Chapter 47
Chapter 47
din wandon cashmere nashi ya bayyana. Sannu a hankali sauran gangar jikin ma ta fito. Kaf wajen ya dauki wani irin tsitttt na bayyanuyar AK din tsaye akan diga digansa. Tsaye yake kam akan tsahonsa na tsayayyen namiji da babu ko rankwafawa. Lallausan cashmere din jikinsa da ba sai an zauna bata lokacin lissafin kudin da suka lashe ba. sun masifar zauna masa da tabbatar da Ak din a matsayin jaruminsa mai gwara kan naira ta yanda duk yaso bisa damar da Allah ya bashi. Kamilalliyar fuskar san nan ma'abociyar kamewa da tsare gida kamar kullum a tsuke, Saidai yau din ma dai akwai ring diamont barima manne da kunensa, hakama zanen tattoo dinsa mai fuskar lion na nan zaune daram. gashin nan daure daga kasan keyarsa ya dauresa har yana dan sauka jikinsa. Kai tsaye saiya fiti a hasalin balarabensa. Babu mai ganin idanunsa kasancewar toshe yake da shade mai duhu sosai. Wanda hakan shine ya sake bayyanar da taswurar halittar kyawun hancinsa daya zauna daram kan fuskarsa. Kafin kace mi tuni kamshinsa ya baje wajen, Gaba daya securityn ne suka sake kamewa kansu sukai cikin nuna tsantsar girmamawa a garesa. Wani irin dakune fuskansa yayi daidaj lokacin da fadawan ke zunewa akan gwawowinsu. Sassanyan iskan dake kadawa da kamshin furanni ya sake shaka. Kafin ya fara takawa a hankali cikin yanayin izza da zallar sarautar dake ratsa shi gaba da baya. Kai tsaye part dinsa dake tsakiyar masarautar ya nufa dake dama zaid da kanshi ya gyara may tare da jesra sukai aikin. Wohoho anan fa akeyinta mutanena Ni naga ikon Allah a wurin nan. Tashin kai tashin gari kenan, na tabbata idan mutum karamar kwakwalwa gareahi babu abinda zai hanata juyewa a wannan lokacin, zanso ace kunga yadda Nera da nera ke kuka a cikin bangaren Ak. Luxury da luxury life ake magana malam, komai dake Cikin bangaren luxury da luxury ne ka iya siyansa sa, wani irin mahaukacin passage ne me kayatarwa, a nutsetstsen lafiyayyen parlounshi na farko oummey'nshi sai jesra ne a zaune domin gani suke tamkar kafin goben abinda suke son gani ga gudan jinin nasu ya disashe. Wani irin murmushin bazatane ya bayyana a saman kyakykyawan farar fuskan shi da gudu jesra ta fada jikinsa tana saki kuka mara dalili. "Trouble meker har yanxun baki girma yhuyhu gurl" Sai kuma yadan yi jimmmm tuno waccen yarinyan da yayi. Oummey ce ta karaso itama tare da hugging yaronta tana sama lallausan gashin kansa. Gashin kansa tadan ja tare da balla masa harara irinta uwa da dan nan. "Ouchhhhh Ommu!" Ya fadi yana kaiwa durkushe gabanta..... *BY AMMEY LAYLERH* *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page 45&46 # ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # Hope # courage # Survival # Humanity # Inspiration 🤍🔥✅✅✔ Wani colourn kyakykyawan murmushi ta saki tana sake janyo kansa tana dorawa akan kafafunta. Kafin wasu hawaye masu zafi suka shiga zubo mata. "Garga me martaba! Lokacin bayyanuwar boyayyiyar gaskiya ne yayi, Alkawarin kare masarautar EMAAR's nake son kamin.... Ta fadi hawaye sosae na balle mata wani irin dauke kansa yayi yana kallon bayansa. Sai kuma ya juwo tamkar wani zaki ya goge mata hawaye ya ce, " You don't have to cry since you have me, i promise Insha ALLAH to be there for you no matter the weather, I promise to you and I promise to be your one and only till the end of time! Na dauki Alkawarin kawar da gurbatattun cikin masarautar nan Insha Allah Oummeyyy!!!" Ya fadi yana me dafa saman kanshi da hannunta yake hade da nashi hannun. Wata nannauyiyar ijiyar zuciya ta sauke tana mikewa tsaye. Ganin dare ne ya sanya oum yi masa sallama ita da jesra suka tafi, har bakin part dinsu ya mikasu da kansa cikin daya daga cikin motocin da suka daukosa. Shima zaid nashi bangaren ya wuce dake jikin ma ak din daga barin damarsa, kayan jikinsa ya zame tare fadawa bathroom wanka yayo duk da kuwa cewar dare ne, Silk kayan barci mara nauyi ya zira bayan ya feshe jikinsa da mayun turarukan. kai tsaye lafiyayyan hadadden gadonsa me kama da alkaki ya nufa. Dakatawa yay daga shirin kwanciyar da yake ya sake dora idanunaa akan yar karamar cctv footage din dake sakale tsakanin wasu manyan flowers guda biyu, murya kasa kasa ya furta. “camera?” Wani irin bacin raine ya ziyarceshi lokaci daya tare da furzar da huci mai zafi daga bakinsa, sai kuma ya cije lips inshi yana ayyana shikenan da aure ne ma dashi. Camarar ta riga ta gan may mata masu ita su gane masa sirrinsa, Sa'ar shi daya shi mutum ne da bai iya tsiraichi ba kowa shi kadan sane kuwa. Wani irin naushi ya kaima manyan flowers din a take suka tarwatse. ⭐ Duk wani lango da sako na bedroom din sai daya bincike ko ina. Babu wata kamara bayan wannan din dai, fasa kwanciyan yayi ya dau systerm nashi ya fara aiki cikinta, da dukkan alamu ransa a bace yake daga yanayin yadda yake sarrafa laptop din kadai zaka gane haka. Kiran sallar farko ya mike tare fadawa bathroom alwala ya dauro yana ficewa a part din kai tsaye. Babu wanda ya ganshi in banda ladanin daya kira sallar, Kai tsaye bangaren ladani ya nufa yana zama haka har mutane suka cika masallacin Aka tada sallah!. Babu wanda ya san da zuwansa haka babh wanda yayi tsammanin ganin a time din, Wannan nutsatstsiyan muryan nashi shine ya ankarar da mutanen dake cikin masallacin tare da zaburar da wasu da sanyasu faduwar gaba. Haka sautin kamilalliyar muryansa yacu gaba da tashi cikin kyakykyawar kira'arsa a cikin suratul Ma'ida. A kuma daidai lokacin me martaba ⭐ sarki Hassan Al-hassan gabban jikinsa suka fara motsawa ata sanadiyar jiwo wani babban gurbin dake cikin tsakiyar kokon Ranshi. Sanadiyar karatunsa daya karade baki daya katafanin cikin masarautar. Haka muryansa ya ringa karade ko ina da ina na cikin fadar tare da ratsa zukata, inda wannan muryan dai ke firgitar da wasu! Wasu kuwa ta saukar musu da nutsuwa tare sa sanyaya gabban jikkunansu. MOH JIDDOH kuwa wata kalan katantanwa tayi jin sautin fitar muryan da ko baka gaban me ita take da tsananin rusuna zuciyar mutum da ladabtar dashi. AL-HUSSIEN kuwa dake daya daga cikin na gaba gaban jam'i baima san sanda kafafunsa suka soma rawa ba yana neman kaiwa zaune. Amma ya dake yaki bama ko wacce alama nuna kanta a tattare dashi, Yana sanye ne cikin cikakkiyar shigarsu ta larabawa cikin wata farar kuwait jallabiya sai shiramin daya nade kansa dashi, sai wani farin glass din daya sanya. Bayan idar da sallarn nashi sosae yayi karatu tare da gabatar da adhkar, Har zuwa sanda gari ya fara haske. Xuwa lokacin manyan dogaran fada sun kewaye gaban babban masallacin musamman ma hanyar da zai fito ta wurin, Wambai, Waziri, maga tajarda, Riga daki, suna can sashen me martaba zaman isowar Garga din, Cikin wannan izzar da dan banzan takun nan nashi ya fito nan fa dogawarawan nan suka masa wani irin dafifi. Kowa nason bashi garkuwa wasu suna gaba wasu suna baya. Kai tsaye apartment din me martaba suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54