Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,182 words 0 views Progress saved
Download Book

*NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 JAJIRTATTU WRITER'S ASS.... 💫~* Page23&24 # ROMANCE # BLACK MONEY # Treason # Strong love # Right # Women's travel # The Secret Society # Oppression # KIDNAPPER'S # Informants # DEEP # BEST LOVE 🤍🔥✅ ★★★★ Da Wani kallon ka shiga hankalinka Isa manu yabi salman dashi don ganin irin mayataccen kallon da yake bin meerah dashi, Kasan Keyarsa yadan shafo yana waskewa abinsa. Kallo daya tama mutanen dake tare da baffanta ta dauke kanta daga garesu tamkar bata gansu ba, duk da kuwa ta gane isa manu don ita ba mutum bace mai yawan mantuwaba. A mutumce cikin salon girmamawa isa manu da salman suka shiga gaida Anne da tambayar me jiki. "Jiki alhamdullih da sauki wllh" Anne ta amsa itama a mutumcen kamar dai yadda suka gaida tan, ta dayan gefen da kanta yake salman ya koma don bai gama morewa kallonta ba. "Baby ya saukin jikinki?" Ta tsinkayi muryarsa me kama da anyi bari an kwashe, ba tare data ko kalli inda yake ba taja idanunta ta kulle abinta domin haka kawai taji ta tsani mutumin farat daya. Shima daga haka ya kama kansa domin be kamata ya fara bata aikinsu tun daga yanxun ba. Sallama sukama su baffa bayan sun ajje katuwar ledar da suka shigo da ita, duk da baffa beso hakan ba amma be ya kyalesu kawai. Kwananta daya da wuni daya amma daga gidansu meerah babu wanda ya leko da sunan dubiya bare taya Anne murnan bayyanar da tayi. Hajiyar salman ma tazo dubiyar haka manyan yan siyasa suka dinga zarya a cikin hospital din domin nuna karamcinsu da girmamawa wa Isa manu. Karfe biyun rana aka basu sallama lokacin baffa baya hospital din yaje gida, suna fitowa harabar hospital din wata rantsatstsiyar black Toyota Camry 2024 ta sha gabansu, duk tsaiwa sukayi a tare suna jiman moton ya wuce ya basu hanya su tari napep ya mikasu gida ga zafin rana da yake dakar ko wannensu. Kokarin kauce may suke ganin yaki basu hanya, sake shan gabansu yayi tare dayin qasa da glass din motar yana sakin murmushinsa me kama dana muna fukai tare da fitowa yana fadin. "Mama barka da rana Ku shigo nine fa" Yayi maganar yana kokarin bude musu Motan domin shiga, "0'oh ba ayi haka ba salman daga haduwa kuma sai dawainiya ai nauyin saiya ma yawa" Amma ta fada cikin hakikanin gaskiyarta, Saida yadan saki wani shegen murmushi kafin ya furta. " Haba mama dawainiyar miye zaiyi yawan matar dazan aura CE fa Insha Allah " Da sauri ta dago kanta tare da watsa mishi wani banzan kallo, domin ita sai yanxune ma ta tuna shi, tasha ganinsa a inda bai dace ba ta dalilin aikinta da irin aikinsu na jonalist (JARIDA) babu inda baya kai mutum. "Halan kai babu zuciya a kirjinka? Nifa a duniya na tsani mutum Mara fashimta OK" Kin dauke nasa idon yayi akanta duk kuwa yadda take jifansa da muggan kalamanta hadu da mummunan kallon da take jifansa dashi, amma shi hakan bai dameshi ba saima sake watsa nashin da yayi cikin natan, hannun Anne ta sake damka tana yin gaba abinta, da sauri yasha gabanta cikin maraitacciyar murya ya furta.....Pls mana babe don Allah Ku shiga" Tana kokarin sake Jan hannun Anne'nta ne taji annen taki biyo bayanta, ita kuwa annen ganin yadda hankulan mutanen dake compound din ne ya Sanyata tsaiwa chakkk. Da ido tama Merrah din alamar data kalli yadda hankula ya fara yowa garesu, kamar ance kalli side din dake damanki idanunta suka shige cikin nasa kyawawan idon, yana tsaye jikin wata mahaukaciyar baka wulik din Ralls rayce car yayi crossing kafafunsa yana buga games da tsadaddar waya abinsa hankali kwance cikin nutsuwa. Wani irin matse hannun Anne tayi tare da dan mutstsikar idonta kadan waiko gizo ya mata, still dai shi din ne tsaye cikin shigar riga da wando na long sleeves sawayensa sanye cikin wasu hadaddun snickers shoe sai idonsa daya to she su da wani mahaukacin luxary shade. Amma hakan bai hanata gane shi din bane *AK* ta furta. (Me wannan abin yake anan?) Ta fada acen kasar zuciyarta. "Didi wai kodai kin hadu da cutar kurumta ne?" Anne data riga ta zauna a cikin motar ta jeho mata tambayar, da sauri ta dauke kanta a kanshi tare da kokarin sanya kanta cikin motar. *"Ashe kedin me arha CE haka ban sani ba tunda har zaki Iya shiga cikin ko wacce tarkacen shara right?"* Haka taji saukar wucewar kalamansa har cikin tsakar kanta dap da ya kawo kansa kamar zai wuce ne. Ahankali ta saki murmushin daya kara kawata kyawun fuskarta a karo na farko tana tsayawa chark. Sai kuma ta dan tabe bakinta tare ta sakin wani murmushin takaici kafin cikin maganarta ta kai tsaye ba tare da jin shakku ko tsoron komai ba, Idonta cikin nashi ta shiga furta. ”Ai abu me tsadane yake birge kowa koda kuwa mutum yasan bazai same shiba yakan Iya tsayawa yayi tayi duk da yasan zaren ba kalan yadin bane, amma zeso ya dandali arziki yakuma bar arziki a inda arziki yake SBD farinjini halittane metarin baiwa wadda duk tsadar Abu seyanada farinjini yake birge kowanne halitta, just if u been a black stomach man ok tell me now but u are very amazing me for ur talked” Tunda ta fara motsa lips nata ya zuba mata kyawawan idonsa, kafin ya saki wani shegen murmushin nan nashi da mutane kema lakabi da na mugunta. A fusace ta shige cikin motar da Sam bata da ra'ayin Shiga 5 minutes da suka shude, harta shiga kuma ta juyo again. ”Remember kasani ayau zaka kara tabbatarwa mutum crismatic ako' Ina nadabanne kuma yanada wuyar samuwa” da karfin masifa ta buga murfin motor'n. Wanda hakan ya sanya salman kwasarta a guje suna barin kurarsu. ★★★ Har bakin kofar gida salman ya kawo su Meerah,bakin baffa na zaune cikin barantar dake kofar gidanshi suna zaune da mutanen da suke karatu duk bayan sallar asuba da kuma isha'i, dake yau kuma ranar alhamis ce karshen sati duk alhamis din duniya sau uku suke daukar karatu. Da farko be kawo su annen bane saida yaga fitowar Annen kafin merrah ta biyo baya. Da dan hanzarinsa ya nufo su har wasu daga cikin mutanen na Mara mishi baya. Shi da kansa ya dauki yan kayayyakinsu da basu da yawa bayan ya dada musu sannu, sallama sàlman ya musu yana cewa da baffa sent xuwa dare Insha Allah, sosae baffa ya dade masa godiya yana fadin. ”Allah ya kaimu min gode sosae” Cikin gidan suka shige shi kuma bayan sun gaisa da jama'ar dake tare da Baffan, shi kuma salman ya dauki hanya yana barin cikin anguwar baki daya. ”Assalamu Alaikum!” Anne da meerah suka hada baki wajen ma jama'ar dake zaune gaban bishiyar setline suna shan iska, amma tari babu Wanda yayi tsakanin matan gidan da kuma tarin yaransu. Saima hayaniyarsu da sukaci gaba dayi suda yaransu wanda ba'a raba gidanmu dashi. Da gudu Affan daya fito daga toilet yayo wurinmu cikin murna sosae yana fadin. ”Oyoyo aunty meerah dinmu ta dawo bayan mamanmu tace bazata sake dawowa ba wai” Wani irin fisgar hannun affan maman

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54