Chapter 24
Chapter 24
da ice da fire I have used the ice. Ta ya kake tunanin karamar kwakwalwarka ya gaya maka daidai? Ko dai ka manta *SARKI NE SHI A DAWA?*" A matukar fusace Ajmaal ya daga bindigarsa ya dana akan Armstrong yana shirin d'ana kunamar binfigar nashi. ”Ajmaal stop!!!” Mr president da shigowarsa kenan ya furta cikin rawar jiki, da dacin murya amma ina tuni Ajmaal yaaaaaaa........ ★★★ AK POV Fitowarsa cikin takun nan nasa na isa da izza tamkar babu wani abinda ke damunsa ya saka uban guards din dake harabar gidan nutsuwa. Cikin Tsananin kwarjininsa da gizagon da kullum ke sanya zuciyar magauta nutsuwa, lullebe a akan kyakykyawar fuskar dake nan tamkar hadarin daya kunshi ruwa yaki ya fashe. Sanye yake cikin ash wandon fendi da farar rigar rugby shirt sai blue Lorenzo snickers a sawayensa. Fuskar nan saye cikin Sun glasses sai nose mark daya sanya. Da sauri daya daga cikin samudawansa ya bude masa wata shegiyar blue car 2024 Bugatti, Cikin tsantsan jin kai ya shige cikin motar rufewa yayi driver ya bata wuta, Sauran motacin na Mara musu baya....... *ISA MANU empire* Hannuwansa goye a bayansa baki daya kansa ya kulle yama rasa wanne tunani zaiyi, ”Dom ITT" Ya fada cikin daga sauti. Wanda kuma yayi daidai da shigowar Salman a rike ce. Ganin yanayin daya tadda dad nashi ya sanya hankalinsa sake tashi over,Saida ya dan fesar da wani zazzafan numfashi kana ya furta. "An dauke Assembly leader wayewar garin yau na Serevellar” “What!?” Isa manu ya fada da karfin masifa tare da kaiwa kasa yana fidda numfashin da yaso sarkeshi sama². Komai bai Iya furtawa a lokacin saida ya debi wasu minutes kafin ya furta. “Lallai yau duk yanda za'ai ina bukatar ayi zanga zangar nan, Kaiiiiiiii abin yayi yawa haka nan, nasan next target nine kuma ko kai” Yayi maganar zuciyarsa na wani irin beating very fast........ Cikin abinda bai gaza 50 minutes ba gangar samari yan ko ta kwana suka gama hallara kansa a babban gidan gonar Isa manu. *By AMMEY LAYLERH📝💐* *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page 25&26 # ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # BEST LOVE 🤍🔥✅ ★★★★ *5:55am* Cincirindon matasan suka zagaye babbar police ɗin dake birnin Lagos da kuma headquarters na sojoji, Suna faɗin *ADALCI* suke so. Su a fito musu da gwamnansu tare da ministan su da assembly leader nasu. Wannan zanga-zangar ta matasan ce ta kuma janyo hankulan jama'a kansu, dan danan cikin mitsitsin loƙaci jama'ar gari suma suka firfito ana zanga-zangar dasu, kafin kace meye Social media ma ta ɗauka. Suna son soldier's da police's su jajirce wajen dawo musu da governor da minister'nsu tare da Assembly leader, Tuni wannan zanga-zangar ta yau lanar Laraba ta zama latest a kafafen yaɗà labarai. Irinsu magazine, Television, Radio. Su Isa Manu da suke cikin gidajensu suna kallon duk abinda ke faruwa tuni suka cika da maɗaukakin farin ciki, lallai haƙarsu ta cimma ruwa dama abinda suke da buƙatar kenan. A tada hazo a cikin garin na Lagos dama kewayenta. Acen kuwa cikin babbar police da kuma headquarters ɗin kuwa duk da barkonon tsohuwar da aka baɗesu dashi sunƙi ko gezau balle su gudu. Ga na cikin gari ma hakan take dole ƴan sanda dama sojoji suka bazu ko ina don bada tsaro wa al'umma. ******* *MEERAH* A Yau Lahadi akayi adda'ar sadakar ukun Affan wanda har zuwa wannan loƙacin meerah na'a cikin alhinin mutuwar. Daren daya kasance dare mafi matuƙar muni a cikin tarihin rayuwar meerah, domin Sai yanxun mutuwar Affan ya dawo mata sabuwa filll. Domin sai yanxu ta sake tabbatar da cewar ehhhhhh lallai ta yarda ta rasa Affan ɗin ta har gaban abada abadan abada kenan, A wannan dare na sadakar ukun ta kasa rumtsa kwayar idonta shi yasa ta ƙira daren da baƙin dare. Dare ne mai ɗauke da tsananin duhu tare da cushewar yanayi kasancewar babu yalwar iska ko kaɗan dake kai komo acikin gari, yayinda sama tayi duhu dulum kasancewar babu hasken farin wata ko ɗigo, haka ma hasken taurari duk sun disashe wannan yana ɗaya daga cikin abunda yasa duniyar tayi mata tsananin duhu, yayinda ko ina ya zama shiru babu motsin kowa a cikin gidan sai ita kaɗai da take kowawa da numfashinta. kasancewar adaidai irin wannan loƙacin kaso 90 acikin 100 na mutanen duniya bacci sukeyi, saboda kowa yasan akance *DARE* mahutar bawa. Saidai awani ɓangare tsawon awanni ashirin da bakwai kenan da MEERAH ke kokawa da numfashin dake shirin barin gangar jikinta.Luuuuuuu idanunta suka rufe kirib, yayinda bugun zuciyarta ya yi ƙasa sosai kasancewar ta jima da fita acikin hayyacinta, wannan yasa ta shafe tsawon awanni 30 batare da tasan duniyar da take ba, ta manta wacece ita da kuma duk wani abu daya shafe ta, ta manta da Cewar an taɓa halittan wata jinsi irinta, komai ya tsaya mata ne cak kamar ba’a taɓa wanzar da ita adoron duniyar ba. Ammma sai' gashi cikin hukunci na Ubangiji maji ƙan bayinsa cikin ƙarin wasu awanni, numfashi ya fara ziyartar wannan kirjin daya jima ba tare da ya shaƙi numfashin duniya ba, wanda hakan yasa ahankali ta soma motsa babbar ƴar yatsar ƙafarta wacce ta ƙame waje guda, A loƙacin da numfashinta ya gama daidai ta a kuma wannan loƙacin ne wani irin ɗaci da ciwo me gigita zuciya ya ya sake sarƙafe tsaƙiyar ƙirjinta. “MEERAH?...” Amma ta ƙira sunanta cikin sautin fitar amon daya sake gigita duniyar Meerah, wanda tarin ƙalubalen da take kan fuskanta ke haifar mata, wani irin rumtse idanunta tayi tare da matse hannuwanta dake rawa sosae. Wani irin mashahurin sanyi na ratsa cikin jikinta. Da sauri Anne ta ƙarasa shigowa ganin kamar Didinta bata a mood me daɗi, domin yau ita ce da malam Abdullahi haka kawai jikinta ya bata Didinta ba lafiya ba. Zaune takai gefen gadon da take kwance. Wata guntuwar kwalla data tarummata ta share zuciyarta na mata suya..... _Shin sai xuwa yaushe zata dena zubar da hawaye akan ƙaddara?_ _Shin yaushe ne babin rayuwar su zai juye zuwa wani mataki na daban?_ _Shi sai xuwa yaushe rayuwarta ita da ƴaƴan ta zatayi haske? Yaushe zasuji daɗin rayuwa ita da ƴaƴanta kamar ko Rai me numfashi?, Yaushe haske zai ratsa cikin rayuwar kowannensu?_ _Shi dama laifi ne dan ƙaddararsu tazo musu a yadda ba suyi zato ko tsammani ba?, Ashe haka duk wata ɗiya ta kwarai take ji idan aka shegentaka? Wani irin ɗaci da raɗaɗi me zafin gaske take ji a duk loƙacin da kishiyoyinta suka jefeta da kalmar shegiya_ _Bafa ita ta zaɓama kanta tasowa a inda babu kowa nata ba! Bafa zaɓen ƙaddararta tayi, ba itace ta zaɓi da rayuwa tayi ta watan gaririwa da itaba, ba kuma itace ta tsara ma kanta yanayin rayuwar da suke ba. Ta buɗe idontane kawai ta ganta inda bata san kowa nata ba, ba UWA ba Uba, ba ƴar uwa ba ɗan uwa. Babu kowa nata data sani itama tsintar kanta kawai tayi a cikin rayuwar da take a yanzu tsumu-tsumu, Tana ƙara roƙon Allah har kwanan gobe Ubangiji karya ɗauki rayuwarta saiya bayyana mata wani nata a duniya........._ _Tana son ta tambayi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54