Chapter 4
Chapter 4
kan 'yar autarsu “MAIRO”, wadda ba su samu ba sai bayan shekaru sha takwas da haihuwar Habibu. Don haka idan ya zo a tura mai kujera ya zauna, ana lale da shi, idan bai zo ba ma falillahil hamdu. Inna Hure ce duke tana faman firfita wutar iccenta, domin ta samu ta kammala abincin rana kamin Malam Bedi ya dawo daga gona. Idanunta sun yi jawur sai zuba suke, ga dukkan alamu irin azababben itacen nan ne Allah Ya hadata da shi. A gefe 'yar lelen ce zaune bisa tabarma tana dandasawa 'yar bebin karanta kwalliyar juma'a da wani tsalelen yankin yadin mamar-mamar da ta tsinto a shagon tela. Ta daga 'yar bebin tana cillawa tana cafewa tana wakarta cikin nishadi, ga dukkan alamu babu yarinyar da ke cikin farin ciki a gidansu a gaba dayan kauyen Gurin Gawa kamarta, sabida daurin gindin sangarta da cikakken gata da ta ke samu daga Innarta. "Ke kam 'yar gata ce, Ta-Ummule. Ni uwarki “MAIRO” na tsaya miki. A taba ki a tabo bala'i, A duke ki, in rama miki. Innata ta tsaya min, Ni kuma na tsaya miki........" Sallamar Habibu ce ta katse ta daga wakar da ta ke rerawa 'yar bebinta, cikin zazzakar muryarta kamar gyare. Ta yi cilli da Ta-ummulen ta kwasa da gudu ta makalkale shi, tana cewa, "Yaya Habibu oyoyo!" Ya ce "Ke da Allah kazamar banza, cika ni, dubi bakinki damale-damale da busasshen koko, hanci duk busasshiyar majina, sannan kalli hannunki duk bakin tukunya, kin zo kin goge su duka a jikina. Wallahi duk sanda na doso garin nan cikin fargabar cakumon da zaki yi min da kazantarki nake, shashashar banza an girma ba a san an girma ba". Ya rabata da jikinsa ta karfi, ita ko ko a jikinta, dariya ma ta ke abinta kamar ba da ita yake ba. Inna Hure ta cika fam, kiris ta ke jira ta sauke mishi kwandon bala'in da ke cike taf a bakinta, sabida wannan tijara da yake yiwa autarta. A ganinta Habibu ya tsani Mairo ne kawai, don shi yana birni, ita tana kauye, duk da matsananciyar kaunar da Mairon ke masa. Babu ranar Allah da zata fito ta fadi, Mairo ba ta ambaci sunan Yaya Habibu ba. Shi kuma da zarar ya zo irin tarbar da yake yi mata ke nan, ita kuwa kamar dada tunzura ta yake ta yi masa oyoyon, da dukkan zuciyarta. Ya matsa gaban Innar ya kai gwiwoyinsa kasa, ya ce "Inna barkanku da gida, mun wuni lafiya?" Ba ta juyo daga fifita wutarta ba, haka ba ta kalle shi ba, ta ce "Lafiya kalau". Cikin danne bacin ranta. Ya yi shiru cikin zargin kansa. Ya san tabbas ya tabo Innar, don ta sha ce masa idan ba zai daina kyarar mata auta ba, to ya daina zuwa, babu dole. Cikin kasada ya ce "Amma Inna ga wannan katuwar yarinyar ki zauna kina hura wuta, ita tana wakar 'yar bebi? Duk wani dan arziki kamarta ai yanzu ya dawo ne daga makaranta, yana haramar tafiya islamiyya, amma ban da wannan, ban da karare ba ta san komai ba, shi yasa duk wasu abubuwa na yara masu hankali, ba ta san shi ba............" A fusace ta juyo ta zuba masa jajayen idanunta, ta ce "Kai saurara. Wai me ye gaminka da yarinyar nan ne? Me ta tare maka? In don oyoyon da ta ke yi maka ne ba ka so, zan hanata, amma wannan sababin da kake yi mata ya ishe ni. Ka zo gidan su ka uzzireta babu gaira babu sabar? Ba ta zuwa makarantar, idan kai ka haife ta sai ka dauketa ka kai ta". Ya sunkuyar da kai ya ce, "Allah Ya ba ku hakuri Inna, Inna Allah Ya huci zuciyarku". Ta ja tsaki, "Tsuuuu!" Ta ci gaba da aikinta tana ta sababi, shi kuma bai kara tofawa ba, bai kuma tashi daga durkuson shi ba. Malam Bedi ya yi sallama ya shigo, rataye da fartanyarsa da alama a gajiye ya ke likis, sai gumi ke disa daga wuya da goshinsa. Yana ganin Habibu sai ya fadada far'arsa, amma jin Inna Hure na ta sababi sai ya maida fuskarsa ya dinke. Ya dade yana sauraronta ba ta san ma ya shigo ba, tana ta fadan idan Habibu ba zai daina tsangwamar mata Mairo ba, to ya daina zuwa, don ba ita ta kirawo shi ba. Malam Bedi ya yi gyaran murya, sai a nan tasan da tsayuwarsa. Ta ce "Ai gara da ka zo, dama binka zan yi yanzun, ka ja wa yaron nan kunne ya sakar wa diyata mara ta yi fitsari, tunda ba a gidansu ta ke zaune ba, balle ya ji kunya don an ce kanwarsa ce". Malam Bedi ya ce, "Anya Hure? Kina kyautawa abin da kike yi wa Habibu? Ina laifinsa don ya zo gaishe ki? Wannan yarinya da kike ta tada jijiyar wuya akan an gaya mata gaskiya, wane ne majibincin al'amarin ta nan gaba a bayan mu? Wannan din dai da kike cewa ya fita harkarta shi ne ba wani ba. To idan ya fita harkar tata ranar da babu mu, wane ne zai shiga? Shin ma me ya yi mata da zafi? Don kurum ya ce ta dinga wanka? To ki yi hakuri, Habibu ya daina cewa 'yar ki ta yi wanka, don Allah ta shekara ba ta yi ba. Kai taso mu tafi masallaci kar mu rasa jam'i". Ai jin haka ta yi daki da gudu ta yayibo mayafinta da takalmin robarta, a gujen ta sake fitowa, "Yaya Habibu ni ma zani masallacin, dama tun jiya ban yi sallah ba". Wani takaici ne ya sake kama shi, ya hadiye ya ce, "To mu je, amma sai ki tsaya a wajen masallacin daga gindin bishiya kina bin jam'in, don mata ba sa zuwa masallacin maza". Ta ce "To idan mun fito zaka rakani mu je mu tsinko wa Inna tsamiyar kunu? Dama Rabe shi yake dora ni, kai kuwa ka ma fishi tsawo". Ya kama baki, "Yanzu Mairo bishiyar tsamiya kike hawa?" Cikin son ta burge shi, da alfaharin hakan sosai a kwayar idonta, ta ce "Mu hau tsamiya mu sauko, mu hau magarya, mu hau dinya, mu tsallaka goba. Rannan Lanto ta fado tim! Ta karya kashin baya, ni kuwa idan na makale a jikin reshen bishiya kamar 'yar Birrai nake. Bana fadowa, sai dai in ciko bujena da goba da tsamiya........." Ya yi gaba ya rabu da ita don takaicinta kamar ya amayo zuciyarsa, amma sai ya yi tunanin to ita me ye laifinta? Innarta ce ta daure mata gindi. Habibu saurayi ne dan kimanin shekaru ashirin da biyar. Ya kammala kwalejin horas da malamai ta Kano, wato (SAS), yana jiran sakamako ne ya wuce babbar makaranta, kodayake ma abin da ya kawo shi Gurin-Gawa kenan yanzun, wanda yake son su tattauna da mahaifinsa. Alhaji Abbas Mai goro kanin Malam Bedi ne ciki daya, uwa daya uba daya, shi ke rike da Habibu da hidimar karatunshi, ko da yake morar juna suke tunda kuwa duk wahalar kasuwancinsa na goro, a wuyan Habibun ta ke, wadda ya ke gudanarwa idan ya dawo daga makaranta da ranakun karshen mako. Suna zaune a unguwar Yakasai a cikin birnin Kano. Yana da matan aure biyu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66