Chapter 33
Chapter 33
Mairo ta ce "Duk ba wannan ba Ladidi. Ki tuba ga Allah, ki sani cewa, Yana kallonki, idan su Baffa ba sa kallonki. Yau idan Baffa ya samu labarin kin cire ciki har sau biyu a wane yanayi kike tunanin zai tsinci kansa? Idan ba kya tsoron Allah, ai kya ji wa kanki tsoron cututtukan zamanin nan da ba su da magani. Idan aure kike so ki fidda daya daga cikin manemanki ki aura mana?" Ladidi ta ce "Na tuba, na bi Allah na bi ki. Wallahi daga yau bazan sake ba..." "……Ki ma sake din mana don ubanki". Suka juya a razane, Habiba ce tsaye a kansu, ashe ta dade da shigowa ba su ankara da ita ba. Ta kwance dankwalinta ta yi damara, ta yo kan ladidi ta hau ruwan cikinta ta soma kirba mata naushi tana ihu tana "Na tuba Mama, wallahi bazan sake ba". Wannan bai ishi Habiba ba, sauka ta yi ta nufi kicin ta dauko tabarya ta yo kanta tana fadin, "Gara na kashe ki kafin kanjamau ta kashe ki, kibar mana abin fadi cikin zuri'armu". Ganin ta yo kanta da tabaryar Ladidi ta yo waje da gudu don tserar da rayuwarta, wannan ya janyo hankalin kafatanin jama'ar gidan yara da manya, suka fito tsakar gida har Dina da Habibu da Baffa. Ganin Ladidin zata yi waje da rigar bacci, kafarta ko takalmi babu, kanta ko dankwali, Habibu ma ya rufa da gudu ya kamota tana ta kuka, tana "Na tuba wallahi ba zan sake ba…….." Habiba ta fito tana sharar hawaye, ta ce, "Ni fa ince, wannan aman da wannan kwanciyar nakin na Ladidi, ba na lafiya ba ne, na zama shashashar Uwa, yanzu Mairo da kunnawana ba su jiye min ba, haka zaki biye mata ku binne mu?" Mairo na kukan tausayin Ladidi ba ta ce komai ba. Baffa ya ce "Mai Ladidin ta yi ne?" Ya tambaya yana kallon Mairo. Ta yi tsuru-tsuru ba ta yi magana ba. Ya sake tambayarta, ta ki magana. Habiba cikin kuka ta ce "Ciki suka je aka cire mata, wai wannan shi ne na biyu, na ji su tana yi wa Mairon godiyar ta rufa mata asiri". Baffa ya ce "Mairon? Da ita aka je aka cire cikin?" Mairo ta girgiza kai cikin kuka ta ce "Wallahi ba ni na rakata ba, ita kadai ta je abunta. Ni asibiti na kaita ta ga likita". Dariya ta kama Habibu, wai asibiti ta kaita, sai ka ce wata uwarta? Habibu ya ce "Ke ma sai mu je a duba ki, don abokin barawo ai barowo ne". Ya hankada Ladidi da ke hannunsa ya tankado keyar Mairon, ya ce, "Oya! Lets go, har gwajin kanjamau duk za a yi muku tunda kun zama karuwai". Mairo ta soma rantsuwar, wallahi babu ruwanta, ba ta da saurayi, ba ta taba yin zance da namiji ba. Babu wanda ba ta baiwa dariya a wajen ba. Baffa ya kamo hannunta ya ce "Share hawayenki Mairo. Babu inda za ki, kanwarshi ce karuwa ba ke ba". 8/1/21, 9:30 PM - Kawata: Mairo Little Mairo tana ta murnar ganin mamarta da ta kwana biyu ba ta gani ba. Shi kanshi Yaya Habibun idan ka lura zaka ga annurin fuskarshi ya karu sosai. Oh! Ashe haka auren so yake? Mairo ta ce a zuciyarta. Kai ka ce sun shekara ba su ga juna ba. A otel din da Amiru ya sauka (Best Western) suka ajiye shi, da alkawarin sai ya shigo da daddare yin dinner. Kuma Mairo yake so ta yi mishi girki. Dina ta yi murmushi ta ce "Ban fa gane ba, kada ka sa Harrit ta bindige min kanwa". Ya yi murmushi ya ce, "Allah babu wasa cikin maganata Aunty Dina, don ni yanzu kin zama Auntyna, alfarma nake nema ku yi min ke da mijinki, kokon bara na yana gidanku, duk da mijinki is not hundred percently agreed (bai yarda gabadaya ba) sabida wasu hujjojinshi marasa makama. Nasan ke za ki dube ni da idon rahma. Zan ba ku mamaki, zan nemi soyayyar Mairo ba campaign nake so ku yi min ba". Har suka iso gida, Dina na jinjina kalaman Amiru a zuciyarta. Ta sanshi, ta san halinshi kamar yadda tasan mijinta. Karya ko joking ba sa cikin halayyarsa, idan ya ce yes, to da gaske yana nufin yes din babu gudu babu ja da baya. Babu kuma abin da zai sa shi ya janye abin da ya sa gaba. Wani irin mutum ne mai nasara akan duk abin da ya sa gaba, wato dai irin mutanen nan ne masu ra'ayin kansu, ba masu fadin karya don wani ya ji dadi ba. Hakanan ba sa iya boye abin da ke zuciyarsu. Ta dade tana addu'ar zuwan ranar da Allah zai nuna mata mijin Mairo, ta sha kissima yaya mijin Mairo zai kasance? Domin ita din 'yar baiwa ce kamar Habibu. To amma ba ta taba tunanin Amiru ne zai ce yana so ba. Kololuwar ilmi, nasaba, arziki, kyau, nagarta duk shine. Bankin duniya yana hannunsu, kudin Najeriya gaba daya yana hannun ubansa, sai ya rattaba hannu a kansu za a yi amfani da su, ko 'yar shugaban kasa yake so zai aura. Duk kalar macen da yake so da gudu za a ba shi, amma ya ce; MAIRO, a ganinta wannan abin alfahari ne a gare su, ita da Habibu domin Amiru ba zai yi karya ba, ba zai yaudare su ba. Ba zai fadi abinda ba haka yake a zuciyar shi ba. To mai yasa Habib cogewa? Ta san abin da yake gudu ba zai wuce Harrit da 'yammatan Amirun ba, domin iyayenshi mutanen kwarai ne, 'yan jiya, bana yau ba, kuma Habibu kamar Da ne a wajen Abudrrahman Gaya. Da irin wanda ya tsugunna ya haifa. Shi ya dau nauyin karatunshi tun daga master har PhD da sauran kwasa-kwasan da ya halarta. Yasan kuma amintarsu da Amiru ba tun yau ba, don haka ta ke ganin ta wannan fannin ba za a samu matsala ba. Idan ma akwai matsalar ta fannin Harrit ai shi Amirun ba yaro ba ne, yasan yadda zai tsarawa kanshi rayuwa. Suna kicin ita da Mairo lokacin da Amiru ya iso. Dina ba ta ce mata komai ba, sai ta yi ma kamar ba tasan zancen ba. Shi da Raymond ne sakatarenshi, suna hira kan harkokinsu shi da Habibu, amma duk hirar ta gundire shi, sai baza ido yake don ganin ta inda Mairo zata bullo, amma shiru. Habibun na hankalce da shi, yau surukuta sosai yake nunawa, duk sai dariya ta kama Habibu, sabida wani ‘respect’ na musamman da ya lura Amirun na bashi. Ya yi fes cikin ta-zarce, na farar shadda excellencior duk da kullum cikin kwalisarshi ya ke amma Habibun bai taba ganin ya yi mishi kyau irin yau ba, to ina ga 'yammata? Wadanda ke jin kamar su ja shi ta karfi, to amma fa banda kanwar Habibu 'Mairo', wadda kallon fuskarshi ma ba zata iya yi ba idan ba dole ba. Hakurinshi ya kare, tare da duban agogon hannunshi. Shi dai kawai so yake ya ganta, ko hankalinshi ya kwanta, amma Habibu ya share shi kamar bai san halin da yake ciki ba. Cikin ikon Allah sai ga Dina ta fito
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66