ba akan kiyiwa kanki fada, yanxu dai shigo na rage miki hanya” Ta fada tana wani iyayi ita nan ga me mota. Wani dan iskan kallo meerah ta watsa mata kafin kuma ta saki murmushin takaici ta furta. ”Ai dana shigar da aka sameta ta haram kwara na shekara ban kai inda nake son kaiwar ba, dadai na shiga motar da ake sameta ta kyazamtacciyar hanya maras kyau!” ”Nifa abu mafi bani takaici dake befi yanda kike cewa wai bazaki shiga motana ba abu kadan kice haram, ina zinar bajikinki nake kaiwa ba nawa ne kuma bake kikai ba, amma ace kina kawata kina tafiya da kafa gaskia Impossible shigo mu tafi” ”Fatima kenan koke fatana Allah ya shiryar dake babu wani kalar kaddarar da zai Sa Insha Allahu na aikata zina. musamman irin wacce kukeyi fatima karuwa tsirara babu ko sakayawa shine sunan da kike amsawa. Kina wofintar da darajarki ta ya mace kina wulakanta suturar da Allah yai miki kina kaiwa mazajen bariki jikinki,suna amfana da ni'imomin jikinki suna halllakar dake! suna amfani da dan abinda Allah ya basu na dukiya suna dulmiyar dake suna rudar dake!, yayinda su nasu yayayen suna cen a killace a nasu gidajen a garkame. Auren da ze gagareki nan baba su nasu yayan na gata suke zasu musu wanda dan gwamna se yar gwamna! Yar minister kuma se dan chiaman, Dan shugaban qasa kuma se yar minister'n kudi ko mimister'n fetur!!! Yayinda ke kuwa aure ze gagareki koda dame daukar ruwan layin kune sabida wanda suke batancin dake sune dai zasu koma su zageki!!!” Wani numfashin bacin rai ta fesar kafin taci gaba da fadin. ”Koda yaron abokanansu sukaji zasu aureki zasuce ke yar bariki ce! Yar Bariki shine sunan dazaki samu daga bakunansu amaimakon Fatima ko *TESTY* din da suke kiranki dashi!!! Ya kamata zuwa yanzu Kima kanki fada fatima ki saisaita nustuwarki da rayuwarki” Dan tabe baki fatima tayi tace ”Bari kiji ko annabi dakanshi yace mu nemi tsari da talauci daga wurin mahaliccin bayi!, Sanin kanki ne kin rigada kinsan irin kuncin rayuwar da muke a ciki. Duniya taki kowa kanshi kadai ya sani, Masu kudi basa bada taimako domin Allah talaka yana cikin wani irin hali na kani kayi, da qyar da sidin goshi kake samun na break, wani kuma saiya kwana ya wuni be ciba alhalin ga masu kudin cennn sun tara sun rasa yadda zasu dashi. Ba dole muje su amfanu da albarkatun jikinmu su bamu mu kashe wutar gaban mu. yanzu kuma Allah yamun hanyar kasuwanci bazan cuci kaina ba allah ma ya gani” Fatima
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54