Skip to content

Chapter 42

Chapter 42

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,192 words 0 views Progress saved
Download Book

shiga kutsa kanta cikin gidan dayafi kama dana barayine ma zatace kome, gadai yadda hantar cikinta take kadawa a zahiri amma kuma ta danne tsoronta haka ma a yanayinta baka isa fuskantar a wanne yanayi take a ciki ba. Kasancewar duhun magrib na dab da kawo karasowane ya sanya ta ringa bin jikin manyan flower's din coumpound na gidan. A haka har takai ga jikin katuwar railer din dake coumpound na wurin,Kamshin da bazata taba mancewa dashi bane taji sun kawoma kofofin hancinta ziyara. Kanta ta dago daga kokarin tafiyar da take shirin ci gaba dayi,Ido biyu sukai daidai Yana kammala wayar shi. Wani irin mugun tsoron kai tsayene yanzu kammm taji ya ziyarceta, Hannuwanta da suka shiga mazarine ya sanya ta dire Robar dake hannunta ahankali gudun kada ya subuce mata, wani shegen kallo ya jefeta dashi a kuma daidai ta sake dago kanta aikuwa yaja kyawawan fararen idonta masu kama dana mashaya a cikin nasa ta hanyar sarketa da nashi catizeen eyes dinsa. Yau kam ta gama tabbatarma kanta tata kuma ta kare tunda ta kawo kanta da kanta gidan wannan me satar mutanen. Muryarta na yankewan tsoro da mamakinsa cikin qaramin sautin ta furta "pah pa pls don Allah........ Wani shegen kallon daya jefa mata ne ya sanyata kimtse bakinta tayi shiru. Gashi kuma daf da juna suke sosai Kai tsaye hancinta babu Abinda yake shakar mata bayan mayen kamshinsa. Wani numfashi taja ahankali tareda dauke idanuwanta daga kallansa gabaki daya saboda tsoransa da taji yana nema Kamata. Jikinta ne ya fara mazari na tsatsanin tsoronsa ganin yana sake matsota, ja baya ta shiga yana sake binta yana ci gaba da jefa mata wannan dan iskan kallon nasa. Kankame jikinta tayi wuri guda tare da toshe kunnuwanta ta fasa wata uwar kururuwar data sanya duka mutanen dake cikin gidan yowa wurin a guje. Wani irin fusgarta yayi a fusace yana yin wata boyayyar hanya da ita. A daidai lokacin kuma harsu arms dake cikin gida sun kawo wurin, wulgawarsa kawai suka kalla ba tare da sun lura da Meerah ba. Suna kaiwa wani wuri ya danna wata na'ura me kamar botton kai tsaye sai gasu a cikin wani fitinannen hadadde tsararren cumputer room. Gaba daya shiga dakin na'ura ta dauki shelar shigowarsa dakin tare da ambatar cikakken sunan meerah kai tsaye. Hakan ne ya sanyata kwatar hannunta daga kyakykyawan rikon daya mata tana bude idonta da niyar mata masa wasu maganganu masu irin myankar zuciyar nan. Ai kuwa bata sauka idonta a ko ina ba sai kan grey 11/in/21 rose glasses out din da kai tsaye hoton mutum yake irin rarrabewa nan, idonta bai sauka akan ko ina ba saikan hotonta daya rarrabe kusa ashirin da wani abin. Sai nashi daya juya baya iyaka lafiyayyar farar fatar jikinsa kawai take iya gani!, Ai bata san sanda ta tafi da wani irin mugun gudu ta fada jikinsa ba tare da kankamesa tana sakin wata gigitacciyar karar daya sanya baki daya nu'urorin dakin daukar karar itama. Wani irin kulle idanunsa yayi tare da sakar mata wata razananniyar tsawar da kai tsaye ya idasa tafiya da numfashinta, domin dama tana dab da somewar na a lokacinma numfashinta ma seezing yake sai tsawar ta idasa tafiya dashi kai tsaye. "Ochhhhhh!" Ya furta yana ma rasa yadda zaiyi da ita saiya saketa daga tsayen da yake, muguwar buguwan da kanta yayi ne ya sanya numfashinta dawowa. Ahankali ta shiga kokarin wara idanuwanta, Dashi dake zaune kan wata kafurar luzury caution ta sake bude idonta. A take komau daya faru da ita yanzu ya sake dawo mata da rarrafe cikin muryan kuka ta isa gabansa. "Don Allah ka taimakeni! Na rantse batar hanya nayi ne Anne nace ta aikeni gidan gwaggonta" "Really?" Ya fada da alamar tambaya yana fiddo da wata yar karamar aba daga cikin aljihun dogon wandon dake jikinsa tare da fadin. "Kodai kin biyo wannan abar ba ohhh" Wani irin zaro idonta tayi tare da fara jijjaga kanta zara fara magana yayi saurin katseta cikin dakilalliyar muryan san nan na no nonsense ya furta. "Shiiiiiiii" Da alamar zeeping na bakinta sai kuma yace. "Ki sani gidan nan da kika samu damar shigowa duk a cikin target nawa ne, don hatta napep in da kika shigo duk cikin tarko nane domin ni kaina na'ura ne. Motocin na kaiwa inda nake na tabbatar da akwai wannan cctv footage nan" Ya karasa da jefa mata abarta yana mikewa tare sai kuma yadan juyo kadan yana sake fadin "Ohhhh Ashe bayan arhar da kike da harda jarum ma kin iya na jinjina miki dama nasan ko waye me ita dole yazo weldone ashe ba silly girl ce" Daga haka ya juya da nufin tafiya ta gudu ta biyo bayansa tana "Niban fadama kowa ba don allah ka fitar dani na Kar hankalin Anne na ya tashii bata san na fito ba da mij....... Wani wulakantaccen kallon daya watsa mata ne ya sanya ta shanye sauean maganarta. Cikin tafiyansa na kamar koda yaushe ya fice ai kuwa tayi wuff ra wawuri hannunsa ta kankame a kirji suka fito tare a dakin. Da wani kyakykyawan lafiyayyan mari ya sauki kyakykyawar fuskanta me kama da atafa don tsananin laushi da haskenta. Ba karamin gigitata marin yayi ba amma ta gwammaci ta juro ta shanye daya dai barta a wannan killed house ne ma ko die house zatace mane oho. Zuwa lokacin kuma har an fara shiga sallan magrib hannunsa ta samu ta yankama wani azabben cijon da saida ta fasa mar fatar hannu, amma kota kanta be biba saima wurin daya bari cikin sauri don masallacin da za'ashiga. Ai kuwa kamar yadda ta shigo yanzun ma tanan tayi nasarar fita kasancewar duk security'n sun riga da sun wuce masjid ne, amma duk da wani gudun bala'i tabar gidan tana faman sauke ijiyar zuciya, Kai tsaye ta sami napep ta fada tare da fada masa sunan anguwar data nufa dab da zata shiga suka hada ido ya mata wannan shegiyar alamar tashi, baki ta murguda masa da yimay alamar yanka wuya tana cewa me napeo din suje..... A lokacin da suka kawo anguwarsu har ana dab da fitowa a masallacin baffanta, da gudu ta fada zauren gidan saida da tsaya ta daidaita numfashinta kana ta shige cikin gidan. Sa'arta daya babu kowa domin duk rashin mutumcin mutan gidan basu wasa da sallarsu, da sauri sauri tayi alwular itama tana fadawa dakinsu a sukwane....... *By Ammey laylerh* *🦅 MIKIYA 🦅* *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page 41&42 # ROMANCE # BLACK MONEY # DEEP # Hope # courage # Survival # Humanity # Inspiration 🤍🔥✅ _______________________ Koda Anne ta idar da sallah tambaya daya ta mata shine "daga ina kike? Sai after magrib kike dawo bayan kuma tun sanyin la'asari kika fita?" Dake ita sammm bata iya karya ba inma tayi karyar nan take ake gane tane ya sanya soma inda indar fadar inda taje din. Uban tsawar da Anne ta daka mata ne ya sanya ta fadin. "Gi gidan su su di sha naje Anne" Ta fadi mafanar a rarrabe ga rawan da muryanta yake. Wani irin kallon baki da hankali annen ta cilla

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54