Chapter 60
Chapter 60
ta sani shekaru goma sha biyu a baya. Wannan cikakken magidanci ne, da yasha gwagwarmayar rayuwar neman ilmi cikin fanninnika daban-daban, ba dan saurayi Junaid Galadanci ba. Duk da alamun shekaru da suka hau kansa, har yanzu yana nan a Junaidunsa da ta sani, ma'abocin zati da kamala, gami da kwarjini bayyananne daga Sarkin halitta. Ta rasa cikin halin da ta samu kanta, rudewa ce ko gigicewa ce? A'a, ko kuwa gaba daya makuwa zata ce ta yi? Ta juya da baya–da-baya zata bar ofishin, ya juyo a hankali ya dubi mai shigowa. "Mariama!" Maironshi da a kullum ta ke zuwa a farke, ko cikin mafarkinshi. Mairon da dai-dai da rana daya cikin shekaru goma sha shidda, zuciya ba ta taba hutawa da kaunarta ba. Ruhi bai bar mafarkinta ba, haka tunani bai taba kuskuren manta ta ba. Ya dago Habib ya dauke shi tare da kama hannun Amir ya zauna a kujerar da mutane suke zama don ganawa da shi. Cikin wata irin kassararriyar murya, ya ce. "Ya ya za ki koma? Ko ba ke ce 'Proffessor Maryam Bedin ba?" Ta ja tunga a jikin kofa, ba tare da ta juyo ba. Ita bata fita ba, ita bata juyo ba. Hannunta jikin marikin kofa, ta ce "Ni ce". Ya ce "To mene ne ajandar?" Ta ce "Na zo neman alfarmar V.C ya samu halartar 'conference' dina ne". Ya yi murmushi yana dauke da Amir ya tako har inda ta ke tsaye. Wani irin sassanyan kamshi da ba zata ce ko na wanne turare ne ba a duk iya sanin da ta yi wa turare ya kassara mata gabbai. "Na kasance ma'abocin son 'twins' Dr. Mairo, ko za ki bani aronsu? Na dawo miki da su bayan awanni goma sha biyu?" Wannan karon ne ta juyo ta dube shi, wasu kibbau na tsohuwar soyayya suka soki idanun kowannensu. Tsohon tsimi ya tashi, wanda ya yi sanadin tashin tsigogin jikin kowannensu. Da kyar ba tare da ta sake yarda sun hada ido ba, ta ce. "Idan iyalinka suka tambaye ka ina ka samo su mai girma V.C me zaka ce musu?" Babu bata lokaci, ya ce da ita. "Ya'yana ne, wadanda Mairon Gurin-Gawa ta haifa mini..............." Kuka ya kece mata, don haka da gudu ta fice daga ofishin tana ji a ranta, ta fasa yin 'conference' din, tunda shi ne ya yi sanadin da ya taso da tsohon gyambon da ya dade da warkewa a zuciyarta. Gidan Baffa ta wuce kai tsaye, ta nufi dakin Habiba ta kwanta tana sakin ajiyar zuciya mai nauyi. Ta yi juyi a lallausan gadon Habiba tana tariyo abinda ya faru cikin 'yan mintina kalilan. Baffa ya shigo dakin ya zauna a kujera yana fuskantarta, ta goge hawayenta, ya ce. "Me ya faru? Ke dai har gobe abun kuka ba shi da wuya a wurinki? Yanzun nan Habiba ta yi min waya ta ce, kin shigo da gudu kina kuka. Idan ka girma sai kasan ka girma, ka koyi dauriya da juriya irin ta manya. Ba akan kowanne kankanin abu ka bare baki ka yi ta kuka a gaban mutane ba". Ta yi murmushi tana goge hawayen idanunta, ta ce. "Baffa, Uncle Junaidu na gani, bayan wucewar shekaru goma sha biyu. Ya tuna min da abubuwa da dama da suka faru cikin rayuwata, shine dalilin kukana, domin na tuna abubuwa da dama da yanayin shekaru da cigaban rayuwa ba su sani na manta ba". Ya ce, "kwanannan naji a labarai anyi ‘appointing’ din shi matsayin shugaban jami'ar Bayero ai. Har yau har gobe kuma bai fasa zuwa gidan nan yana gaishe ni ba, bai fasa yi min manya-manyan alhairori ba. Sannan son ki har yau bai barshi ba. Ban taba ganin 'SOYAYYAH' irin ta Junaidu ba. Don haka ni ma har gobe ban fasa yi mishi addu'ar budi da nasarar rayuwa ba". Mairo ta cika da mamakin jin cewa Uncle Junaidu na zuwa wajen Baffa har yau. Amma koda wasa Baffan bai taba gaya mata ba. Ba ta gama mamakinta ba su Habib suka shigo suna ta tsalle, kowannensu rike da kit-kit da leda fal 'choculates' suka fada jikinta. "Mummy mun dawo... Daddy yana gaishe ki". Sai Baffa ya tashi ya fita, ya tarbi Junaid a dakin bakinshi. Habiba ta shigo dauke da kulolin abinci. Su Amir suka makale ta suna ta ba ta labarin inda Daddy ya kai su. Ta ce, "Wai wane ne wannan Daddyn?" Amir ya ce "Daddyn Mummy ne". Mairo ta ce "Rabu da shirmen su Mama, shugaban jami'armu ne". Habiba ta yi murmushi ta ce. "To ko da shi za a yi ne?" Ta yi shiru ta daure fuska bata bata amsa ba. Don ba abin da ta tsana a rayuwarta irin a yi mata zancen aure. Baffa ya dawo dakin yana murmushi, ya same ta tana cin abinci. "Idan kin kare sai ki je ku gaisa da Alhaji Junaidun. Daga nan ya ce yana so zai kai Amir asibiti, don ya ga alamun ba shi da lafiya". Matsayin Uncle Junaidun da kimarshi da ke zuciyarta, ya fi gaban ta ce ba zata je ba. Baffa ya ci gaba da yi mata nasiha mai sanyaya zuciya da sanya imani, akan lokaci ya yi da ya kamata ta tsaida hankalinta wuri guda ta yi aure, domin cikar mutuncinta a duniya da lahira. Tunda Amiru da Daddynshi basa bukatar komen. Ta yi sallama a kofar dakin, yana zaune cikin kujerun (leather) da suka yi wa dakin kawanya, Habib da Amir akan cinyoyinsa, yana ta haba-haba da su kamar ya maishe su cikinsa. Ya dago idanunshi da suka yi fari sol, yana dubanta. A zahiri Maironshi ce, sai dai fa wannan Mairon babbar mace ce 'yar shekaru talatin da doriya, wadda kuma a idanunka da kiyasinka ba zata fi shekaru ashirin da biyar ba. Wannan bakauyar da aka kawo mishi kafafuwanta jawur cikin lalle tsohuwa ta fada kwata, fatar kamar shuni, yau idan ka dube ta, tsammani zaka yi Balarabiyar Omman ce, ba wai 'yar asalin kauyen Gurin-Gawa ba. Kallonta ya ke, kallon da ke nufin al'amura da dama. Ita ma kallonshi ta ke, kallon da ke tuna mata da al'amura da dama. Da gaske Uncle Junaidunta ne, sai dai wannan ya kara yi mata GiRMA. Ta TUNA BAYA... ta tuno ALHERInsa gare ta, ta tuno SIRADIN RAYUWArta, ta yi ALKAWARI ko BAYAN RANTA matsayinshi ba zai taba canjawa daga zuciyarta ba. Cikin muryar GIRMA ya ce. "Mairo, ina Amiru Abdurrahman?” Ta kai gefen mayafin abayarta ta dauke wasu siraran hawaye da suka kawo mata zarya. A hankali tace. “Mun rabu!” Duk suka yi shiru na 'yan dakikai. Can kuma ta kawar da shirun da cewa. "How comes kai ne sabon V.C dinmu, amma ban taba sani ba?" Shi ma ya yi murmushi ya ce. "Ni nasan kina cikin 'proffessors' saidai ban tabbatar ba, sannan ban taba tunanin ba kya tare da maigidanki ba, a wane dalili zan nemeki? Sannan bani da tabbacin ke din ce ko ‘namesake’ dinki ce, na dai ga sunan da ya tsayamin arai ‘among the proffessors’, Sannan ai ban dade ba ai, banyi dadewar da zaki san ina cikin makarantar ba” tace “haka ne”. Ta sunkuyar da kai kafin ta dago ta sake cewa "Ikon Allah kawai". "Ni ma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66