Skip to content

Chapter 51

Chapter 51

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

wani dan iskan salo. Tun kamin motarsu ta gama parking dolly dake sanye cikin wasu shegun outfit riga da wanda na baxon ta balle murfin motar fa fito. Akan inda giya, shisha, cigarette's coc suke ta fara nufa kai tsaye. Shishar ta dauka ta mata wata kafurar zuka tana baza hayakinta daya hada hoton love. Zaune takai akan almurun kujera. Tana zare wawakeken shade din daya kusan cinye rabin fuskarta. Mafi hankalunan yayan ajebor din dake zagaye da wurin ne ya dawo kanta, Nanfa suka mata caaa aka har wasun su na kakarin kama hannuta donsu shakata tare da ita. Kai tsaye club dancing din ta shige ya soma wata kalar rawar daya sanya manyan yaran daukar ihuuuuuuu suna sowa. Nan fa kowa ga fara kokarin isa ga dolly saidai taki ba kowa damar hakan. Har suka karaci shedancinsu suka tashi wajajen karfe biyun dare. ★★KANO★★ Idan muka koma kano kuwa sosae rayuwar kamal da mariya ke gudana cikin kanciyar hankali, akwai girmama juna a tsakanunsu sosae suna zamansu lafiya yau kimanin kwanakj tara kenan da aurensu. Amma babu abinda ya taba shiga tsakaninsu. Hasalima kowa daki daban yake kwana abinsa. Sammm daga shi har ita babu abinda ya dame su kowa ya harkan gabansa. A kullum zata shiga dakinsa ta gyaro masa ta kuma wanke masa ƙananan kayansa a washing machine. Kamar kullum yanzu ma aikin gyaran ɗakin take hankalinta kwance, ɗomin dama sauya fita take shigowa ta gama masa Aiyukansa ta tafiyarta. Riga da wando ne a jikinta na palazzo ride vizzon ruwan kasa inda rigar ta kasance baka irin me kamar robar nan. Kanta babu ɗan kwali sai fakin gashinta da tayi a ƙasan ƙeyarta. Bluetooth ne a kunne ya tanaji latest waƙar Hamisu Breaker me taken mu daina TSORO. Wanda wakar yake ratsa zuciyanta kai tsaye, domin tabbas talakan kasa shine a wahale babu tsoron Allah a zuciyoyin shuagabannin mu. Kana babu tsoron Allah a wajen wasu jami'an kasar. Tun ɗazu yake tsaye yana kallonta a ƙalla ya mata sallama sama da sau uku amma shiru bama ta jishi ba. Wani kakan shagaltar yayi a kallonta yadda take motsa ƙananun laɓɓanta shi yafi komai tafiya da imaninsa, aikinta take cikin nishadi da nutsuwa harta kammala ta juyo da biyar tafiya, Nan sukayi hudu dashi saurin ja baya tayi tana sunkuyar da kanta kasa tare da faɗin. "Kayi mantuwa ne yaya?" Ta tambaye shi,shiru ya mata yana sake kureta da mayen kallonsa. Jikinta ne ya ɗan soma rawa kaɗan Idanunta na cikowa da kwalla. Gudun ko ganinta a dakin sane ya ɓata ransa, "Don Allah kayi hakuri!" Ta fadi muryanta na karyewar sansomin kuka. Komai baice mata ba haka ta raba gefensa ta wuce.... Taku ɗaya tayi a na biyu taji lallausan hannunsa cikin tafin hannunta, cak ta tsaya zuciyanta na bugawa domin duk tsawon zamansu ko yatsarta be taɓa kwatankwacin kamawaba. Juyowa tayi Idanunta na zube da hawayen da take ta kokarin ganin boyewa. Ta buɗe baki kenan da biyar sake bashi hakuri ya taryi nata numfashin ta faɗin. ★I LOVE YOU★ Wani irin yankar kirjinta taji yayi numfashin na kokarin barin gangar jikinta. Dagowa tayi a tsorace hakan ne ya bashi daman tallafar fuskanta yana jefa idanunsa cikin tsakiyar nata idanun. Wani kalan mamular baki tayi Idanunta na far far. ★And I really love you 2 appreciate my love★ Kalamansa suka dade mata dirar MIKIYA a tsakar kanta. "I lOBE YHU MARRIYERTOU" ya sake faɗi yana janyo ta zuwa cikin jikinsa. Xuwa lokacin kuwa ƙafafun kariya sun soma rawa tana dab da kaiwa kasa ya rigata yana dorata a kan ƙafafunsa. Ji da ganinta ne suka dauke na wuccin gadi, {KAMAAL?} Ta tambayi zuciyarta ta hanyar furta sunan sa a cikin zuciyar. Hannuwansa dake cikin nata har loƙacin ta damke da karfin daya sanya kamal ɗago kansa yana me sake dubanta kaɗan. (KAMAAL!) ba tare data sake fargaba zuciyanta ya ƙara ambatar sunan. "Yeah KAMAAL SURAJ RANO na tsananin ƙaunar MARRIYERTOU fiye da duk yadda zaki zata" "Kasan kuwa da wace kake tare?. Tare kake da Mariya Mariyan da sau uku anasa bikinta ana fasawa, wannan mara sa'ar! Wannan wacce ba kowa bace ita fa ce wacce ta tashi cikin tsananin rayuwa? Sammm Ni banyi zubi da kalan matar auren kaba yaya KAMAAL, A nawa tunanin ka aure nine domin cire mahaifina daga cikin damuwa. Ka aure ni domin kana tausayinmu wacce zaka iya sak........ Bata karasa ba ya rufe bakinta da nashi tsawon minti uku. Sai kuma ya ɗago idanunsa na tara ruwa. "Na aurekine don ina sonki MARRIYERTOU! Na aureki bisa jagorancin zuciyata domin tun baki kai haka ba nake jinki har cikin raina!, Yanayin nutsuwarki, kamalarki haɗi da kyawawan halayenki ban bayyana miki bane gudun kada na ɓata alaƙarki da tsofaffin samarinki. Amma sai gashi Allah ya bani ke ta inda banyi zata ko tsammata ba!. Sai da nayi azumin kwana uku na nuna godiyata ga Allah daya bani ke a matsayin matar aure na, Alfarmar dazan nema daga gareki shine kawai ki SONI!, Ki SONI kada kwatankwacin yadda nake muku ne inason mu rayu cikin aminci bisa jagorancin tsabtatacciyar soyayyar da zamu gudanar a cikin rayuwar zaman aurenmu!" Sosae ta sake ƙanƙameshi tare da sake shigewa cikin jikinsa tana sakin wani irin kukan da batasan dana me zata ƙirashi ba, kukan farin ciki ko akasin haka?.... "Nasha tazarar dake tsakanin mu irin tazarar sama da kasa ne yaya KAMAAL! Na zata SO be yimin adalci bane dana kamu da son wanda nasan bazan taɓa samu ba har gaban abada a matsayin mijin aurena. Nima INASON KA YAYA KAMAAL! Inaga tun kamin ka kamu da soyayya nina kamu da taka soyayyar yaya KAMAAL. A zatona kamin zarra kafi karfina tako ina Shi yasa na bisne hakan a cikin cannn karshen zuciyata! I LOVE YOU FOR EVERYTHING my Ayh" Kanta ya dora akan kirjinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugu fat fat. "Da gaske kike? Da gaske kina sona Mrs Ayh?" Ya fadi kuma yana jefa idonsa cikin tsakiyar idonta, kanta ta gyada mishi tana sake lafewa a jikinsa..... Bakinsa ya haɗe da nata daga zaunen yana mata wani irin lafiyayyan Romance. Daukarta yayi cilak yana shigewa bedroom nashi, a ƙalla sun ɗauki good 30 minutes kana suka fito hannunsa riƙe da files ɗin daya dawo ɗauka...... Wurin aikinsa ya koma kai tsaye domin kota halin yayane so yake saiya cafke me lefin nan, haka zai ci gaba da zakulo manyan masu laifukan da suke ɓuya ta karkashin kasa. Kai tsaye Lafiyayyen office nashi ya wuce Saida yayi wasu ƴan rubuce rubuce akan file ɗin kafin ya janyo laptop dinsa copying komai yayi ta ciki. Wayansa da yay ƙara ne ya fidda woyace me muhimmanci dole ya amsa, bayan sun gama ya kunna data da niyar turo sako ta Whatsapp sai abubuwa suka yi ta faɗowa saman screen ɗin woyan musamman ta peonies. Da niyar share sakonnin Ni yaje amma saiya dakata ganin hoton kamilallar fuskan da bazai taɓa mantawa da ita bane akayi wasu rubutuka akai. Kai tsaye ya gane pisc ɗin na ranar dazai bar kasar ne. ★WANTED?★ Ya sake maimaitawa wani guntun murmushi na kufce masa kaɗan. "Ya baku baya kuyi duk iya yinku har zuwa makura maza kuyi ta

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54