Skip to content

Chapter 16

Chapter 16

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,191 words 0 views Progress saved
Download Book

wani irin girgiza tare da fesar da ruwan dake jikinsa, Ahankali yabar wurin yana nufar compound din gidan. Duk inda ya wulga sai kaga wadan nan samudawan dai suna risina masa tare da gai da shi. ★★★ "Will you shut that your dirty mouth up!, are you stupid Ina magana kana yimin zancen banza da wofi, kodai ka samu tabin hankaline ban sani ko ban sami labari Impossible wannan bamai yiyuwa bane".. Yadda ya hayayyako yana masifar kadai zai sheada maka koma miye aka fada masa a cikin wayar bame dadi bane. " Me gida ka yarda dani na rantse da uban daya haifi ubana Salman baya cikin airport din nan, kasan bazan maka yawa ba fa me gida" Sosae jikin Isa Manu ya dauki wani irin Mazarin bala'i Wanda safiyar yau ne aka sallameshi daga hospital, ta karfin tsiya bawai don ya gama samun sauki ba. "Kai lele karka sa jinina ya tafasa fa, in banda zancen banza taya za'ace an rasa dan mutum sukutum tum a airport. Hauka ma kenan yanfa kaga last call nawa da salman din du du du bai wuce 40 minutes ba" "Na rantse da assamadu me gida bincike iya bincike nayi amma fa maganar gaskiya salman sammm baya cikin airport din nan..... "Stop your dirty mouth Lel... Chak ya tsaya ba tare daya kai ƙarshen Eee ɗin ba sakamon rumgumeshin da yaji anyi ta baya, kafin ya tsinci murya ɗa mafi ƙololuwar soyuwa a gareshi yana furta. " Nayi Surprise Daddy" Wani irin guntun numfashi Isa Manu ya fesar tare da juyo da Salman zuwa gabansa, sai kuma yaɗan shiga bubbuga gadon bayansa tare da furta. "Daddy's boy kafa tsoratar dani sosai irin sosae ɗin nan fa nake nufi" "So sorry daddy" Salman ya furta tare irin kama gefin kunnen sa guda. Wani ƙayataccen murmushi Isa Manu ya saki tare da nufar stairs da yaron nashi Yana faɗin "kai dai muje sama akwai abubuwan yi da yawa a gabanmu" nan suka nufi saman abinda. Har ɓangaren sa ya kaishi saida ya tabbatar Salman ɗin ya shige bethroom kana yabar ɗakin yana furta. "Karka ɗauki dogon laƙaci daddy's boy ka sameni cikin office ɗin cikin gida just 40 minutes kawai na baka" Ficewa yayi a sashen ta wata ɓarauniyar hanya. 45 minutes ago Sai gashi ya fito sanye cikin ƙananun kaya na shan iska, office ɗin daddy'nsa dake cikin gidan ya nufa direct. Yana tafe yana latsa faskekiyar wayar dake rike a hannunsa. Kai tsaye ya tura office ɗin mahaifin nashi ba tare dako neman izini ba, da sauri Isa Manu daya lula wata duniyar ta daban ya ɗago kansa tare da duban her yaron nashi abin alfaharinsa, ganin yadda daddy'n ke kallon sane ya sanya shi ƙarasowa cikin office ɗin yana zama kan kujerar dake facing da mahaifin nashi. Wasu files ya janyo tare da turasu zuwa gaban Salman. Files ɗin ya shiga dubuwa sosae kafin ya ɗago kansa yana dubar mahaifin nasa tare da ɗan fada fuska yana wani irin yamutsata. "Daddy?" Ya faɗa cikin wata kasalalliyar muryan dake nuni da taɓarar nan irin ta ƴaƴan hutu. "Yes daddy's boy duka abin da kagani a jikin files ɗin haka nake son komi ya tafi a yadda na tsara" "Amma daddy meye amfanin haɗa alaƙana da ita yarinyar da ka sako batun neman neman aurenta?" Wani dogon numfashi Isa Manu yaja tare da tattaro hankalin sa baki ɗaya zuwa ga Salman ɗin. "Ita kuwa take da amfani daddy's boy, idan har hasashena ya bani daidai yarinyar tana da wani ɓoyayyan abu kodai tana akwai abinda ta riga ta sani kame da wani abu!" Ya sauƙe numfashi kafin yaci gaba da faɗin. "Tunda har akayi kidnapping nata Ni meyasa basu haɗa dani ba, neman aurenta da zaka shiga shine zai janyo hankalin koma waye zuwa gare mu. Kuma yarinyar zata kasance a ƙarƙashin ikon mune hakan shine first kafin mu tafi plan B" "Amma daddy.... "Amma me? Daddy's boy" Isa manu'n yay saurin tarar numfashin Salman ɗin. Hakan ya sanya shi yin shiru ba tare daya sake yunkurin furta ko wacce kalma ba. "Hakan shine best solutions namu boy kana a tada hankulan jama'a. Ka sanya su Bom fire su tada zanga-zanga game da kwamushen su governor da kuma minister da Akayi ta haka ne kaɗai zamu cimma burin mu. Ya zaman mun jefi tsuntsu ɗaya da dutse biyu kenan Ni dasu Boshosho zamuji da sauran". "Wow Wow hoooooo wuuuu woohoo hooo good idea daddy ina alfahari dakai.... Salman ya fadi yana ihu tamkar wani ɗan daba. Mu haɗe a next fage my gold fan's...... ~ BY AMMEY LAYLERH ✍️~ *🦅 MIKIYA 🦅* _Mai hangen nesa 👀_ *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 17&18 🤍🔥✅ ★★★ #ANNEH POV Kwananta biyu aka sallamota bawai don ta gama warware wa ba saidan sallamar data naima da kanta. Tunda ta dawo cikin matan gidan babu wanda ya ko leƙo inda take, duk da kuwa cewar suna sane Amma baƙin hali da sama Rai wahala ya sanya babu wanda ya kalli inda take. Ita kuwa samm ba su bane a gabanta ɓatan ƴar tane kawai damuwanta, duk irin uban fari da jikin da take da a cikin kwanaki uku babu shi ga duhun da farar fatarta da sirka. Kasancewar jikinta da suffarsu irin na cikakkun larabawan nan ne wani irin kyau da haiba Anne ke dashi. Wannan shine kyau nata da yanayin kyawun jikinta shi yafi komai ƙona zuciyarsu abokan zaman nata. Tana zaune saman darduma tayi irin kifa kan nan na rashin samun nutsuwar zuciya. Yanzu a wanne hali *DIDI* take dama haka rashin ɗa a kusa dakai yake?, Dama haka ko wacce uwa take ji idan tana a irin halin da take?. Toma wai miya haɗa *DIDI'ƊINTA* ta wannan AK ɗin? Ak is a known criminal in Lagos, ta gagari kowa he is a kidnapper as well as an arm robber. "Ya ALLAH ya ARRAHAMANU ka kare min *DIDI* aduk inda take ka bayyana min ita cikin amincinka ya zul'Arshim majeed" Wani irin suya zuciyarta take mata yau inama ace tana da Asali? Inama ace tana wata ko wani ɗan uwan, yau inama ace tana da mahaifiyar da babu abinda zai hana ta rungume ta tayi kuka, tayi kuka iyaka kuka tayi kuka me sunan kuka ko zuciyarta ta samu salama da nutsuwa. Cikin zubda hawaye ta furta _"SHIN WACECENI?"_ Kamar daga sama taji Muryar maman haidar tana furta. *"KEBA KOWA BACE face tsintacciya mara asali mara galihu ƴar tsintuwa wacce uwarta tayi cikin shegenta ta hullar a bola"* Wani irin rumtse idanunta tayi da ƙarfin bala'i tana jin yadda ƙirjinta ke sama da ƙasa. "YA RABB!" Ta faɗa tana wani irin fesar da iska ta cikin bakinta me zafi. Kamar daga sama taji ƙarar shigowar sako a wayar *DIDI'ƊINTA* Sake kulle idanuwan tayi kafin jikinta na rawa da janyo wayar data zame mata tamkar itane meerah'ɗinta. Hannunta har karkarwa yake wajen buɗe saƙon domin gani take a kowanne loƙaci kan iya turo saƙon bayyanar meerah'ɗinta ne ta cikin wayar. Sai dai kash!..... Saƙon ma bai hada hanya da kidnapper's ɗin ba, saƙo ne da akan turo mata duk shekarar duniya na

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54