Chapter 24
Chapter 24
sutturu da kayan gyara? Sai dai duk yadda ta so ta dinga taimakawa Mairon tun a makaranta Mairon ba ta yarda, cike ta ke da wadatar zuci, kuma cikin godiyar Allah. Mairo ta yi wa Nabilah jagora zuwa dakin Baffa. Ta zube a kasa ta gaishe shi, ya amsa cikin far'a da cewa, "Lafiya kalau Nabilah, an gama karatu sai aure ko, ko kuwa babbar makaranta za ki wuce kamar kawarki?" Ta ce "Eh, makaranta zan wuce". Ya ce "To Allah Ya ba da sa'a". Sannan ta gaya mishi ta zo ta dauki Mairo su je gidansu, iyayenta su ganta. Ya ce "Babu damuwa, don Allah kada Mairo ta kai dare". Suka ce "Insha Allah". Cikin nutsuwa Nabilah ke tuki har suka hau kan titin sakateriyar Audu-Bako, Mairo ta dauka Tarauni suka nufa, sai ta ga Nabilah ta karya akalar motar ta sha round ta hau kan titin state library, ba ta kai karshen titin ba ta yi kwana ta shiga unguwar Ahmadu Bello Way, ta tsaya a harabar gidansu mai lamba dari da biyu (No. 102), suka rufe motar suka karasa cikin gidan. Tun Mairo na mamakin tangama-tangaman falullukan da suke wucewa har ta daina mamaki, sai tazbihi ga Allah Mai azurta wanda ya so. Ba ta taba shiga gida irin wannan ba ko a mafarkinta. Ba su tsaya a ko'ina ba sai a babban falon Momin Nabilah, wadda ta fito tana tafa hannu tana 'Lale da Mairon Nabilah". Ta yi murmushi ta zamo daga cikin kujera tana gayas da Momin, kamin ai haka tuni Nabilah da wata dattijuwa wadda da alama mai aiki ce sun cika gaban Mairo da kayan tande-tande da lashe-lashe irin wadanda ba ta taba ci ba a rayuwarta. Shi ma Daddyn Nabilah ya sauko yana marhaban da Maryam. Ya zauna a cikin su, Mairo duk ta kasa sakewa sabida bakunta da rashin sabo. Saukin kan iyayen Nabilah ya burge ta. Ta tabbatar Nabilah 'yar gata ce ta karshe, ita kadai ce kwallin kwal, a wurin iyayenta. Daddy ya ce da Mairo da zarar takardunsu sun fito ta kawo mishi zai taimaka su samu gurbi a jami'a ita da Nabilah, ta yi godiya sosai. Karfe biyar na yamma Mairo ta yi haramar tafiya. Akwati guda Momi ta shake mata da kayan shafa da dogayen riguna kala-kala, Nabilah ta maidota gida. Tana shigowa idanun Hajara da Habiba akan jakar hannunta. Jikin Habiba har rawa yake, ta bi bayan Mairo tana son ta ji ina Mairo ta samo wannan diyar arzikin, har ga shi ta dawo da galleliyar jaka cike taf da kaya. Har karo suke ita da Hajara wajen shigowa dakin. Habiba ta ce "Bude jakar mu gani, me muka samu?" Hajara kuma ta ce "Wannan bakauyar ta iya bude irin wannan jakar ne? Gafara nan ki gani". Ta jawo jakar ta soma kici-kicin budewa. Ta zazzago duk kayan da ke ciki tana al'ajabi. Habiba ta ce "Ina kika samo wannan diyar arzikin kuma?" Mairo ba ta yi magana ba suka soma kasawa, Habiba ta daga rigar da ta fi kowacce kyau a ciki, ta ce "Wannan zata yi wa Ladidi". Ta sake daga skirt da rigarshi ta ce, "Wannan sai a bar wa Batulu idan ta kara girma zata yi mata dai-dai, ke ki rike wannan din". Ta tura mata wata 'yar yaloluwar rigar barci suka tattara kashi uku bisa hudu na kayan suka yi waje da sauri har suna tuntube tareda karo da juna kada Baffa ya jiyo su suka gudu dakinsu. Mairo ta ce, "Allah na tuba, suttura tsumma, mene da zan damu kaina?" Duk da Baffa ya hana a bata aikin wahala wanda ya fi karfinta ba su fasa ba a bayan idonsa. Mairo na hakuri da su da kokarin kyautata musu su da 'ya'yansu a kullum, amma ta rasa dalilin da yasa mutanen nan suka ki jininta, ko zata wuni tana aikin bauta, shara, wanke-wanke, wanki da wankin bandaki ba zata taba yi musu gwaninta ba, balle kalmar “madallah” ko “an gode” ta gitta a tsakani. Watanni uku cif da gama makarantar su ta samu labarin fitowar jarrabawarsu, don haka ta soma shirin zuwa gidan su Nabilah don su je makaranta su karbo sakamakonsu. Baffa da kanshi ya kaita gidan su Nabilah tana yi masa kwatance tana nuna masa hanya har suka iso gidan. Ya sauke ta ya juya da cewa, idan sun dawo Nabilar ta maidota gida. Amma Allah sarki, sai ta tarar da Nabilah kwance ba ta jin dadi. Ta zauna a gefen gadon da ta ke kwance ta dora hannu akan goshinta, zafi rau! Momi ta shigo da filet a hannunta mai dauke da soyayyar plaintain da dankali da kwai, ta ce "Ungo ba ta Maryam da kanki, watakila zata ci, tunda ni nayi-nayi ta ki karba". Mairo ta ce "Haba Nabilah, ciwo da rashin cin abinci ai abin ba kyau, ki daure ki ci ko kadan ne don Allah". Ta karba tana kokarin mikewa, Mairo ta tusa mata filo a bayanta don ta ji dadin jingina. Momi ta fita ta bar su. Tana fita Nabilah ta fashe da kuka mai tsanani. Hankalin Mairo ya tashi, ta ce "Lafiya Nabilah? Wani abu ya faru ne?" Cikin kuka ta ce, "Me ye bai faru ba? Hajiyar Daddy ce ta zo ta ce ba ta yarda na ci gaba da karatu ba, aure za a yi min da wani cousin dina. Bayan kuma bana sonsa, kuma sati mai zuwa za a daura auren, shi ma bai ce yana sona ba, wai wata Igbo ya zo musu da ita daga can inda yake karatu a Kudu, shi ne ba su amince masa ba, suka ba shi ni. Allah na tuba auren soyayya ma bai tsira ba a wannan zamanin balle auren tushe? Sabida Allah na yi kama da matar tushen iyaye?" Mairo ta rasa abin da zata ce "Ki ce ba ciwo kike ba, tunanin aure ne. Ni ban ga aibu a nan ba, tunda iyaye ne suka hada, ai ALHERI ne, kuma alherin suke nufin ki da shi. Ki yi biyayya ga iyayenki Nabila za ki ga da kyau a rayuwa. Soyayya aikin banza ce, don watakila yadda kike son mutum shi ba haka ba ne a zuciyarshi ba. Na gani akan kaina Nabilah. Har yanzu kuma ban ga inda soyayya ta kaini ba, sai kunci a zuci, ruhi da gangar jiki. Nabilah yau zan gaya miki abin da ke raina shekara da shekaru. Wato soyayyar Uncle Junaidu. Na dauka yadda na ke azabtuwa a zuci, da gangar jiki da soyayyarsa, shi ma haka yake sona, ashe ni ban sani ba, Uncle ba haka ba ne a zuciyarshi ba. A ranar da na yanke shawarar fallasa mishi asirin zuciyata, a ranar ya zame, ya gudu ya barni, ba tare da ya sanar da ni komi a kanshi ba. Wanda ke nufin ba ya bukatar anymore mu'amala da ni. Har yau ni kadai nasan abin da nake ji a zuciyata Nabilah. Hasashenku ke da Innata, bai zamo gaskiya ba, Uncle Junaidu ba SO NA yake yi ba, tausayina ne da taimako". Nabilah ta yi shiru cikin mamaki, yau Allah Ya nuna mata ranar da Mairo ta bude bakinta da kanta ta fada mata cewar tana son Uncle Junaidu. Ina ma ace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66