Chapter 8
Chapter 8
koda ɗagowa bane har Saida yaji an buɗe masa ƙofar motar, alamun sun iso keñan. Kai tsaye yana fita wajen sink ya nufa alwula ya ɗaura domin anata ƙiraye ƙirayen sallar magrib ne, hakan yasa suma sauran yaran nufar gaban tarin sink ɗin dake jere reras suka shiga ɗaura alwular suna take masa baya wurin bautama mahaliccinsu. Sune ne basu dawo gidan ba sai wajajen ƙarfe taran dare, a parlourn suka dakata suka fara shirya dining ɗin domin suna buƙatar suyi ɗinner. A nutsen sa ya shiga saƙƙowa zuwa loƙacin 9:35 ne, ahankali ya doshi kan dinning ɗin nasu yana baza wannan mayataccen ƙamshin nasa cikin shigar short trouser fari da kuma vest blue wadda takara haska farar fatarsa,yau kammm ko ƴar p-carp ɗin babu saman kan nasa, hakan shi ya bama lallausar baƙar sumarsa bayyanu wacce aka yima wani irin kwalliyar dada, gefe da gefen kuma an kitse shi sai tayi shilim a tsakiyar kan sa tare da sakkowa har ƙeyarsa, wani irin shining take yi na tsabar kyau da makudan kuɗaɗen da ake narka mata. zama yayi yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tare da buɗe wani kyakkyawan food plask lafiyayyan tuwon semo ne da jar miyan dage dage domin shine abu mafi sauƙi daga cikin jerin abinciccikan boss ln nasu, kuma dama best favorite food nasa kenàn, idan kana son ka birgisa to ka masa tuwon semo. Duk da baya a yanayi me daɗi hakan bai hana fuskarsa nuna jin daɗin saba. Barka da dare suka masa kafin axton ya matso ya fara saving nashi, tuwon semon ya zuba mishi , ya ɗora masa A gabansa tare da sanya masa spoon a ciki, karamin cup na glass yaja yana tsiyan ya masa win with alcoholic a ciki, A hankali ya fara feeding kansa, ya danci da dama kafin ya ture plate ɗin, wannan glass cup ɗin ya ɗauka tare da fara sipping nashi tamkar wani King. Tsammm ya miƙe yana komawa saman sopa tare da jan shisha ya shiga zuƙar ta yana fesar da hayaki. Suma Abincinsu suke ci hankali kwance, suna kammala cin farar shinkafa da jar miyar suka miƙe tare da zagaye boss ln nasu. tamkar wanda zasu hana zarar ransa idan loƙacinsa yayi. Wayar sa ya ɗauka kawai yawuce warsa bedroom, cikin tafiyar ƙasaita wadda sarauta tagama ratsa jinin jikinsa. Yau kam babu aikin babu aikin daya tsaya yi kai tsaye kwanciyar sa yayi bayan yayi adda'oin barcinsa kamar kullum. ♥️🤍🤎 *MEERAH* Kamar kullum gidan na nan kamar kasuwa, duk uban sallamar data rinka yi amma babu wanda yayi ƙoƙarin amsata, itafa har mamakin gidan su take yadda abubuwa suke tafiyar musu tamkar irin gidan jahilan nan, kanta kawai ta sanye xuwa barandar da mahaifiyarta take zaune tana aikin zuzzuba humra cikin kwalabe. Zaune takai dab da mahaifiyar nata tana faɗin "AMMANMU sannu da aiki!, ina raiha tayi ne naga ban ganta ba?" Dago kanta wacce ya kira da amman tayi tana cewa "yawwa meerah raiha na ɗan aike ta ne bayan layi, gidan jajiya kareemah zata kai mata humra" Nooding kanta kawai tare da cewa "Ina Affan naga ban ganshi ba..... Kafin ma ta rufe bakin saiga wani ɗan bakin yaro nan a guje irin ɗan shekara shida ɗin nan zuwa bakwai, a guje ya faɗa jikinta tare da faɗin "oyoyo aunty meerah na!" Rungume shi tayi tana sakin dariyar farin cikin nan ta buɗe bakinta kenan da niyar yin magana, gaji an wani janye shi a jikin ta. Cikin haki da masifar dake cin gabjejiyar matar dake tsaye ta rike hannun yaronta ƙammm, "meerah ki fita a harkan Affan fa, ko sai kin iskan tamin da?, duk yaran gidan nan da suke nan ga sunan kamar jamfa a Jos, amma duk babu wanda kika liƙema sai ɗana dalilin ki iskanta min ɗa ko?, to wllh bari malam ɗin ya dawo bazai yiwu ba dole ne yau na datse alaƙar dake tsakanin ki da Affan" Kanta dake mata ciwo ta riƙe domin dama komai take yi dauriya ne kawai sharrrrr wasu hawayen takaicin familynta ya saukar mata, _Wai sai yaushe kan family's nasu zai haɗu wuri guda?, sai yaushe zasu gane Allah da girma yake?, yaushe ne zasu san daɗin zumunci da ƴan uwan taka, gidan mu ya kasance wani irin gida ne me cike da son kai da son zuciya, kowannensu yana tafiya ne ya kife kansa kaɗai ya sani da rayuwar yaran sa. Gidan mu yafi karfin a ƙira shi da ko wanne irin suna, domin kafff iyaka bincike na na gaza samun sunan da yayi daidai da rayuwar gidan mu, kawai zan baku abin a dunƙule ne kowa yaje ya nemi fassara!. Mahaifin mu malam Abdullahi gwani yana da mata huɗu, duk wani haƙki na uba ɗa yana bamu saidai sammmm iyayenmu basa taɓa fashimtar hakan, kullum babban burinsu shine meda gidanmu filin yaƙin sunƙuru dana fili. Ga yawan tarin iyalan da Allah ya bashi, gamu da masifar dangin kamar tsaƙi amma sai ka kasance jajirtacce ɗan zamani zaka zauna da kowa lafiya a sannu a sannu muna tafiya, zaku fashimci halin kowa da kuma manufa na_ Wannan keñan Amma dake zaune tana ci gaba da zuzzuba humrarta cikin kwalabe idan ƙasa tana magana to kuwa tayi ita ma, haka Maman Saude ta karaci bala'inta tayi gaba ita da Affan dake ta kuka, yana miƙo min hannu, sai tallar ƙeyarsa take. Na yunƙura zan tashi keñan ƴar ƙaramar wayata irin tecno common ɗin nan tahau ruri cikin waƙar hamisu breaker me taken _Kada ki bari zuciya ta zuga ki_ saurin kallona Amma tayi tare da tsare Ni da manyan Idonta wanda duka muka gada daga gare ta, Cikin in ina nashi ga faɗin. "M.... MD ne, Ammah wai yana son za'a fira dani, kuma kinji wai dole sai dani za'a yi firarn, bayan duk ga su mardiyya nan su hayatu amman dole sai dani za'a yi wai" Kanta ta mayar taci ga *🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀} *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/DGIo9iiSjlgJPPqFHNtddH ____________________ *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 7&8 🤍🔥✅ Aikin ta ba tare da tace komai ba, haka yaci gaba da ƙiran Ni ban ɗaga ba kuma ban tafi ba. "Ki amsa shi, Idan kuma baki so ki bashi amsa ki dena ja masa rai har haka!" Ganin abinda nake son ta fashimta ɗin bata fashimta bane, ya sani faɗin. "Fuskata za'a haska a yayin firan Ammah!" Saurin ɗagowa tayi tare da dubana sai kuma tamin nuni dana shige ɗakin kawai, alamun bata son maganar. Handbag ɗina na ajje a kan doguwar kujerar dake parlourn mu, dake ciki da parlourn ne dakin namu, kayan jikina na rage ina faɗawa kan kujerar tare da kwanciya bayan nasha maganin ciwon kan. A take nannuyan barci yayi awon gaba dani, ban farka ba sai bayan sallar magrib, daƙyar nake Iya buɗe ido na sabo da nauyin da suka min, Adda'ar tashi daga barci nayi tare da tashi ina fita alwula na ɗauro na data salla ina zaune na haɗe kaina da gwuiwa na abin duniya duk sun gama sanyoni gaba raiha ta shiga ɗakin, zama tayi kusa dani tare da daura kanta saman ƙafafuna tace, "Yaaya kije Inji baffa yana ɗakin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54