Chapter 13
Chapter 13
dai ta kasa hakan dan cikin ƙanƙanin loƙaci jikinta yay wani irin masifar nauyi nan ta silale jikin kujera idanunta na lumshewa. Daga haka bata sake sanin mike faruwa ba kuma. Baifi 10 minute da fitar motar ba baffan meerah ya shigo station ɗin, sosae hankalin sa yayi wani kalan masifar tashi, jin wai mahaifin meerah ɗin yazo yayi belin meerah ɗin. To waye mahaifin meerah kuma wanda ya wuce shi?, Kodai hankali ne kawai suke neman rena masa. Amma saiya danni zuciyarsa cikin tsanako da dattako irin nasa yabar station ɗin ya barma zuwa an jima kaɗan, wai a ganin sa kawai yau ɗin ma basa da ra'ayin barin sa ya ganta ne kawai shi yasa suka ɓullo masa da wannan zancen. ★★★ Wani kalar furzar da iska yayi yana maida kansa jikin saman sopa ya kwanta tare da lumshe idanunsa a hankali. Shi kaɗai yasan abinda yake ji game da taurin kan yarinyar data zaba buga game dashi. Ya fahimci lallai bata fahimci a ramin da take neman jefa ƙafarta bane. Amma zai bata loƙaci ta gama nata kalar ɗan ƙaramin wasan kafin ya fara buga babban game da sai tayi dana sanin sanin AK a rayuwarta da tayi. Idan ita ƙaramar ƴar iskar layi ce, zai tabbatar mata shi na duniya ne baki ɗaya, dan ba zubar da jini kawai ya iya ba harda cin uban duk wanda ya shiga sabgarsa. Lallai ta ɗaukarma kanta Dala ba gammo tunda tayi kuskuren zana fuskar sa, ya fahimci ita ɗin ƴar zafin kaice tun daga yanayin yadda ta mu'amulance shi a gidan jaridar su, amma ba komi tayi nata zafin kan ta gama duk zai sauƙe mata su kuwa nan bada jimawa ba. Ya jima a wajen zaune har su Axton suka dawo ɗauke da abincin da Vincent ya sasu suka yo order. Amma shi boss ɗin sai yace bazai ci ba. Ya haɗa coffee kawai da biscuits mai daɗi. yana shan coffee ɗinsa da biscuit tare da nazartar yarinyar. Koda ya kammala shan coffee ɗin bedroom ya wuce kai tsaye Maimakon kwanciya bathroom ya faɗa, ya haɗa ruwa mai ɗumi cikin bathtub tare da haɗa kayan ƙamshi kala-kala a ruwan sannan ya shiga ciki. Sai da ya kashi mituna a cikin ruwan na ratsashi da miƙar masa da kowace gaɓa sannan ya fito ya shiga wajen wanka ya ɗauraye jikinsa. Bayan ya fito salla ya fara gabatarwa tare da shafa'i da wutiri sannan ya shiga shiri. Yayi ƙyau sosai cikin shigar tasa tamkar ka sacesa ka gudu. Ga wani uban ƙamshi na tashi tamkar duka Company'n haɗa turaren ne a jikin sa. Sumar nan tasha gyara daka gansa kasan ya haɗa jini da masu jajayen kunnuwa. Hakama kwantaccen gashin sajensa sai walƙiya yake gashi kwance luf-luf ya sake fidda taswurar doguwar fuskarsa. Sai da ya tabbatar komai ya masa yanda yake buƙata sannan ya fito cikin nutsuwarsa da takunsa na tsayayyen namiji. National Hospital atarubus 3:45pm Accidents and Emergency aka shiga da wannan farin dattijon dake sananne ne shi babu wanda bai san waye Isa Manu ba, A kaff cikin Lagos harma da zagaye ta cikin ƙanƙanin loƙaci aka shiga bashi taimakon gaggawa. Ba ƙaramin tashin hankali su anne suka shiga ba ganin har bayan sallar isha'i babu baffa babu dalilin sa Raiha sai kuka take, baffa kuwa da kansa ya gama kullewa ne yasa jininsa naiman hawa nan take, bai sake tsorata da lamarin ba sai loƙacin ƴan sanda suka zo da batun mutumin da ya yi belin meerah ƴan fashi sun sun tare sa a hanyar sa ta mika Meerah ga iyayen ta a round about ɗin sa na shan kwanar anguwar su malam Abdullahi gwani. Cikin abinda bai wuce kiftar ido ba labaran suke zake hargitsa media, ƙura takai ƙura kam a wannan loƙacin, a kuma daidai loƙacin ne aka shiga musu da malam Abdullahi gida a yanayi mafi munin gani. Nan da nan matan baffa biyu suka shiga yaɓama Anne maganganu baƙaƙe. Wai akan yarinyar data gama gantalewarta a titi suke neman rasa malam, wllh baza su yarda ba. Anne kammm zuwa lokacin ma ita kam babu abinda take iya fuskanta daga cikin maganganun nasu, a fisge taji kalmar ƙarshe daga cikin ɗaya daga cikin matan. "Dama ai barewa ba zata yi gudu kuma ɗan ta ya rarrafa ba, wllh malam ka auro mana masifa da bala'i, gashi kuma masifar daka ɗaya ƴanta sune suke ƙoƙarin ajalinka, kaje garin kwashe kwashenka ka auro mace mara asali wanda ba'a san inda asalin ta take ba, wanda ya wuce ƴar gaba da fatiha me bakin duniya" Dipppp ji da ganinta suka ɗauke daga nan bata sake sanin ainihin abinda ke faruwa ba. ★★★ Sannu a hankali na shiga motsa idanuna da suka min matuƙar nauyi da ɗaurewa. Sai kuma na shiga buɗesu sannu-sannu harna gama buɗesu. hasken daya cika idanunane ya sanya na ɗan tashi a zabure da sauri. komi daya faru ya ringa dawo min daki daki har zuwa sleeping pawdern da suka shaƙa min. Ƙirjina ne yay wata irin masifar bugawa da sauri na ambaci sunan Allah. Cikin sauri na mike na nufi ƙofar bathroom ɗin da nayi amfani dashi wajen uzurina. Alwala na ɗauro sauri² gudu² na fito praymad ɗin da nayi sallah akai jiya yauma na nufa, a nutse na fara sallar cike da nutsuwa.bayan na idar na sulale a wajen ina saki wani irin kuka mai tsuma rai da da zuciya. Na jima kwance a wajen ina kuka kamar numfashina zai rabu da gangar jikina. Nama rasa ina zan kai tunanin na. Handle ɗin dakin naji an taɓa tare da shigowa mutumin jiya da dare ne duk da cewar fuskarsa a rufe take amma tsab na gama gane shi, kasancewata mutum bai kaifin basira, plate ɗin dake ɗauke da soyayyar wainar kwai ya ajje min tare da ledar bread recipe ya juya abinsa da niyar tafiya. "Lallai hakan da kuka yi shi ne ya sake tabbatar min da cewar ku dukkanin ku lusaraine, kolaye ne tunda har kuka rasa abinda za kuyi sai kidnapping mace" nayi maganar tare da jan wani mugun tsaki. Duk da ya tsaya cak tun fara maganata bai juyo ba. Harna kammala maganar kuma bai tanka min ba ya buɗe ƙofar ya fice tare da sauri tare da kulleni ta baya. Ido kawai na zubama ƙofar wasu kalar hawayen bakin ciki na sake gangaro min da gudun tsiya. A yanzu ba wai kaina kawai nake tausayi ba su Annena baffana Raiha ɗina nake tausayi da halin da zasu shiga sune suke matuƙar tada min da hankali fiye da komai. Bai cika 20 minute da fita ba sai gashi ya sake dawowa farin handkerchief ɗin dake hannun sa ya jefa saman fuskana hakan yasa na fara ganin bibbiyu kafin kuma na tafi luuuuuu. Ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai bayan sallar zuhr, a wani bedroom ɗin na daban na sake tsintar kaina ba wanda aka fara kaini ba. Da kyar cikin mutuwar jiki na miƙa na nufi hanyar da tsammanina ya gama bani bathroom ne, ilai kuwa bathroom ɗin ne toothpaste da brush na farke su a ledartarsu, saida na fara wanke bakina kafin alwala sallar zuhr tayi tare da fara duk wasu addaoin da suka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54