Skip to content

Chapter 39

Chapter 39

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,190 words 0 views Progress saved
Download Book

koda yaushe damar shan iska muke basu!, shine babban kuskuren da mukeyi yallaabai a koda yaushe tazarar itace zarrarsu a garemu" "Uyummmmm na fahimceka kamaal baka sanshi bane shiyasa mutum ne shi me matukar hadari" Wani irin tirjiya yayi tare da yowa baya ya fuskanci yallabai din kafin kuma ya saki murmushin takaici ya furta. "Kace bansan waye shi ba? Shiba Aihuwarsa akay kamar sauran mutane ba? Aiba daga sama ya fado ba, ka sani kotu zata iya amince da maganarka, doka zata iya amincewa. Amma Allah bazai taba amimcewaba! Idan kana ganin yafi karfin hukuma to kasani Allah ne zai iya hukunta duk wani mugu dake mulkar bayinsa. A yayinda shirun Al'umma zai zamto tsawa hawayensu yayi ambaliya tamkar tekun maliya. Ko kuma tarin radadin dake bisne a cikin zuciyar kowanne bawa ya koma makamin da zai ceci rayuwaesu Allah ne kadai zai iya hukuntawa Allah daya" Ya fada a tsawace tare da bugar desk din yana barin dakin taron. Baki daya da kallo suka bishi officer Hassan Arwai ne ya dubi yallabai tare da fadin. "Zafin kansa yayi yawa! Jin kansa yake a matsayin da bai kawo ba, haka daukar kansa take a matsayin zarrarsa" "Stop!!! " Yalaabai ya fadi domin yanzu bai bukatar su sake hargitsa tunaninsa. "Pls every body get out" Ya sake fadi a tsawace tare da dafe kansa da hannuwansa. Kai tsaye gidansa ya nufa zuciyarsa na masa tsananin zafi da suya, Allah ne kawai ya kawo shi gida lafiya bawai don iyawarsa, dan yadda ya bama motar wuta kawai idan ka kalla ka tsoratama. Ganin wata siena fake a kofar gidan shine ya sanya shi tunanin su waye kuma domin shidai yasan baya da wanda zai kawo masa ziyara, tunda danginsa sun jefar dashi gudun kada susha wahalar dawainiyarsa, Allah ne kadai ya raya shi in banda haka da bai kawo wannan lokacin ba. Ruwa iska sanyi tsananin rana duk akansa suke karewa baya da matsugunni duk inda ya raba korarsa ake kamad kare koma yace annoba. Ijiyar zuciya ya sauke domin sammm bama ya bukayar ya ringa yawan tunano rayuwanshi na baya domin hakan tafarfasa zuciyarsa yake, kirjinsa kuma ya masa nauyin da yake gaza sarrafa kansa da fushinsa idan har beyi fashe². A nutse ya bude motarsa ya fito yana fitowa baban mariya na fitowa daga cikin gidan kamaal din, hannunsa dauke sa tray. Tsaiwa yayi ya fasa tunkarar gidan. Fuskansa da fara'a ya karaso har ganan kamaal din yana cewa. "Yan uwanka ne na rano da yan gwarzo suka zo wajen ka" ya fadi yana kama hannun kamal din. "Yan uwa dai baba?, ni kuma a ina nake da yan uwa ai bana da kowa....mebi mistake sukayi ne bara na karasa daga ciki" Ya fadi yana yin gaba. "Harda Malam Haruna rano shima baka san shiba?" Baban mariya ya jeho masa tambayar data sanya kamal tsayawa cakk da kafafunsa. Wata zubar bacin rai na karyo masa, wato sai yanzune ma suka dashi a jerin yan uwa, kenan raina masa hankali sukai tunda har suka san inda yake zaune kai tsaye. Cikin bacin rai yayi cikin gidan yana fito da yar karamar pistol din dake sakale a jikinsa, da karfin gaske ya tura kofar parlon wanda hakan ya sanya jama'ar dake zaune a parlon firgira. Ganin wani matashin bazaraten saurayi tsaye a gabansu me tsananin kamanni da Suraj din sune ya sanya jikin wasu fara rawa. Da sassarfa wani dattijo ya karaso inda yake tsaye da nufin tabashi, wani irin jaaaa baya yayi cikin fushi ua furta. "Me kuke nema?wannan yaron da kuka jefar kuka guda dan kimanin shekaru goma ko wa!?, to ku sani inma shi kuke nema wannan ya dade da mutuwa, wannan dake gaban ku ba kowa bane niba kowa bane face bawan Allah wanda ya raya shi bisa tafarkinsa na gaskiya da kuma bashi kariyarsa acikin duka lamuransa don haka I say get out in my house tun kafin ku fasata wannan bawan allah" Hawaye sosae suke suna rokonshi daya yafe musu sunsan sun aikata kuskure amma ya taimaka ya yafe musu, wani da suke kira da kawu ilu ne ya rarrafo gabansa cikin kuka ya shiga fadin. "Tabbas munyi kuskure!, munyi kuskure kamaludden amma ka yafe mana kowa a lokacin ya guji daukar kane sabo da gudun dawainiyarka, duba da tsananin azabar da talakan kasa yake sha. A namu banzan tunanin gani muke ba zamu iya ba kaidin zaka zame mana nauyin da bazamu iya dauka ba!, a jikin takarda naga hotonka ina gani na nemo shamsu nace ya karanta min. Kamal rano kadai daya ambata ya bani tabbacin kamal dinmu ne kamal din da kanina yamutu yabar min!, kamal din da talauci yasa na gaza daukarsa a matsayin......... Sai kuma wani irin kuka ya sarke shi janye kafarsa Jamal yayi da karfi tare da daka musu tsawa a karo na biyu yana fadin su fuce may a gida. Wani kyakykyawan bahagon mari baban mariya ya dauke fuskar kamal dashi. Cikin fushi ya furta " Idan har ba karya kamin ba da kace a matsayin mahaifi kake kallona to ban yarda ka kare furta ko wacce iriyar magana wa danginka ba inhar bame dadi bace! Kana ka basu masauki me kyau naji kuma wani abu ya biyo baya kaga yadda asalin fusata take. Fuuuuuuuu ya fice a parlon yabar kamal da hannu rike da fuska, sunkuyar da kanshi yayi domin hakan da baban mariya yayi na masa nuni da cewar tabbas beyi rashin mahaifi ba Wani irin girma da kuma darajar baban mariyane ya sake dabaibaye kamal. Domin a wannan zamani samun wanda zaiga kana aikata ba daidaiba ya tsawatar ma kanyi matukar wuya. Wani idan yaga kana aikata ba daidai memakon ya hana ka saima ya sake ingizaka da ingiza fushinka *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page 39&40 # ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # Hope # courage # Survival # Humanity # Inspiration 🤍🔥✅ _______________________ Suuuuuuu suuuuuuu suuuu haka Lafiyayyun baƙaƙe motocin ke sura uban speed saman shimfiɗeɗiyar kwaltar. Tun daga anguwar Victoria island har zuwa fitacciyar anguwar banan island duk inda suka gifta zakaga basu hanya ake, domin kuwa kallo ɗaya zaka ma motocin da irin uban speed ɗin da suke bayarwa ka gane bana lafiya bane. Cikin dan kankanin loƙaci sai gasu a gaban wani haɗaɗɗen plat house ,sannan kai tsaye suka fada danna hancinan motocinsu gidan wanda uban security'n suka wangale musu ƙaton get ɗin. dukka motocin suka shige ciki suka kuma samu wajena gurbin da aka tanada don ajjiye motoci suka faka. Kafin mutanen dake ciki sanye da baqaqen suit suka firfito suna bada tsaro wa na cikin motar. dukansu sanye cikin baƙaƙen kaya gaba ɗayansu manyan bindigune a hannayensu.Cikin da zafin nama ɗaya daga cikin security'n ya isa ga motar dake tsaye dukka qofofinta a kulle yayi knocking baqin glass din motar tare da ma arms magana, yar ƙaramar magana sukayi kafin ya bar wajen. sannan ya sake zagayawa right side na seat ɗin bayan motar ya buɗe qofar,yaja baya cikin girmamawa don bawa mamallakin motar fitowa. Saida yaja wasu ƴan sakanni kafin kyawawan sawayensa su fara fitowa, sai daukar idanu

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54