Skip to content

Chapter 31

Chapter 31

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

ku, amma hakan ba yana nufin za ki zauna zaman jiransa ba ne, a'ah, matar mutum kabarinsa. Na ji dadi da ba ki gaya wa mahaifiyarsa ko ke wace ce ba, da ina nan ma, da ba zaki je ba, koda yake ba wajenshi kika je ba, wajen wadda ta yi SANADIN kawo shi duniya ne, gaishe ta da zuciya daya ba laifi ba ne. Ita darajar diya mace a wurin da namiji guda daya ce, don haka yi min alkawarin mantawa da soyayyar Uncle Junaidu. Ki bude file ki sanyata a ciki, ki rufe, ki adana. Ki fuskanci rayuwarki ta gaba, kin ji Mairona?" Cikin shesshekar kuka ta ce "Na ji Yaya Habibu, na yi maka alkawari". Ya tayar da motar suka harba kan titi. Mairo na addu'a cikin ranta, Allah Ya ba ta ikon rike wannan muhimmin alkawari da ta yi wa Habibu, domin ba karamin nauyi ba ne ya azawa zuciyarta ba, da ta ke fatan Allah Ya ba ta ikon saukewa. *** *** "KUDI" Aka ce su ne 'KARE MAGANA'. Suna zuwa gida me zata gani? Ma'aikatan Julius Berger. Sun sa katafila sun murkushe gidan Alhaji Abbas, sai fili fetal. Tuni har sun fara auna rodi sun kakkafa matattakalar katako sun fara aikinsu. Su Habiba da yaransu duk suna gidajen iyayensu, sai an gama ginin zasu dawo. Can gidan su Habiba suka je suka dauki yaran, Habibu ya zuba su a mota suka wuce Dutsinma. Mairo da takwararta da Muhammad da ta ke kira Abbana suna baya, Abbas yana gaba tare da Habibu, wanda ke tuki cikin kwarewa da sukuni. Abba yana ta yi mata tambayoyi tana ba shi amsa dai-dai yadda kwakwalwarshi zata dauka. Sanyin A.C gauraye da ni'imtaccen kamshin turaren Yaya Habibu na 'Miyaki' ya gauraye motar. Ya sanyawa Mairo wata irin nutsuwa cikin zuciyarta. Habibu bai tsaya ba sai a garin Funtuwa, ya sai masu gasassun kaji da lemunan kwali da ruwan Faro, suka mika. Bai kara tsayawa ba sai a kofar gidan kakannin matarshi da ke cikin garin na Dutsinma. Habibu ya fidda waya yana kiran Dina, ya ce "Ga mu nan mun iso". Mairo na gefe, harde da hannuwanta a kirji. Idanunta kur, akan kofar fitowa gidan, tana zuba idon ganin wace ce wannan Dina, da ta mamaye zuciyar Habibu haka? Wace ce Allah Subhana Ya yiwa baiwar samun wannan Habibun? 'Yar Katsinawan sai ta fito, kyakkyawar fuskar fal far'a. Sanye da doguwar bakar riga da mayafinta kirar Bahrain. Fara ce, amma ba sol ba, ta ma fi dai-dai da a kirata choculate colour. Mai wadatar giran ido, gashin ido da sumar kai. Ba ta taba ganin mace mai kyawun fata irin matar Habibu ba. Gayun ne ya hadu da jin dadi, ya gauraya da hutu, ya cakude da wadataccen ilmi, sannan kwanciyar hankali da zaman kasar sanyi ya biyo baya. Suka yi wa juna wani irin sassanyar kallo ita da Habibu, sannan ta karaso ta rungume Mairo, tamkar ta tsaga kirjinta ta sanyata don kauna. Wani irin matsiyacin kamshi da Mairo ba ta taba ji ba ya ziyarci hancinta. "Lallai wasu tun a duniya Allah Ya ke ba su Hurul'eeni". Mairo ta ce a zuciyarta. Da tana ganin Dinan ce mai sa'a da ta samu Yaya Habibu, ashe shi ma Habibun mai sa'ar ne, don cikin mata dubu, da kyar zaka samu biyu irin Dina. Da tana ganin Nabilah 'yar gaye, ashe Nabilah 'yar dukununu ce. Ba ta gama zancen zucinta ba, tattausan hannun Dina kamar na jariri ya kama nata, ta ja ta cikin gida. Bayan ta bi 'ya'yanta daya bayan daya da kisses da runguma. Wata dattijuwa ce tsohuwa tukuf, sanye da atamfa super holland zaune a can kuryar kayataccen falon bisa darduma tana lazimi. Da gani babu tambaya, ita ce uwar Baban Dina. Habibu da yaran suka zauna a kujera yayin da Dina da wata yarinya budurwa da alama mai aiki ce suka shiga hidimar fito da warmers, plates, da cokulla. Ba ta katse laziminta ba, shi ma Habibun fita ya yi don samun jam'in sallar la'asar. Mairo tana fashin sallah, don haka suka zauna ita da yaran da Dina suna cin abinci. Dina ta rasa ina taka-saka-ina-taka-aje da Mairo? Soyayyar Habibu ta shafe ta. Ganinta ta ke tamkar kanwarta ta jini. Sai wajejen karfe biyar Habibun ya shigo, lokacin Hajiya ta idar da laziminta, suka soma gaisawa da Habibu. Itama Mairo ta duka tana gaishe ta. Dina ta ja ta dakin da ta sauka, ta hada mata ruwan zafi a baf da turarukan wanka, ta ce ta shiga ta yi wanka. Mairo ta ce, "Ai na yi wanka da safe". Ta yi murmushi, ta ce "Sakewa za ki yi, ita mace so ake ta yi wanka sau uku a rana. Idan hakan bai samu ba, ta yi sau biyu. Sannan na ji smelling din jikinki bai min yadda nake so ba". Don haka Mairo ta hau wanka, cikin kwami da ruwa mai dumi, da kamshin bathrobb din desire-dunhill mai sanyaya zuciya da ni'imtata. Da sabulun da ko a mafarkinta ba ta taba gani ba, wanda in ka yi wanka da shi, ba sai ka shafa mai ba. Ta ji fatarta har wani santsi ta ke da sheki. Jikinta ya yi laushi tubus. Ta dauro alwala ta fito, ta samu Dina na jiranta zaune a bakin gado. Ta zube mata kayan shafa da turarukanta, ta ce ta shafa, sannan ta dauko riga da siket masu kauri na Bersace ta ce ta sanya. Ta zaunar da ita a gabanta ta sa dryer tana busar mata da gashi, sannan ta bi layi bayan layi na gashin ta shafe shi da Indian hemp ta taje ta matse da bound, ta bi jelar ta jere da ribbons kala uku masu taushi. Nan da nan sai ga Mairo ta fito kamar Sushmita Sen. Dina ta yi murmushi ta ce "Maryama, haka kike da kyau kamar Habibu?" Mairo ta ji kunya, ta sunne kanta tana dariya, ta ce "Anti Dina ai ke kin fi Yaya Habibu kyau, fari kawai ya fi ki". Ta ce "Allah Ya nuna min ranar da tawa Mairon, zata girma ta tashi kamar wannan Mairon. Kinga yadda na ganki yanzun nan, haka nake so kullum na ganki. Ita mace ba abin da ya fiye mata jikinta daraja. Idan ta gyara shi, to ta gyara martaba da mutumcinta, mijinta zai like mata tamkar kaska, ya ji ba abin da ya ke so ya kusanta a duniya sai ita. Shi kamshi wata rahma ne da Allah Ya saukar mana mu mata, kuma shi ne babban sirrin rike da namiji. Kin ji ko Mairo?" Mairo na dariya ta ce "To ai ni ba ni da mijin". Ita ma ta tayata dariyar ta ce "Zai zo ne, gallele kuwa, ni na gaya miki". Can dakin baki suka iske Habibu, shi ma ya sake fesa wanka, ya yi shiri cikin T. shirt din DKNY fara sol da ratsin jaja-jaja da wandon jeans kai ka ce saurayi ne dan shekaru ashirin da biyu, babu mai yarda ya aje 'ya'ya uku a duniya, ya bi Mairo da kallo don da fari bai ganeta ba, ya ce "Kai! Halitta!!" Suka kyalkyale da dariya ita da Dina. Ya soma hararar Dinan cikin wata irin soyayyarta da ta kara

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66