Skip to content

Chapter 23

Chapter 23

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
Download Book

Saude tayi cikin fushi ta shiga sirfa masa masifa. "Ance ba zata dawo ba din dan ubanka, affan zanci ubanka a gidan nan wllh shege marar zuciya ban hanaka kula wannan yadin magen ba @ gidan nan” Kuka yake yana ta kokarin kwatar kanshi daga mahaifiyarsa, wata uwar tsawa ta daka mishi tana jan hannunsa kiiiiiii suka shige daki. Ahankali ta dauke kwallar da suka tarum mata, tana jin wani Abu da batasan ko miye shiba yana tokare kirjinta, tana bakin cikin irin wadan nan abubuwan da suke faruwa a rayuwar gidansu. Daki suka shige duk kuwa yadda take jin kukan affan yana ta kuka yana fadin wllh saiya rataye kansa, tanajin sanda maman saude tana fadin ya rataye mana idan bashi da hankali. Da haka suka shige dakinsu kwanciya tayi ita kuma Anne zama tayi don ta huta. ***Bayan an shiga sallar la'asar affan dake labe yana ta faman sauke ajiyar zuciya, satab satab ya leko saida ya tabbar babu kowa a tsakar gidan kana ya fito tsakar gidan. Gyalen mamansa dake rataye a kan window ya dauka da gudu yabar dakin yana yin gaban bishiyar setline din tsakar gidan. Gyalen ya cilla ya hada ya masa daurin azar gagi, turmi ya taka ya zira kansa cikin daurin azargagen da yayi tare da shure turmin da kafarsa. Ji kake zug kansa ya zuge. Bacci tasha sosae Wanda har batasan iyakar shi ba, ihun maman saude shine ya farka da ita sama sama take jin ihun tana fadin. ”Jama'a Ku temake ni affan ya rataye kansa, Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un! Wayyo affan, wayyo jama'a, yanxu dama Ashe da gaske kake rataye kan naka zakayi affan?” Da wani mugun gudun bala'i na fito har inacin tun tube, kaff matan gidanmu suna tsaitsaye an rasa Wanda zai sinto affan. Hakan yasa na janwo drow din da muke tara ruwa na taka zan sinto shi. Drow din da nake kai naji an ture da karfin masifa, ji kake *tummm* na fado daga kan drow din. ”Shegiya mayya wllh kema saikin mutu tunda kece sanadiyyar kashe min da” Sune kalamai na karshe da kunnawana suka jiyo min na tafi duniyar somewa......kan kace meee gidan harya cika da mutane ko nace samarin gidan, jikin baffa kuwa rawa kawai yake don kowa a gidan ya shaida irin girman shakuwar dake tsakanin baffa da kuma affan din, Yaya Ibrahim ne ya sinto affan kan yay jale alamar a karye yake,wani irin kuka maman saude ta kece dashi ta fadi kasa tana mututuwa tana tunballo ta ratayo wuyan affan din tana kuka, Anne kuwa wani irin rumtse ido tayi tana jin wani irin dacin da bata San na miye ba na taso mata. ”Innalillah wa'inna ilaihir raji'un²” Ta fada tana jin wani zafaffen hawaye na karyo mata. Yaya Auwal ne shida Sapwan sukayi saurin Ciro affan daga jikin maman suna fita dashi don kaishi hospital. ”Ibrahim miye haka kuma zakuy? Kulli nafsin za'ikatul mauti! Dukkan mai rai mamacine saida muce ubangiji ya jikan Nasiru (Affan) ya kuma Sa mace tane” Cewar baffa da baki daya jikinsa yayi sanyi, su kansu manyan hawaye zubar musu yake domin affan irin yaran nan ne masu azabar shiga rai, dadi da kari akwai shi da nutsuwa,hankali, biyayya Sam shi babu ruwansa da yadda tsarin gidan nasu yake duk da kasan cewar yaro me dan bazai zarce irin shekara biyar din nan ba xuwa shida. Kan kace me makwafta sun cika gida harma da sauran yayan gidan aurarru duk sun iso, duk wannan fadi tashin da ake babu wanda ya sake bi takan meerah. Tana cen palon baffa da yasa Ibrahim ya maida ta cennnñ, bayan yayyafin ruwa da yasa aka mata ta farka amma alhamdulillah kuma ta sami bacci. Cikin kankanin aka suturta gawar affan aka meka shi xuwa gidansa na gaskiya. Sisae ya sami jama'a kasan cewar Sa yaro na kowa, har a manyan masallatu da gidan radio aka sheda rasuwar. Sai bayan sallar isha'i wajajen goman dare kana malan Abdullahi ya shigo, har xuwa lokacin kuwa meerah na palon Baffan, da kansa ya tada ta ruwan tea din da aka kawo masa ya hada mata da kansa, tare da bread saida ta wanko bakinta da fuskarta kana ta zauna tana tonkoshe kafafunta a gaban baffan. Haka badan taso ba ta shiga tura ruwan zafin zuwa cikinta amma sammm taki cin bread din, xuwa lokacin idanunta sun fada sosae sunyi zuru² duk da cewar dama tana a halin jinya be. Maman Auwal CE ta shigo dakin da sallama kasan cewar itane da girki yau, wani mugun kallo ta wullawa meerah a fakaice tare da Jan kwafa. Ita kuwa a tsanake ta mike tana ma maman Auwal sannu, ciki² ta amsa ta ita kuwa ta kwashi tarkacen tana yin woje bayan ta sake baffanta gaisuwa a karo na biyu. ★★★ *Armstrong* Gurfane yake gaban manyan police din dake kewaye da dakin, jikinsa duk jini ya jigata iyaka jigatuwa. Wata uwar tsawa dpo ya kwatsa mushi yana furta. "Tell me know zaka fada mana inda sauran suke ko sai yanke ma yatsun hannuwa?” Dago kansa yayi Wanda yake sharkaf da zufa, kafin a galabaice ya dago ya dubesu tare da sakin murmushin daya kusan haukata zukatan police din. “Wai kuna son na baku batu akan Boss ne¿” Ya fada tare dabin su da jajayen idonsa, da badan boss yaki bashi dama ba da tuni ba wannan batun ake ba wani ake. ”who is ur boss master' who is he?” Dcp ya fada cikin zafi yana cakumo wuyar rigar Armstrong. *”AK”* Ya furta cikin wani jahilin sautin daya sanya dcp sakinsa yana yin baya a mugun tsorace, jikinsa na wani irin mazari dpo kuwa wani irin yanka yaji zuciyarsa tayi. A kuma daidai lokacin manyan soldiers suka danno Kansu cikin babban dakin horaswas. A zafafe Ajmaal ya wani irin cakumi wuyar rigar Armstrong hada shi yayi da jikin gini yana furta. ”INA YAKE?” Hhhhhhhhhhhhhh sautin dariyar Armstrong ya karade dakin kafin cikin wani sauti ya shiga furta. ”Ganinsa kawai kansa kafafu su dau mazari, zuciya ta fara bugawa tamkar kazar da tagaji ta kwanta a cikin mai sai gata a kafe. Kunsan waye AK kuwa? _Shine mugun da yake lalata mugyayen kasa!!!, shine me tsince kazantar cikin al'umma! Kuma shedanin shedanun cikin al'umma, a shirye nake da in bada rayuwata ga *AK* wanda nake kallonsa a matsayin uwa uba Yar uwa Dan uwa” Dogo kansa yayi tare da bin Ajmaal da wani dan iskan kallo hannunsa yakai gefen bakinsa dake disar jini ya goge, duk kuwa da cewar hannunsa na cikin handcuffs ne. Cikin dangerous voice nashi ya furta. ”kodan sabo da mutuwa ta tai ma'ana shekeni!!!, zoka harbeni. Ko zaka rage radadin dake sukar zuciyarka domin shi kasan *BA YA MUTUWA*” Wani irin damkar wuyar rigar Armstrong Ajmaal yayi tare da bashi wani mugun naushi a gefen fuskarsa, saida ya dan dakata kafin still ya sake damkar wuyar rigar nashi yana sake furta. ”Idan har baka fada min inda yake ba na rantse sena sheke ka kafin nabi ta kansa shima na karkkarya kasusuwansa a gaban idonka” Wani shegen dariyar bazatane ya kwacema Armstrong. ”AK is too hard for me to break, diamond ne shi kafin a narka shi sai an yi amfani

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54