Skip to content

Chapter 3

Chapter 3

Mikiya Book One Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
Download Book

and you are giving your feet to this militant boy, he is taking use dahar ya samu zarrar da zai riƙa mana dauki ɗai ɗai, ya zama dole a wannan karon mu kawo ƙarshensa" Yayi maganar ne tare da duban duka soldier's ɗin dake fuskantar sa, cikin dakakkiyar sautin sa ya kalli ɗaya daga cikin soldier's ɗin yana furta. ”Ajmaal har yanzu kana kan bakar ka na kama EAGLE?” "Yes sir." Wanda aka ƙira da Ajmaal ɗin ya faɗa tare da sara ma mr. President ɗin. Ɗaya daga cikin soldier's ɗin ne ya kuma miƙewa Saida yayi solid na mr. President ɗin kana cikin bauɗaɗɗar murya ya shiga magana kamar haka. ”Har yanxu ina mamaki sir.mutumin daya bamu horo sannan kuma ya kashe ƴan ta'addar da babu adadi!, me Ze sa ya zama ɗan ta'addar?” Wani kafirin murmushi mr president ɗin ya saki tare da tsare wannan soldier's ɗin da firgitattun idanunsa, cikin dakakken sauti ya furta. ”Har yanxu kana son eagle kenàn?" "Kwarai sir amma ba kamar yadda nake son ƙasata” Cikin tsare shi da ido mr. President ya furta ”Idan har kai ka samo shi zaka iya harbinsa?” Saida ya kuma solid na president ɗin kana cikin Amon murya furta "Kwarai sir zan iya!, amma idan na tabbatar bashi da laifi, nayi ma wannan alƙawarin sir.” Cike da jin zafin Ajmaal ya mike cikin fusata ya fuskanci wannan soldier's ɗin. "Jaheed kodai kana tare da AK ne, in banda haka ta ya kake tununin cewa Eagle bashi da laifi?” Shima wanda aka kira da jaheed ɗin ya juwo yana sake fuskantar Ajmaal ɗin, kafin cikin yaƙi ni yace. ”Idan baka son mutum zai iya siyar da borkono kuce ba zafi, haka zalika zai zai wuce ta cikin ruwa kuce ya tada kura, mutum kan gwada zafin wuta ne sau ɗaya a rayuwa, wannan sojan shi da kansa yake ta famar fafutukar shiga wutar, taya kuke tunanin mutum mai tsananin gaskiya da kuma sadaukar da rayuwarsa domin ƙasar da kuma aiki da zuciya kamar ABDULMALEEK KUWAIT AK zai iya zama ɗan ta'addar? kamar yadda kuke ƙiransa da shi, dole Akwai dalili ko nace dalilan da suka sa ya zare kansa daga cikinmu” Ba shi Ajmaal ɗin daya qA@@ maganar ba shi kansa mr. President ɗin yasha jinin jikinsa, wani irin shiru ƙatoton office ɗin ya ɗauka, kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyarsa, wani irin shiru ƙaton office ɗin ya ɗauka na kusan second 40.kafin Ajmaal ya magantu "ko tantatama bayana yi kana ɗaya daga cikin ƙashin bayansa" Ya buɗe baki da shirin sake yin magana keñan mr president ya Wani irin doka table a take komai da yake kai ya tarwatse komai yayi nashi wuri fuuuuu ya fice a office ɗin a fusace, ganin haka ya sa duka soldier's ɗin suma suka mimmiƙe suna barin office ɗin, wani irin kill smile Ajmaal ya saki loƙacin da yake dab da fita. *ISAH MANU EMPIRE🔥* Wani katafaren ƙerarre haɗaɗɗen luzary ne iyaka ganinka gini ne Irin na manyan ƙusoshin kasar,wanda suka ci suka sha kai harma suka tada kai, baki ɗaya ginin gidan ya kasance na glass da glasses ne. Duk kuwa irin girman da gidan yake da, amma kewaye yake da uban wasu jibga jigban soldier's. Kai tsaye katafaren parlourn gidan na kutsa kaina,da wani farin dattijo na fara cin karo wanda keta faman safa da marwa. Hannuwansa goye a gadon bayansa wanda a ƙalla zai iya kaiwa shekaru 80 ko irin da biyar ɗin wani irin sintiri yake famar yi, wanda kallo ɗaya zaka mashi ka kai tsaye ka gane cewar tabbas baya a cikin hayyacin sane, da ƙarfin masifa ya dunkule hannunsa tare da kaima iska naushi. "Why is everyone afraid of him? Wanene shi yaushe ma aka haife shi dahar zai sanya ni gudun tseran tsira" Yayi maganar Cikin zallar ɓacin rai da kuma jin ƙona daga cikin tsaƙiyar ƙirginsa. Da sauri ɗaya daga cikin samudawan mutanen dake zagaye a ɗakin suka haɗa baki wajen furta. "Ko wa ye izini kawai zaka bamu!, mu kawo maka kansa BOSS" Idanuwansa da suke rine sosea ya ɗago tare da zuba musu jajayen idanunsa da suka ƙanƙance. Numfashi ya fesar me zafi kamar bazai magana ba, sai kuma ya magantu, Cikin wani irin dakakken sauti ya furta. "EAGLE, MIKIYA Shi nake da buƙata!" A razane A ƙiɗime hankali tashe suka ja baya namomin jikinsa na rawa, suka shiga bin boss in nasu da kallon You are smart 😳😱👀 Hhhhhhhhhh to ai shikenan 😅🥰 A gimtse 🫰 🙃♥️✅ *BY AMMEY LAYLERH ✍️ ✅* *🦅 MIKIYA 🦅* {Mai hangen nesa 👀} *~We want an end to oppression💪~* https://chat.whatsapp.com/GiLzmY90dz17bRbw5yMYBg ____________________ *NA MARYAM NASEER* ~AMMEY LAYLERH ✍️~ ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* Page 3&4 🤍🔥✅ ★★★Sosai yasha barci mai lafiya a safiyar ta yau kasancewar a daren jiya ya jima bai kwanta ba. domin bayan ya dawo daga fitar daren da yayi sosea yayi aiki a cikin laptop nashi,wanda ya raba dare yana yi. Sallar asuba ma daƙyar ya fita masjid dake cikin anguwar yayo Ahankali ya soma buɗe lumsassun Idanunsa da har yanxu suke cike da barci, santala santalan fararen sawayensa ya fara zubowa kan tattausan carpet ɗin dake gabansa. A nutse kuma ya miƙe yana nufar haɗaɗɗen bathroom nashi, shower ya sakamar kansa sosai ruwan ya dake shi, kana ya tara ruwa masu ɗumi da daɗin ƙamshi a cikin bathtub,Wanda gefe da bathtub ɗin akwai drawers masu yawa da wata full sized jaccuzi da kuma site din wata striated rectangular glass shower tana wani fidda wani irin ƙyalli, kamar ba'a taɓa amfani da shi ba shima gefen sa da akwai fixtures masu ɗaukar hankali sosai. Yaja tsahon loƙaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe chocolate Colo mai azabar taushin tsiya dan har wani wani maski-maski take yi tsabar taushi da kuma laushinta,da mini towel ɗin dake a hannunsa ya shiga tsane jiƙaƙƙiyar tulin sumar dake kansa mai tsaho, Fuskar nan a tsuƙe Samm babu alamun rahama a cikinta. Gaban ƙaton mirror'nsa ya nufa cikin tafiyar jin kai da kuma isa. Hand dryer dake saman mirror ɗin sabuwa fil ya ɗauka ya jona a socket, ya shiga busar da himilin sumarsa da tafi kama data ƴan India, lotion ɗin dake jere saman mirror'n ya shiga shafa wa jikinsa sama sama. Saida ya mulke jikinsa da spray's nashi masu azabar ƙamshi da tsada, kafin ya nufi gaban wardrobe nashi data kusan cinye bango guda. Tsabbb yayi shirinsa cikin wasu haɗaɗɗaun track suit baƙaƙe, sai glass ɗin daya sakaye idanunsa a ciki tare da facemask ƴar gadon, phone's nashi kaɗai ya diba yana nufar main Parlour, cikin takun cikakkun mazan dake ji da kansu. Kafin ya fito tuni su milse sun gama shirya komai daya dace, jin takun tafiyarsa da baya taɓa ɓuyane ya sanya su risinar da kansu ƙasa, cikin girmamawa suka haɗe baki wajen furta "Good morning Boss!" Saida yaja wasu luƙuta kafin ya amsa "kuna lafiya" iyaka saman laɓbansa. "So boring Boss" Wannan karon kammm da ka kawai ya amsa su, yana zama kan ɗaya daga cikin ƙayatattun kujerun dake kewaye da dinin Area ɗin, A ƙasaitance yaja wata haɗaɗɗiyar kwalba wine Wanda naga ansa with alcohol, zubawa yayi a glass cup ya farasha, bai wani shada yawa ba,

Table of Contents

Chapters

54 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54