Chapter 35
Chapter 35
wacce ya kira da umayma ta furta . "kada ka samu damuwa malam insha allah allah shine zai kayo mana dauki lokacin da bamuyi zata ko tsammata ba bi'izinillahi" "amma ke ina iya ganin damuwa akan fuskarki umaymatu, kuma kinsan bazan iya juriyar hakan ba" da sauri ta juya tana barin wurin domin kada ta raunatawa mijin nata zuciya..... kanta ta hade da jikin bakin kofar da take tsaye hawaye masu zafin gaske na zubo mata. tana tsananin umminta da babanta, wai sai zuwa yaushe rayuwa zataji kansu su fita a halin kani kayin da suke a ciki na halin rayuwa? sai zuwa yaushe suma zasu dandani irin yadda zakin rayuwa yake?. "Ya Allah!" mariya ta furta cikin wata iriyar raunatacciyar murya. sallan magriba da aka kira ne ya fitar da baban mariya cikin tawakkali da karfin zuciya. Cikin sanyin halinta kamar koda yaushe anutse ta mike kanta duke a kasa, saidai ahankali take matse lips dinta da kyawawan teeth dinta. kai tsaye gaban dan karamin fanfom dake gaban bishiyar mangoron gidan ta nufa....alwala ta daura tana jin duk ma yanayin baya mata dadi baki daya. shi kuwa malam auwalu da mutanen anguwa ke kiransa da baban mariya bayan idar da sallar isha'i, dake shine lilaman masallacin anguwar yana zaune har saida kowa ya gama fita kana ya mike da zimmar fita. wata farar embulons ce ta fado daga saman jikinsa cikin rawar jiki ya shiga waige2 saidai baiga kowa ba.... saurin fitowa yayi a masallacin da shi ya fara cin karo,wani irin dafe kansa malam yusufa yay. me yasa aduk lokacin da yake da bukatar taimako sai shine kadai me taimakonsa. jiki a sanyaye ya karasa xuwa gaban farar motarshi da yake tsaye, sanye yake cikin kakin yan sandan shi kamar kullum. "Na rasa wanda zai taimakeni amma ba wanda ya taimakamin, duka na tambaya haka ban samuba! amma kai bamma tambayeka!" ya kasa karasa maganar shi sabo da kukan da yaci karfinsa. "Aina riga na fashimci komai dana kalli cikin idanuwanka. wannan ba komai bane" inspector KAMAL RANO ya fadi "bansan ta yayene zanyi wani abu game da yata ba. ban kuma san da wanne irin idon zan dubesu ita da mahaifiyarta na fada musu cewar auren ya fasaya!. bayan fitowana daga cikin gida zuwa masaaci. KAMAAL?" Malam yusufa ya kurayi sunan shi cikin karyewar zuciya. cikin tsananin.zafin dake narka kirjinsa ya furta. "A yau da kai danane dana zartar maka da wani hukunci kai tsaye! ko kuma in baka umarnin aikata min wani abu" idonsa daya tara kwalla ya dago yana kallom baban mariyan. kafin cikin muryan da kai tsaye ba zaka iya tantance taba yace. "Ya kuma zakace haka baba? kenan niba danka bane kome?. matsayinka a wurina ya wuce makwabtaka ni KAMAAL IDREES RANO A MATSAYIN MAHAIFI NAKE KALLONKA, ka bani ko wanne irin umarnine ni kuma in aiwatar maka shi cikin sauri da tsananin biyayya" hawaye da kuka ne suka zowa baban mariya lokaci daya, cikin jin yakini da kuma karfin zuciya ya furta.............. "KAMAAL A MATSAYINA NA MAHAIFINKA NA BAKA UMARNIN AUREN MARIYA!" wani irin dokawa kirjin kamaal yayi amma saiya danne hakan cikin cikakken bin umarnin nashi kamar yadda ya daukar masa alkawarin ya furta. "A MATSAYINA NA DANKA NA AMSHI AUREN MARIYA, AMANA SAI DAN AMANA! HALACCI SAI DAN HALAK, zan amshi wannan auren bisa wakilcin waliyina ABDOUL-MALEEK" Da karfin gaske ya rungume kamaal din yana fadin "nagode na gode nagade kwarai da gaske bana da haufi akan baka auren mariya da nayi kamaludden uban daraja uban kamala" ..........Umayma cikin karfin hali ta gama kammala girkinta bayan fitar mijin nata. har zuwa yanxun da bayan tayi sallar isha'i take zaune gaban dakin malam liman, da abincinsa da take jirayin shigowadsa! shigowar malam cikin tsantsan fara da kuma murmushin dake kwance saman fuskar sane ya sanya itama nata murmushin fita da sake fadada, "Alhamdullih umayma lallai Allah maji kan bayin sane ne, cikin hikimarsa da buwayarsa ya mana canji da mafificin alkhairinsa" ya fada yana kaiwa zaune kan tabarmar da umayman ke zaune, sai kuma ga kai dubansa dakin mariya tare da kwalla mata kira. "MARIYA" "na'am baba!" ta amsa shi cikin faduwaf gaba tana fitowa tare da tsugunnawa a gaban mahaifan nata. sannu da zuwa tama tayi mar kallonta yayi tare da mata nuni data zauna. zaman tayi tana sunkuyar da kansa kasa. "kaddara wata abace me tsanani haka kuma me sauki! sannan kuma wata abace da ba'a iya ganin launinta da ido, hakanne ma yasa ba'a iya sauyata daga mummuna zuwa kyakkyawa, acikin kowanne rayuwar ɗan Adam akwai salon tarin ƙkaddarori masu tarin yawa, akowacce duniya akuma koda yaushe kaddara tana tafiya ne daidai da rayuwa. Sannan kuma babu wani bawa wanda ka iya gujema tarin ƙkaddarorinsa. haka kuma ana haifar kowanne bawa ne da salon tashi ƙkaddarar, kisa a ranki shima musan baya cikin kyakykyar kaddararki mariya. domin kuwa iyayensa sun janye kamar yan baya, amma da ubangiji ya tashi miki zabinsa saiya sanja miki da mafificin duka sauran samarukan da suke fasa aurenki. data tashi saiya baki kamaludden me kamala, me karamchi, me nagarta ki amshi wannan zafin a matsayin zabin ubangiji domin kuwa shi kadai yasan manufarsa akan hakan" ita dai tunda baban nata ya fara fadar maganganunsa bakinsa kawai taga yana motsawa kamar sauran lokutan baya. Ita kuwa meta rayuwa da take juyin wainar masa da ita, daga wancen kasko zuwa wannan kasko? kodai ta aikata wani zunubine da yake ta bibiyar rayuwarta?. *KUWAIT* ***** ***** Cike titin yake da motoci ba komai ya haddas hakan ba sai wani uban shegen go slow da wata ƙshegiyar bakar mota mai kyan gaske ta hada kirar lexus. anyi crossing dinta akan titin yadda ta rufe titin completely duk glasses dinta tinted ne. dan haka ba'a hangar wanda yake cikin motar,mutane sai hayaniya suke. kallo daya zaka ma motar kasan ba dan karamin kudi aka narka wajen siyar motar ba. gurin ya cunkushe mutane sai hayaniya suke yi,abu mafi ban mamakin shine normally gurin yake babu traffic, murfin wata farar mota aka bude wata kyakykyawar matashiyar budurwa ta fito sanye cikin shigarsu irin na larabawa. bakar abayane a jikinta tayi rolling da siririn vail abayar, sai bakin shadow data sanya a fuskanta da alamu sabo da kare hasken rana ta sanya shi. kai tsaye inda akayi bloocking hanyar ta nufa a nutsenta. cikin harshen larabci wani matashin balarabe ya furta "yan kibi a hankali mutumin is very dangerous, shegun kasar kuwait kenan ake magana anan" ko inda yake bata kalla ba saima ci gaba da tafiyarta da tayi. wasu shegun manyan motocine guda shida suka ratso ta cikin titin da wannnan motar tayi blocking hanyan, dole sukaci burki suma kafin mamallakin motocin wanda yake sanye cikin wata iriyar shiga ta alfarma ya bama daya daga cikin tight security'n umarni ha duba ya gani mene ya haddasa wannnan go slow din. "ba bukatar a duba ZAID EMAAR'S ne" mahboob ya fadi dake zaune a kusa da sit driver. "innalillahi yanxun dama gantalewar zaid din shima harya kai haka? bayan shigo mana gida a bugu banda yawon club's club's dinsa ashe harda tarema mutane hanya ya iya!" cewar MOH JIDDO da take zaune a kusa da AL-HUSSEIN EMAAR'S. a mugun fusace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54