Skip to content

Chapter 4

Chapter 4

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

yaja plantain chips ya fara cakuta kaɗan yaɗan taɓa ya tashi tare da wine ɗin ya koma kan caution ɗin parlourn ya kafa bakinsa ya fara sha inda saida Ya shanye Kafin ya ajiye bottle ɗin. Laptop ya janyo tare da buɗe mukullan sirrin ya shiga sarrafa abarsa cikin kwarewa. A rikice a kuma ɗimauce Rooney ya faɗo ɗakin cikin tashin hankali ya nufi ogan nasu kai tsaye, system ɗin dake hannunsa ya dire gaban uban gidan nasu. A tare miles axton lani da kuma Vincent suka ja baya suna toshe bakunansu, hankali tashe suka juyo baki ɗaya da nufin Boss ya kalla laptop ɗin, amma ga mamakinsu abinda suka kalla ɗin ya tada musu hankali shine Boss ɗin nasu yake kalla hankali kwance tamkar babu abinda ke damunsa ko kuma ya girgiza shi. A baɗini kuwa wata iriyar tsuma namomin jikinsa suka ɗauka.bai motsa da ga zaman da yay a lallausar kujerar ba ƙafa ɗaya kan ɗaya. Yayinda bayansa ke kishin kiɗe jikin kujerar kansa a sama kaɗan, Yanda yay biris ɗin sai ka ɗauka baima fahimtci kamai dangane da hakan ba, Yaja kusan 10 mint kafin yaja wani irin huci ya furzar yana mai buɗe rinannun idanunsa da suka sake wani irin garai-garai ai nahin suffarsu ta idanun mage na sake bayyana a fili. Zaune ya tashi da ƙyau sai dai a nutsensa yake Samm babu alamun firgicewa a tare dashi,Sudai baki ɗaya sun gaza samun Nutsuwa sai kai da koma suke famar yi a cikin parlourn, suna a cikin wannan alhinin ne kuma get man na gidan ya faɗo parlourn against. "Boss da akwai matsala" Wani irin rumtse idanunsa yayi a duniya kalma mafi muni daya tsani ji itace kalmar yaji an ambaci matsala, ya tsani jin kalmar andaɗe da fice wannan babin, don haka ya kalli get man ɗin tare da ɗunkule hannunsa tamkar wanda zai kai naushi, sai kuma ya kaima iska naushin, yana fesar da wani zazzafan Numfashi, loƙaci kaɗan kamanninsa suka sanja jikinsa ya shiga rawa kana ganinsa zaka san he is not on his mood,musamman yadda yanayin jikinsa ya sanja tare da wani irin tsuma. Cigarettes ɗin dake jere gabansa ya ɗauka a zuciye da sauri Vincent yazo gaban sa tare da kunna masa lighter ya fara zuƙarta a haukace, cikin ƙankanin loƙaci ya har gitsa parlourn da hayaƙin cigarette. Saida zuƙe wajen kara biyar kafin yaji zuciyarsa ta ɗan risina, cikin hosky voice nashi ya furta "A tura saƙon kai tsaye!, Vincent maza a nemo mana biza daga nan zuwa yamma" "An gama Boss" Suma suka haɗe baki wajen faɗar hakan suna fita daga parlourn baki ɗaynsu, Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga parlourn ya nufi bedroom ɗinsa. Zaune yakai saman lafiyayyan gadonsa Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane Abubuwane kawai suke masa kai-komo a rai da suka wayi gari dasu. Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba, domin zai iya cewa kusan a haka ya rayu, Amma na yau ɗin sai yafi ƙona zuciyar sa fiye da koda yaushe,dan duk sunzo masa a bazata ne. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba. Goran ruwan dake a Centre table ɗin ya ɗauka. Batare da yabi takan kofin dake kusa da ita ba ya ɓalle murfin kawai yakai bakinsa ya fara kwankwaɗa, Sai da ya shanyesa tas sannan yayi cilli da bottle ɗin. Sake furzar da huci mai zafi yayi a karo na ba adadi yana sake nutsar da kansa. Sosai abubuwa masu yawan gaske suka shiga ƙoƙarin zeroying Brain nashi. Tamkar kuma wanda aka zabura ya miƙe aɗan zafafe yana yin gaban ƙofan Glass ɗin dake a shafe da Pics manya na emeji me hoton lion, babbar yatsar hannunsa ya sanya a take wurin dake a shafe yayi On tamprint na yatsunsa, zuuuuuuu wata haɗaɗɗiyar ultra door ta baiyana. Wasu manyan Computers ne A ɗakin dasu jojjone ta ko wacce kusurwa dake ɓangaren, akan wani ƙayatacce dogon table saikuma macbook akan wani dogon lumtsatsen kujera, Zama cikin hanzari tare da ɗaukar MacBook ɗin dake kan kujerar, buɗewa yayi yafara aiki cikin ƙwarewarsa da kuma baiwar iya sarrafa ko wanne abu, yakai kusan 40min yana danne danne, wata iriyar ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya tashi yana barin ɗakin da yafi kama dana bincike. Yana fitowa daga wannan ɗakin ya ciro iphone XR ɗin sa, NO na Vincent yayi dialing NO In, cikin ƙanƙanin loƙaci daga ɗaya ɓangaren ya cira wayar yana faɗin "Boss" "Get ready to go out operations!" Da wannan ƙasaitar nashi yayi maganar yana zare farar Morocco ta mazan dake jikinsa, cikin sauri sauri ya shirya kansa cikin straight leg trim trouser sai black Versace greco hoodie, ƙafafunsa sanye cikin wasu haɗaɗɗaun black hermes cover shoe, sai hannunshi sanye cikin wasu haɗaɗɗun safan hannu, ga kuma facemask ɗin dake saman fuskarsa dake saye cikin sun glasses ɓaki wuliƙ dashi. Yana fitowa coumpaund ɗin tuni wannan samudawan sukayi shiri na musamman sun ɗane cikin rantsatstun baƙaƙen motocin su. Suna ganinsa suka hau fito da shewa suna faɗin "BOSS! BOSS!! BOSS!!!" Cikin wani irin salo da ƙwarewa Miles ya yayi tsalle ya diro yana shirin buɗewa Boss In nasu car, hannunsa dake a rufe ruff ya ɗaga masa yana mashi nuni da power bike ride ɗin da zai hau, sara masa yayi yana komawa cikin motar, shi kuma cikin wani irin taku ya nufi power bike ɗin tare da daura hannunsa akan key na machine ɗin, wani irin tsalle yayi cikin salon daya zam ɗabi'arsa ya haye saman machine ɗin, tare da masa key wani irin kuka yayi machine ɗin ya ɗauka. Kasancewar shine a gaba ya sake daidaita machine ɗin Cikin sallon ƙasaitarsa ya ɗaga hannunsa sama ƙaramin yatsansa ya fara musu wata alamar dasu kaɗai suka san ma'anar kayansu. Suna gama fashimtar haka yaja machine ɗin da wani irin azababben gudu ya fita a gidan baki ɗaya, suuuuuu motocin suma suka rufa masa baya Sosai motocin ke sheƙ uban gudu a titi tamkar suna a jerin gasar tsere, bakajin komai sai ƙara ƙainarsu, Da yawan sauran motocin dake a kan titin sauƙa suke gefen hanya domin basu fili, ganin yadda suke zuga uban gudu na tashin hankali, dan duk mai hankalin da yaga wannan gudun yasan bana lafiya bane ba. Kai tsaye Lekki suka nufa daidai wani mahaukacin ƙaton luzary suka kutsa kansu, tuni jami'an tsaron gidan suka soma sakar musu wata. Wani irin sakin kan machine ɗin yayi tare da Ciro wasu bindigogi guda biyu kirar berreta M9, tsalle ɗaya yayi ya diro akan power bike ɗin ya fara tafiya kamar irin fusataccen zakin nan, Saida yayi pulling trigger Kafin cikin wani ƙayatacce salo ya soma harba bindigar. A gigice Governor Ibrahim Khaleel Nasara dake zaune irishe irishe acikin mahaukacin parlourn sa yayi wani tsalle kamar mage ya haye saman lumtsememiyar kujerar jikinsa na kerma, minister Zubairu tanbuwal kuwa rasa ma yadda zai yi yayi sai kawai yayi knell down a tsakar parlourn. Acen coumpaund na gidan kuwa Sosae jami'an tsaron suke neman gagararsu

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54