Skip to content

Chapter 49

Chapter 49

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,190 words 0 views Progress saved
Download Book

ba. Saidai masu hadiyar zuciya su hadiya in yaso ta buga su mutu" Ak ya yaboma Moh maganfanun da tunda uwarta ta haifeta ba'a yaba mata koda kwatancinsu ba. "ABDOUL-MALEEK" Muryan Oum ya katse shi daga wata maganar da yake shirin sake yanko mata. Hatsaniyace sosai ta kaure a cikin dakin kowa yaki ya rusuna kowa ji yake da nasa zafin kan. Abinda ya rusunar da rigimar nasu faduwar da Oum tayi. Wannan shine dalilin lafawar komi haka Ak yama Oum dinsa daukar jarirai ya fice da abarsa zuwa clinic din masarautar, Shine da kansa ya duba Oum nashi kasancewarsa dactor, kana pilot ne idan yaso babu inda baya ketawa a kasashen duniya. Kana gashi Babban soldiers wanda matakin farko ma da Marshal ya soma..... ⭐Washe gari ⭐ A nutse yake Sakkowa daga matakalar benen zuwa entrance din da zai sada shi da bangaren oum dinsa. yana sanye cikin wasu fitinannun lallausan farin yadi. yayin da kuma ƙkafarsa ke sanye cikin wani black combat toms mai kyau irin na yayan sarakunan nan, Sai wata mini jacket din daya dora saman kayan yar filic da ita. babu abinda ke tashi ajikinsa sai wannan fitinannen kamshin turaren nan nasa me azabar tsada da bama wanda yake shakarsa cikakkiyar nutsuwa ta musamman. Tamkar wanda akema wanka da madara haka farar fatar jikinsa ke daukar idon me kallonsa. Cikin cikakkiyar takun da kallo daya zakayi masa ka gane cewar kakkarfa ne sabo da motsa jikin da yake aduk kwanan duniya ta hanyar machine gams. Blue eyes din nan rufe cikin wani luxury sun glasses wanda ya sake bayyana taswirar karan hancinsa da yake mike ziyat tamkar da biro aka zama masa shi daram. pink lips din nan nashi sai wani kalan glowing yake tsananin taushin na bayyanuwa wa me kallonsa, kallo daya zakama Ak ka gane shi din me kyau ne kana na musamman masha Allah,domin allah ya wadatashi da komi najin dadin rayuwa. cike da kwanciyar hankali da nutsuwa yake takawa irin takun dake nuna shidin kakkarfan namiji ne kana tsayayye. Marar daukan wargi da in Manners din nan. Kai tsaye babban katafaren parlourn Oum dinsa yama tsinke wanda girmansa yake dauke da wasu tsadaddun furnitures, parlour ne mara tarkace amma yana da kyau na fita daga hayyaci. Kayatattun royal cushion din dake zagaye da parlourn sunyi may kawanya, daga tsakiya kuma akwai wani shimfiɗaɗdiyar red carpet da throw pillows akai, sai wani ƙkaramin round table daga gaban wani kebantaccen rug, sai babban plat screen plasma din da ya kusa cinye bango guda na parloirn don girman shi. iskan A/cn dake kasawa kai tsaye yake fidda wani irin daddan yanayi a cikin parlourn, dubansa ya kai ga ƙkaton agogon dake manne a bango wanda yake ƙkawace da zanen pop, tare da pisc na Oum shi tare dame martaba. ⭐10:25am agogon ya buga cire pcarp din kansa yayi yana kallon ƙyakkyawar fuskan Oummey'nshi dake zaune kan caution mug ne a hannunta me dauke da zazzafan ruwan bunu marar madara. Kallo daya zaka mata kagane ita din mahaifiyarsa ce saboda kamar dake tsakaninsu, lumshe idanunsa yayi hadi da dan sauke numfashin ganin zaune cikin koshin lafiya da yayi. Cikin amon muryansa mai dadi da nutsuwa yace "Takabbalallahu minna wamin kum alaina wa'alaiki ya Oummey! ". Shafa tulin sumar kansa tayi wanda yasha gyara mai kyau da sheki yayin da yake durkushe agabanta ya dafa hannayensa duka biyu a ƙkafarta, cike da kulawa tace "Amin barkan mu da wayewar garin Alhamis lafiya habeebty" Jesra dake tsaye hannuwanta sarke akan kirjintane ta dan turo baki gaba tare da fadin. "Aifa shikenan nikam tawa ta kare tun da nakan gaban goshin ya dawo" Cikin yanayinsa na rashin son magana yayi dan murmushi yana faɗin "Kina kishi da hakan ne jes?” ya fadi hakan yana maida kallonsa ga mahaifiyar tasa yana faɗin "Ya Oummey nah ya saukin jikin ki?". " Alhamdulillah naji sauki tun da ka dubani HABEEBT?,kaje ga Me martaba ya kamata ka sake auna yanayinsa Garga" Kansa yayi noding yana mikewa tare sa barin shahin...... *BY AMMEY LAYLERH* *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page 47&48 # ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # Hope # courage # Survival # Humanity # Inspiration 🤍🔥✅✅✔ ⭐ NIGERIA ⭐ A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take yau din kace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙkaddarar jiyanka!. Rayuwa mataki biyu ce Acikin kowacce duniya duk wacce kaddararka ta zabar maka zata kaika ne zuwa makomarta, sabanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurbatacciya. A yau dai ga merrah wacce take dab da amsa sunan mrs Salma isa manu, wanda komi da komai ya gama kammala kansa daya danganci bikin aurensu wanda ya rage kwanaki biyu takkk. Kamar kullum yanzu ma zaune take a palon Annenta tana danna wayarta wajen karfe biyar da rabi na yammacin ranan alhamis. A zahiri danna wayar take amma a badinin ta ita kanta bazatace ga abinda take aikatawa a cikin wayar ba. Abinda kawai ta sani shine tana lallatsa wayar ne. Sallamar da aka yine ya sanyata dagota da kanga. Hajiya ummace ta shigo da sallama rataye da jaka a hannunta. Mikewa tayi ta nufeta tana murmushi ta amshi jakar tana fadin "Hajiya sannu da zuwa" Zama tayi akan kujerar palon kana ta amsa da cewar "Yauwa Merrah na biyo sahun kine dama kwana biyu shiru bakya zuwa. Ni na rasa wacce iriyar amaryace wannan ace gyaran jikinka ma gudunsa kake?' Kyaje gidan ne mijin ya koroki astagfiroullah Allah na tuba. Wllh tsaya kiji wannan bikin da naje Ikaja. Bayan kai amaryar da kwana biyu mijin nan ga daho kaza a dafe rigijff tasha kayan miyarta sharr. Ai wllh nake baki labari yakai gidan su amaryar nan bayan uwarta taci taji salam babu komi tace wannnan ai kunyi mantuwa babu komi a ciki na kayan hadi. Kinsan me yace ce musu yayi yanda sukaji kazar nan haka yaji yar su, to yanzu dan Allah me amfanin hakan? Wllh babban gata nake miki yar nan" Wani murmushin da baikai zuci ba meerah ta saki tana sunkuyar da kanta kasa. Acen kasar zuciyarta tana furta (Ni wllh da yamin daidai kuwa amma fa ni bama yarda zanyi wannan me kama da birin ya taba niba, bare ya hada jiki dani nevermine wllh) Fitowar Anne shine ya katse meerah daga duniyar tunanin data fada. Kallo daya Anne ta mata ta dauke kai tana karasawa inda hajiya umma ke zaune. Gaisawa sukai nan suka fada wata maganar daban ba wacce hajiya umman keta kokarin ganin ta kawota ba. Jakar kayan Anne ta turama meerah tana fadin taje tayi amfani dasu kafin ta shigo dakin itama. Hayaniyar data kaure a cikin gidan ne ya sanya su umma fita. Wata matashiyar mata ce wacce taci wani ubansun ado jikin farin leshin daya sha doguwar riga half bubu, sai farar siririyar yarinyar dake gefenta cin mutumci take zuwaba a cikin gidan tana fadin sai an nuna mata uwar data haifi amaryar da ake shirin likama dansu, dan son zuciya da bakar zalama anga gidan arziki shine za'a likema dansu... Kallo daya Anne ta watsama matar ta dauke

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54