Chapter 48
Chapter 48
nufa yana a tsakiyarsu, sun sanya wasu kyawawan sandunan zinare gefe da gefen Ak din. Hasken streetlight din dake kewaye da ilahirin masarautar na sake Duk inda tawagar Ak suka gitta hadimai zubewa suke akan gwuwowunsu suna mika gaisuwa. Ko sau daya bai daga ido ya kalla kowa ba, sai hadimansa ne ke amsama duk wanda yay gaisuwarn. Tun a harabar shiga babban sashen me martaba sarki Hassan Al-hassan din ak ya dakatar da dukkanin hadiman. Sashen Sarkin⭐ shine shahi mafi kyawu da kawatuwa da duk wasu kayan kyale-ƙkyale a masarautar EMAAR's din. Gini ne da aka ginashi da zallar gilashi. Yana da hawa biyar dan haka sai da lifter kana kake isa apartment na sarki hassan din, Asalin apartment nashi kenan zama lissafa muku irin uban dukiyar da aka narka a ciki ainahin fadar me marta ban batama kai lokacine kawai. Su kansu dogayen benayen dake gine a fadar abin azo a kallo ne. Idan kahau hawan karshe kuwa na cikin ainihin fadae duk abinda ke faruwa a cikin masarauta EMAAR's din kana iya kalla daga saman fadar. Kai hatta da wajen masarautar ma kana iya hangowa. Hadiman dake tsaron sashen matsayin sojoji suka maye gurbinsu wajen take ma Ak din baya har xuwa parlourn farko. Anan din ma hadiman zubewa suka dingayi kasa kawunansu a risine domin girmamawa a gareshi har zuwa falon na biyu. Haka anan dinma wanda suke tare dashi zuwa parlou na biyu suka dakata, na falon na biyun na take masa baya har zuwa parlour na uku suma iyakarsu nan,Anan kuwa wani basamuden soja daya ne ya masa rakiyar wanda shine amintacce da yake iya haurawa har zuwa falo na hudun. Wani badakare ne kwalli daya tal a hawan karshen wanda saida amincewarsa ne kake iya ganin Sarki hassan Al-hassan kai tsaye din,Anan riga daka ha kwashi gaisuwa wurin Ak tare da bashi izinin ganin me martaba kai tsaye. Saida na'ura tayi kururuwar isowarshi tare da tantance shi kana ya sanya kansa zuwa hasalin FADAR EMAAR's din. Wani irin numfashi ya sauke me dumi yana jin yanda namomin jikinsa ke wata iriyar tsuma, Ahankali ya lumshe kaifaffan idonsa yana ambatar sunan Allah. Kafin ya sake bude idon ahankali kai tsaye akan MOH JIDDOH dake harde bisa kilisa tana cin inibi cike da ƙkasaita irin ta masu isa ya fara sauke idonsa. Itama daga idanun kadan tayi ta dube shi a sheke tare da zubarwa tare da kara hura hancinta sama, Wata Kujerar narkakken zinaren dake dunkule lik rug maga daka ya janwo zuwa gaban Ak. Wani irin zaune yakai zaman nan nasa mai cike da isa da tsantsar izza. Wanda hakan ke haukata wasun su domin zamane da yake fidda tsananin kwarjini da haibar da Subhanahu wata'ala ya masa. Crossing kafarsa yayi daya kan daya yana jan trow trey'n dake gaban MOH JIDDOH wanda yake shake da yayan itatuwa. Inebin dake narke cikin zuma ya dauka tare da kaiwa bakinsa yana dan cirar kadan. Wani irin motsa bakinsa yayi tare da lumshe idonsa saboda yadda tsananin zakin inibi da zumar suka tsinka yawun bakinsa. Tare da ratsa har tsakar kansa kai tsaye. Wani irin marin bazata takai ma fuskan Ak din da idonsa ke lumshe MOH JIDDOH tayi. A bazatan taji shima ya rike hannunta karafff tare da bude tsayayyun idonsa yana dan girgiza mata kansa. Irin I DON'T CARE MANNER's din nan. Kyawawan idanunta ta juya a fuskar Al-hussien sai kuma ta janyesu zuwa ga Mahboob da mandood. Dama duka sauran mutanen dake cike da dakin. Shi kuwa Ak dake rike da hannun Moh jiddoh yi yayi tamkar besan abinda ya aikata ba, saima maida idonsa da yayi yana sake kullewa. Yanda yai tamkar besan mike faruwa a wajen ba shine ya sake hasala Moh jiddoh.. Cikin muryan daya fara manyanta amma kuma yana fita da tsananin kaushi ta furta "Me kuke bukata da bazaku wanke min fuskan wannan tantirin yaron da mari ba! Kana kumin dumu dumu da jikinsa da duka? Ko saina baku umarni ehhhhh!!?" Ta fadi tana watsama su Alhussuen din wani mugun kallo. Cike da girmamawa Al-hussien ya dan rankwafa. Tare da fadin. "An gama Ya ummienah Umarninki shine abin jiranmu kana kuma wajibane a garemu" Kamar yanda be motsaba ba haka be bude idanuwansa. Saima karkada kafafuwansa da yake yi cikin isar da yake jin yakai koma ya zartata. Yunkurowa Al-hussien yayi da niyar kashe fuskan AK da mari. Wani irin bude idaniyarsa yayi tamkar zaki wurgi da hannun Moh yayi tare da damkar na Al-hussien din yana sauke firgitattun idonsa akan shi. Kafin ake yayi wani abu Moh ta dauke kyakykywar fuskarsa da wani lafiyayyan mari. "Ka sani HAU'WA KULU bata yafiya haka bata daukar kuskure koda kadan ne bare kuma me girma irin naka, ka sakar min da hannun yaro daka rike shi da kazamin hannunka da bashu da tsarki!. Ka sani taba hannun mutum irinsu Al-hussien sai hannun daya cika duka sharrudan musulinci, ba kazami irin naka ba daya gama cakuduwa da dattin zina" Atare Oum, Adeenerh, jesra, al-mustapha suka wani irin kulle idonsu da karfin masifa. "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!" Oum ta furta tare da RAZEENERH da suke kira da MAH. Mahaifiya Almustapha sai kuma yarta ta fari wacce tayi batan dabi sama kasa aka nemeta aka rasa. Shi kuwa boss din wani irin tsuma jinin jikinsa ya dauka. A fusace zaid da bazai iya jurema cin mutumcin da ake ba biyuninsa bane ya mike.yana toshe kunnuwansa tare da furta "STOP" Mandood ne ya mike tsayen shima ta hanyar tarar zaid din yana jefa masa wani shegen kallo tare da fadin. "Me yasa kake da taurin kaine?, Idan ba'a kasa dakai ba baka gaggawar dauka domin gudun abin fada ko martanin da za'a iya maida maka" Wani shegen kallo ya wurgama mandood din tare da cewa. "Niba rago bane da zan zauna a gaban idona naga ana aibanta jinina na kyale haka! Taurin kaine dani! Ni mutum ne da ako da yaushe yake cin nama da nama karya kasuwan nake nabi ta kansu na mitsitstsikesu domin na gama amfana da tsokar jikinsa" Luuuuuu Ak yaja idonsa dayabi zaid dashi kamad zai kulle su gaba daya sai kuma ya budesu war akan twins dinsa gudan jininsa zaid. Wani irin fashewa da kuka Moh tayi tana mikewa tsaye tare da fadin. "Tabbas jinin Maryam masifa ce a garemu, ni dama tun farko banso hassan ya aurita ba wllh! Har iyaka na ketara masa akan auren wannan me bakin jinin, na rantse ba zata shigo cikin gidan a matsayin matar aure amma saida ta shigo tazo ta haifa mana jaraba da masifa a masarauta" "Ashe kinga kenan baki da matsayi da iko akan dan da kike ikirarin naki ne, duk da kin yankamar iyaka amma saida ta ketara, kince ba zata shigo ta shigo! Ko wanne mutum yana da gari kana yana da iki a inda yake. Ba tare da kin tare ta daga shigowarma kuma ta shigo harta haifa miki magadan masarautar EMAAR's kina ji kina gani wannan masarautar ta zama tata. Wannan garin ya zama nata bayan wannan mene bakyason ta sake tsallaka miki, wannan masarautar tamu ce garin ma namu ne a gaban idonki zamu mulki masarautar dama kasar da kike ikirarin Oum bazara shigo
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54