Skip to content

Chapter 8

Chapter 8

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

ke. Suka jera abinsu Mairo na ta addu'ar samun nutsuwa cikin zuciyarta sakamakon ganin cincirodon al'ummar kauyensu wadanda ake nufin ta yi karatu a gabansu. Tuni Malam Bedi ya isa wajen tun kamin su zo, yana cikin rumfar iyaye maza, a sahun gaba, yana ta ware ido don ganin ta inda Mairo zata bullo. Can ya hangota rike da hannun Innarta, ta samu wajen zaman da ya dace da Innar ta zaunar da ita, sannan ta karasa cikin 'yan group dinsu suka yi sansani. Taro ya yi taro, mai gabatarwa ya fara gabatarwa bayan bude taron da addu'a, daga limamin garin Gurin-Gawa. Maryam Bedi, ita ce wadda aka fara kira ta bude taron da karatun Alkur'ani cikin daddadar kira'arta kai ka ce diya ce ga Khusairi, inda ta karanto karshen suratul Fathi, wato ayar nan ta "Muhammadurrasulullah…...." Gaba dayan jama'ar dake wajen jikinsu ya yi sanyi, sai ga Malam Bedi yana kuka. Da ta dasa aya aka dauki kabbara kowa na cewa "Ai Mairon Hure ce, diyar Malam Bedi". Innar kuwa sai washe baki ta ke, bakinta ya ki rufuwa don kuwa duk matan da suka san ita ce babar Mairo, sai gaisawa suke da ita. Yayin da 'yan bakin-ciki, wato wadanda ke da 'ya'ya a makarantar ba a kuma kirawo 'ya'yansu ba sai zumbure-zumbure suke yi mata, ko a jikinta wai an tsikari kakkausa. Haka nan Mairo ce dalibar da aka fara kira ta amshi allonta daga hannun Mai girma shugaban karamar hukumar Kumbotso. Malaminsu ya karanto mata farkon suratul Bakara tana bi tiryan-tiryan cikin kira'ar da ta fi ta malamin. Bayan nan Mairo ta karbi kyautar dalibar da ta fi kowa iya Tajwidi, sannan daliba mafi da'a a gaba dayan daliban shekararsu. A sa'ilin da maigirma Chairman ya amshi lasifika domin gabatar da jawabinsa na babban bako mai jawabi. Budar bakinsa sai cewa ya yi "Na dauki nauyin karatun wannan yarinya MARYAM BEDI a makarantar sakandiren 'yammata ta gwamnatin tarayyah da ke Minjibir". Gabadaya aka sa kabbara. Abokan Malam Bedi suka shiga taya shi murna, ya rasa inda zai sa kansa don farin ciki. Mairo ta riga su komawa gida domin an ce su tsaya za su gana da Chairman. Inna Hure na shigowa ta suri Mairo ta goya a baya, ta sa zane ta daure ta, ta sa majanyi ta kara daurewa. Ta shiga zagaye dakin da ita, ita kuwa sai dariya ta ke. Kamin su zauna gabadayansu. Malam Bedi ya gabatar musu da bayanin da maigirma chairman ya yi masa na cewa, zai tallafawa karatun Mairo a babbar makaranta ta gwamnatin tarayya. Zai mika komai ta hannun shugaban makarantarsu ta boko tunda dama gab ta ke da zana jarrabawar fita firamare. Ya kare da cewa. "Amma fa makarantar ta kwana ce". Nan da nan farin cikin da ke makale a fuskar Inna Hure ya yaye, Mairo ta lura da hakan, ta ce "Haba Inna, wannan ba wani abu ba ne. Zan dinga zuwa hutu kuma ana zuwa ziyara. Kin san Lanto ma ta gidan Kado tana makarantar kwana a Kwa. Duk bayan watanni uku dawowa ta ke. Sannan bayan kowanne wata ana zuwa ziyara". Inna ta ce "To ni wa zai kai ni birni? Har in gano ki a kowanne wata?" Ta ce "Allah Shi zai kai ki, ga iyalin Baba Abbas za su iya raka ki". Nan da nan Hure ta yi kicin-kicin da fuska ta ce "Ke, raba ni da wadannan mutanen. Ni dai na yi hakuri har ki zo hutun". Mairo ta yi murmushi ta ce "Shi ke nan Inna". Malam dai jinsu yake a zuciyarshi yana mamakin dalilin Hure na kin son yin zumunci da iyalin dan uwansa. Bai sani ba ita a ra'ayinta shi ne, idan har zata ke shiga shirginsu wata rana za su sake yin yunkurin rabata da Maironta don taje tayi masu bauta amma ba don Allah ba. Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, su Mairo aka kammala zana common entrace, aka zauna gida zaman jiran sakamako. Ba jimawa ya fito, shugaban makarantarsu ya mikawa Chairman. Cikin sati uku sai ga takardar daukar Maryam Bedi, cikin sabbin daliban FGGC Minjibir na shekarar. A na so kuma ta isa makaranta cikin sati biyu, hedimasta ya kira Malam Bedi ya damka masa ya kuma gaya masa ya hadawa Mairo kayan abinci da ake hadawa dan makarantar kwana, ya kuma ba shi katifar Mairo da filo, domin makarantar ba sa bukatar akwatun karfe. Malam Bedi ya dawo gida shi da Hure aka hau shawarar abin da za a hadawa Mairo, Hure ta daka mata kuli-kuli ta kuma shanya mata Rama mai yawan gaske, da zata dinga jikawa idan ta yi sha'awa ta kwada ta ci, kwaki kwano biyar, kanzo kwano uku, yaji rabin kwano, omon wanki da sabulun wanka. Man shafawa da man kitso, man kuli da manja. Mairo ta ce, su sayo mata brush da maclean, aka siyo a Fanshekara. Shi ke nan kaya sun hadu sai tafiya. A daren Inna Hure ta kwaba lalle ta yaba mata a kafafunta aka daure aka kuma zura hannun dama cikin dumar lalle, shi ma kan safe ya yi jawur kamar jini, duk adon tafiya makaranta ne. Aka tsefe kai aka yi mata kitson doka guda takwas. Babanta da Hedimasta su za su kai ta Minjibir, don haka tun karfe bakwai hedimasta ya ke buga musu zaure da yake shi ma Chairman ya cika shi da abin arziki duk don ya kula da karatun Mairo. Mairo na kuka Innarta na yi, a haka suka rabu. Hedimasta dauke da katifar kwanan Mairo, malam Bedi rike da dindimemiyar (Ghana Must Go), a haka suka doshi tasha. Hedimasta na ce da Bedi daga wannan zuwan da zamu yi da kai, duk hutu kai kadai zaka dinga kawota, don haka ka dinga kula da duk abin da na yi". Malam Bedi ya ce "To, angode dai". Suka samu bayan motar rake suka dane, ta fito da su Fanshekara, daga nan suka hawo motar Bata/Kuroda. A nan suka hau motar Minjibir, Mairo a maleji su kuma a kujerun gaban motar. Tafiyar awanni biyu ta kawo su Minjibir, aka sauke su a tasha. Daga nan suka hau tasi aka kai su har kofar FGGC. Suka gaisa da maigadi, suka ba shi ajiyar kayan su suka karasa cikin makarantar. Jikin Mairo ya yi sanyi matuka ganin irin tsaleliyar makarantar da aka kawo ta. Ta daga ido tana hangen dalibai cikin kayan makaranta iri daya, cikin tsari da nutsuwa. Kowacce a nutsenta ta ke tsaf, tana tafe cikin kamala. Ba ka jin hayaniyar komi sai sautin malamai suna koyarwa cikin azuzuwa, shi ma din a tausashe. Mairo ta kalli kanta sama zuwa kasa, ta hango bambanci a farrake tsakaninta da irin jefi-jefin daliban da ta ke ganin suna wulgawa. Gabadaya sai ta ga kanta kamar wata almajira, duk da kuwa ta kure adaka, ta sha lalle. Ga jambaki jawur ta rambada ta yi kuma jagira da digo a tsakiyar goshinta. Duk da hakan ba ta ji ko dar na zama a wannan makarantar ta yi karatu ba. Ta yi tunanin cewa, ba wannan ne abinda ya kawota ba, darasin da za a koya mata ne, Yaya Habibu ya dawo ya yi alfahari da ita. Suka tambayi ofishin shugaba aka nuna

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66