Skip to content

Chapter 65

Chapter 65

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

shi. Ya amsa yana duban ta sosai, ganin yadda ta ramar da kanta cikin ‘yan kwanaki kalilan saboda damuwa. Bai nuna mata komi game da zuwan Junaid da Amir ba, tambaya ta farko da ya watso mata ita ce. “Mairo maza biyu za ki aura ne???” Ta cira kai da sauri ta dubi Baffanta, ya girgiza kai ya ce, “Yo maza biyu mana? Kin amshi maganar Junaidu, an gama komi sai shafa fatiha kadai ya rage, sai kuma ki turo min Alh. Abdurrahaman da kansa ya zo bikon ki? Sannan shima Amiru ya zo, dukkanninsu da rokon a maida aure. To dukkansu akwai mutunci da ganin girman juna tsakanina dasu. Don haka bana bayan kowa, zabi yana gare ki, kamar yadda shari’a ta baki dama. Ina so ki gaya min wanda kika fitar ni kuma ranar da na sanya ba zan daga ba zan daura aure”. Kanta a sunkuye ba ta yi magana ba, har sai da Baffa ya gama yana sauraron ta. Ganin ta ki yin magana ya ce, “Kefa nake saurare Mairo”. Daga can kasan makoshinta ta ce, “Baffa ni bani da zabi a cikinsu, kamar yadda ka ce sharia ta bani damar in zaba, ni kuma na baka wannan damar, ka daura da duk wanda ka ga ya dace. Duka ina son su ina kaunar su, don haka ba zan iya zaben daya a cikin su ba”. Baffa ya girgiza kai yana murmushi. Autar Inna Hure, bai san sanda zata daina yarinta ba!. Ya ce, “To shi kenan, tunda haka kika ce, na kuma gode da wannan GIRMA da kika bani, ya nuna min cewa kin amince ba zan yi miki zaben tumun dare ba. Da fatan duk wanda na zaba miki a cikinsu za ki yi min biyayya shima ki yi masa, ba tare da an tsaya yin wasu tone-tone da kwakulo laifin da ya riga ya shige ba, za ki zauna lafiya dashi har karshen rayuwarmu”. Kanta a kasa ta ce, “Na yi wannan alkawarin Baffa”. Ya ce, “To tashi ki koma kan aikin ki, Allah ya yi miki albarka”. Cikin zuciyarta ta ce, “Amin”. Ta taso ta fito kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Daga Amiru har Junaid ba ta kara jin duriyar kowa ba. Ta bi shawarar Nabilah, da ta ce dukkansu kar ta neme su ta rabu dasu. Sai ana i gobe daurin auren da ba ta san da wa Baffa zai daura ba a cikinsu. Text din Uncle Junaid ya shigo cikin wayarta da misalin karfe uku na sulusin dare. Ta zaro wayar daga karkashin filonta, hannunta na rawa ta duba, ga abin da ke rubuce. SAKON UNCLE JUNAID GA MAIRO! “Marriage is much more important than mere relationship. It’s the root of all family tree. Any mistake in sowing the seed will be disastrous.... a mature seed has better chances for germinating than an immature one.... A garden close to one’s home has to be watered and tendered than that which is very far away................... -Mai son ki. (wato aure yafi muhimmanci fiye da dangantaka kawai. Domin shine jijiyar bishiyar iyali gaba daya, don haka hadari ne babba asamu kuskure wajen dasa wannan bishiya.... kosashshen iri zai fi saurin yado fiye da talalabuwa.... lambun da yake kusa da gidan ka zaka fi bashi ruwa da kulawa, fiye da wanda yake nesa.............). Ta karanta ya fi cikin carbi, kafin ta fahimci me sakon Uncle yake nufi. Yanzu ne ta fahimci ashe duk sakonnin nan da ake turo mata tana Michigan da ‘logo’ na hular ilmi, ashe Uncle Junaidu ne. Ta kifa kai cikin filon ta, tana kuka mara sauti. Kukan tausayin Uncle Junaidu! A lokacinda ta fahimci Uncle Junaid ya sadaukar da soyayyarshi ga aurenta da ‘ya’yanta..... Ta yadda har ya kira alakarsu da ‘mere relationship’. Ita ma ta yarda ta amince AMIRU SHI NE ZABIN ALLAH, ba zabin zuciyarta ba......!!! [8/20/2019, 06:30] Meema: Daga kowanne bangare ba su samu matsala ba, sun samu kwarin gwiwa daga Baffa, Yaya Habibu da Alh. Abdurrahman Gaya. Wadanda burinsu kenan. Hatta Hanan wadda ke da 'ya'ya biyu a lokacin da mijinta Ramadan ta samu halartar walimar maida auren Dr. Mairo da Amirunta, Amina da Uncle Junaidu, wadda aka gabatar a ranar asabar, juma'a, ashirin ga watan maris, daruruwan jama'a suka shaida daurin auren Mairo da Amiru a karo na biyu, a kofar gidan Alh. Abbas mai goro. Wannan aure ya ga kusoshin ilmi, daga Kano da wajenta, da daukacin jami'o'in Najeriya. Furofesoshi, kwamishinoni da daktocin ilmi, abin ba a cewa komi. Daga Mairo har Ameeru babu mai ra'ayin bidi'o'i, dokance suke da a sake mallaka musu juna. Tsohuwar soyayya ce ke aiki tare da taimakon sabuwar soyayya. Ta dankawa Alh. Abdurrahman da Hajiya Aisha jikokinsu kamar yadda suka nemi alfarmarta, sai fatan Allah Ya ba ta wasu masu albarka. Tana nan zaune a bakin gadonta, tana jiran angon wanda ke can yana ganawa da bakinshi, tare da duba agogon hannunta. Rabin awa kenan da fitar Dina, ta fada bayi ta sake sheko wanka mai suna wanka, tunda kuwa ba ta taba yin irinshi a rayuwarta ba. Ta feshe jikinta da 'fehrenheit' da 'cerruti' dinta kamar yadda ya ke a al'adarta. Tana kokarin sanya kayan barci ya turo kofar ya shigo cikin bulalen 'pyjamas' yana rike da wani dan fulas mai tsananin kyau. Kunya ta kama Mairo, kamar bata taba sanin Amirun nata ba, wanda hakan ya janyo ta sanya rigar a bai-bai. Amir ya yi murmushi, ya rausayar da kai ya iso gare ta, ya ajiye filas din hannunshi a gefe, ya dora kanshi a dogon wuyanta. At last! Sa’ar tashi ce a karo na biyu. Gashi ga Maironsa, bayan gushewar shekaru uku kwarara, cikin duniyar kuntatacciyar soyayya. Shikuwa me zai yiwa Uncle Junaidu, ya biya shi a wannan duniyar? Babu, sai adduar Alheri. Kyawawan fuskokinsu suka zahhara cikin mudubin. Dukkansu suka saki sassanyar ajiyar zuciya mai nauyi. Wadda ke cike da godiya ga Allah! Cancarakas! Ya dagata ita da filas din da ya shigo da shi sai 'bed-room' dinsu. Ya zaunar da ita a bakin gado, ya mika mata filas din, ya ce. "Sako ne daga Nabilah, ta ce hannu-da-hannu na baki. Ya zama shi ne cimarmu a wannan daren, sai dai ban san ko mene ne a ciki ba". Ta soma kicin-kicin bude filas din, da kyar ta samu ta bude. Suka bi cikin filas din da kallo dukkanninsu. “Kwadon Rama” ne wanda ya ji kuli-kuli, tumatur da albasa sai kamshi ya ke. Dariya ta kama Mairo, don ta lura Nabilah dai na son a TUNA BAYA…..... ne. Mairo ta soma cin kwadon ramarta sosai, kunnenta kamar ya tsinke don dadi. Ta kusa cinyewa ya rike fulas din, ya rausayar da ido yana yi mata kallon nan nasa da shanyayyun idanun nan nasa, wanda ya kassara kuzarin jikinta. Ya tada wani tsohon al'amari, wanda ya riga ya shude a tsammaninta. Amir da Mairo, suka ce “Takori kauce a nan, yau bama bukatarki”. *** Washegari Daddy yayi kiransu, ya danka musu ‘passport’ dinsu, mai dauke da visar kasashen duniya guda uku; Athens, Amsterdam da Pretoria. Yace da Amir yayi amfani da hutun sa na karshen shekara suje su huta tsayin watanni uku. Mairo bata tashi dawowa ba, sai da guzurin ciki

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66