Chapter 21
Chapter 21
baya kawai taji an rungumata shiru tayi domin gudun kar tayi kuskure, domin tasan tana tsaƙiyar damisai ne masu farauta. "Me yasa jiya nata ƙiranki kizo ki tayani kwana amma kika ƙi amsa woyana?" Salman ya faɗa yana ɗaura haɓarsa kan wuyanta, "Ina bacci ne ban san ka ƙira ba" ta bashi amsa itama. "uyummmmm to yanxu da kika shareni fa? Ko shima baki gannin bane?" Ya sake jeho mata wata tambayar " kana son Hajiya tasan alaƙar dake tsakanin mu kenan?" Itama ta jefa masa Tata tambayar shiru yayi domin yasan baya da amsar da zai bata. "Daddy's boy wai me kake a kitchen ne bayan kuma kasan kai muke jira! Kana karka manta yau muna da fita ma" Saurin zareta a jikinsa yayi tare da fitowa yana faɗin "Naga tana wani aikin ne shi ne nayi tunanin ɗorawa amma nama fasa kawai right" Zama yayi tare da furta "good morning daddy..... "Morning how are you doing today daddy's boy....... "Fine with you?" "ALHAMDULILLAH" daga haka kowa yaja abinda ransa yake so suka fara breakfast nasu, good 30 minutes suka kammala suna gamawa bayan sun wanke hannayensu Salman da Isa Manu suka fice zuwa gidan iyayen MEERAH wanda a yau suke son cika ƙudirinsu. ★★★ *AK* Gudu sosai bugaggun motocin suke akan kwaltar da zata sadaka da wannan rantsatstsen Company'n na *LIVESTOCK AND FEEDING INTERPRICESS* duk inda suka gilma mutane basu hanyar wucewa suke, dubada da irin uban gudun da motocinsu keyi na tashin hankali. dukkan hanyar da suka biyo kowani mai abun ha wa ƙoƙari yake ya basu hanya kar a halakashi. Wasu na Allah wadai da su wasu kuma na musu fatan shiriya ne kawai. Ahankali yabuɗe idanunshi jin motocin sun tsaya buɗemai motar Armstrong yayi da sauri, fitowa yayi yana bin parking space ɗin wajen da kallo dayaji flowers da kallo komi looking neat a perfect kaman a dubai, wani guy ne fari dogo ya ƙara so wurin yana sanye da baƙin suit da necktie a wuyansa hannunsa riƙe da Ipad ƙirar apple. Cikin girmamawa ya sarama Ak ɗin da yake jingine da jikin motar yayi folding hannun sa a kan ƙirjinsa. Duk da yasan bai zama lallai ya amsa shi ba, Drectly cikin tamfatsetsen Company'n suka shiga, Armstrong, Axton, miles, ne kaɗai suka mara musu baya, duk inda suka gilma sai kaga idanu caaaaaa akan Ak kasancewar ba sananneba duk kuwa da cewar shine mai Company'n, Kasancewar Ak wani irin mutum ne mai murɗaɗɗan hali na rashin bayyana kai ko sirrinshi. Mutum ne da idan ba sanin shi kayi ba baka taba sanin shine mai amsa sunan Companonin dake zagaye da Nigeria. Don be yarda da baza sirrinshi ba irin yadda sanannun keyi shi yasa wani loƙacin harya shiga wuri ya fita ba'a taɓà sanin shine wannan me campanins ɗin, baka taɓa sanin shine wannan babban criminals ɗin, baka taɓa sanin shine *AK*. Kuma *ABDOUL-MALEEK EMAAR KUWAIT* He's not a social media fan. Restroom ɗin dake babban Company'n suka shige su biyar cifff, suna zama Kabeer ya matso tare da ɗan ranƙwafowa kan Ak ɗin, ɗan danna screen din ipad ɗin dayake riƙe da shi ya shiga masa bayani ta cikin ƙaton magazine ɗin dake room ɗin, A kan wani business daya taso musu da manyan tycon na ƙasashen woje. Bayan sun kammala tattaunawar ne Kabeer yace "Sai 5 marcopolo buses dazamuyi amfani dashi for excursion's" "All right okay" AK ya faɗa daga haka suka miƙe daga zaman tattaunawar, bayan sun biya ta breakroom sunyi ɗinner, daga nan *A MALEEK MEMORIAL ORPHANAGE HOUSE* ɗinsa suka nufa. Bayan ya gansu ya buƙaci a bashi list na abubuwan da suke buƙata,nan suka bashi ba tare da sunga fuskar saba kamar ko yaushe. Wasu mahaukatan kuɗi ya tura ta account ɗin Managern gidan. Daga nan *TEXTILE FEED INDUSTRY* suka nufa nan ma yaga yadda komi ke tafiya haka dai suka ta zagaya wurare daban-daban ta har dare, daga ƙarshe a wani haɗaɗɗen Restaurant suka yada zango nan sukayi ɗinner amma banda boss ɗin da yaki cin koma, Dole Armstrong ya mashi takawey . _WASHE GARI_ Yana kwance akan ƙayataccen Royal Italian bed nashi woyar shi da yay ƙara ya farkar dashi, kunne yakai woyar bayan yayi peak calling woyar. "Boss anyi arresting ɗin Armstrong a hanyarsa ta maida Meerah ga iyayenta." Wani ɗan banzan murmushi ne ya kuɓce mishi a bazata. (Aikin ka nakyau Lion) Ya faɗa acikin zuciyarsa a bayyane kuwa ajiyar zuciya ya sauƙe tare da datse ƙiran. A cennn station kuwa tunda suka samu damar arresting na Armstrong suka kulleshi a wani matsiyacin ɗakin kulle masu aika mugwayen lefuka. Kai tsaye hospital aka nufa da meerah bisa jagorancin Isa Manu daya samu damar ganawa da mahaifin meerah A safiyar jiya dan gane da neman aurenta ga babban ɗansa Salman. Kai tsaye dake Isa Manu sananne ne kasancewar shi Father's na manyan ƴan siyasa yasa malam Abdullahi amincewa da batun da yazo may. Daɗi da ƙari kuma duba da yadda yayi ruwa yayi tsaƙi akan ɓacewar Meerah. Saida lilitoci sukayi checking up nata suka tabbatar da babu wata matsalar bayan ta sleeping pawdern da suka shaƙa mata. Amma ce ta kwana wurinta wacce take tama Allah godiyar bayyana mata DIDI'ƊINTA da yayi cikin amincinsa. Tana zaune gaban gadon da MEERAH take kwance wacce tayi ƴar rama kaɗan wasu abubuwa ne suke mata kai da komo a tsakar kanta, Har bata ga sanda meerah ɗin ta farka ba sai ji tayi ta riƙo hannunta.... A hankali cikin muryan da yayi low sosae ta furta. "Anne na yauma mafarkin nake yi ko kamar yadda na saba?". Cikin maɗaukakin farin ciki Anne'n ta rumgume ƴarta cikin muryan kuka ta shiga faɗin. "Wannan ma mafarki bane DIDINA, wannan zahiri ne a zahirance Allah ya tseratar mana dake cikin amincinsa" Kanta ta ɗora a kan ƙafafun Anne'n tanaji inama itace ta samu damar da hawayenta yake zuba kamar yadda na Anne'nta ke zuba, ƙara cusa kanta tayi a wuyan Anne dake sheshsheƙar kuka ta lumshe. ido tana sauraren kukan Anne'n. Tana jin dama ita Allah zaiba damar yin irin wannan kukan, koba komai hawayenta zai wanko kaɗan daga cikin raunin dake danƙare a cikin zuciyarta. Saida Anne ta share hawayenta da bayan hannu kana ta ɗago fuskarta, ɗago MEERAH daga jikinta tayi cupping fuskarta a raunace cikin muryan kukan ta furta. "Yi kuka! Kiyi kuka MARYAM yi kuka!!!. Kana ki ɗauki hakan kamar haɗuwar hadarin kakane ya haɗa ,kuma ya baje ya ɓace ɓatt kamar komai ba'aiba. Karki bari abinda ya faru dake yayi tasiri a ranki dahar zai yi pinning ɗinki down. FIGHT DIDINA fight the feeling and move on!" Ai kuwa Atake ta fashe wani irin kuka me ƙona zuciya. Ɗauke guntuwar kwallar data saƙƙo masa malam Abdullahi yayi wanda yake tare da Isa Manu tare da Salman. Wanda ya kafe MEERAH da masifaffun idonsa ko kyaftawa babu, kaddai ace wannan zazzabar beb ɗin itace yarinyar da zasu yi Auren manufa da ita. Wllh Idan itace kuwa idan har aka aura masa ita babu shegen daya isa ya raba shi da wannan zazzafar bebyn. _DOWN_ _catafares_ _Slow motions_ _AK K he's going to shikenan *BY AMMEY LAYLERH 08104493215 *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54