Chapter 49
Chapter 49
ne, ni kuma na ga da na shata ai gara na sha tabar". Ta zumbura baki, tana toshe hanci ta ce. "Ni don Allah ka ba ni hanya na wuce..." Amma fa banda kaduwa ba abinda jikinta ke yi, Amiru ya bala'in sanin 'weakness' dinta. Karfin halinta da jarumtakarta suna ba shi mamaki. Kiri-kiri ga shi tana cikin kewar mijinta, a idanunta da gangar jikinta, amma a fatar baki ta nuna ba haka ba ne. “Ko in baki (hanky) ki toshe hancin da kyau??” Kanshi ya tura cikin gashin kanta ta baya, bayan ya cillar da 'bound' din da ta daure gashin da shi. Yana shakar kamshin kumfar 'pert-plus' da ta ke amfani da shi ba tare da ta sa wa gashinta 'relaxer' ba. Amma sai ka rantse kullum 'relaxer' ta ke shafa mishi. Can cikin kunnenta yake rada mata. "Rakiya za ki yi min Mairo". Da sauri ta ce "Zuwa wajen budurwarka?" Ya yi dariya, ya ce. "Ga budurwata nan ina tare da ita, shopping zan yi". Ta ce "Ni ba zan bika ba kullum kana yawo da wadannan gardawan masu shegen kallon tsiya kamar wasu 'body-guard' dinka". (Raymond da Franklyn). Yayi dariya. Ya ce "To zan sallame su. Mu biyu zamu yi tafiyarmu, sannan ba shan Aspen a hanya, in kin ganni zan saya ki kwace credit card din, hakan ya yi miki?" Ta gyada kai cikin gamsuwa. "Amma kai zaka fadawa Anti Dina". "Idan don wannan ne, ta kwana gidan sauki, uuwata ce ita ko kanwar ubana? Daga kawo ajiya?” Abin ya bata dariya amma ta gimtse. "To bari na karasa hada mata salad din, yunwa take ji". Har zuwa lokacin bai sake ta ba, ya bi ya kankane ko'ina na jikinta. Sai faman sunsunarta yake yi kamar zai hadiyeta. Sai da ta hada da magiya sannan ya sassauta rikon da ya yi mata. Tare suka fito ta isa ga Dina ta mika mata farantin, ta nufi dakinsu don ta kimtsa. Wanka ta sake ta zuba riga da siket na wani material yellow mai santsi, ta nada dan bakin mayafi a kanta, ta matse da fil ta kara feshe jikinta da turaren (fahrenheit). Tana kokarin saka takalmi ta jiyo Dina na kwala mata kira, don haka ta dauki jakarta 'polo' mahadin takalmin da ke kafarta ta fito. Ba ta san me ya fadawa Dina ba, ta ce "Amiru ya ce za ki raka shi shopping ko? To sai kun dawo". Suka hada ido ya daga mata gira, ya kashe ta da murmushi. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta. Ya mike yana kiran Raymond ya fada mishi su je sai ya neme su, yana tare da Madam dinshi. Ya karbi makullan motar Mairon hannun Dina, suka fito. Tafiya suke sannu a hankali, irin tafiyar da ke sanya nishadi a zuciyar ma'aurata, kuma irin tafiyar da ke kara wa masoya kusanci da juna. Babu wanda ke cewa uffan sai zuciyoyi kadai suke magaba. Ya mika hannu yana karo sautin Abdurrahman Sudaith da ke tashi a hankali cikin radiyon motar, cikin suratul Anfal. Hankalin Mairo na kara nutsuwa da mijinta, wanda dan zaman da suka yi na tsayin watanni ya sanya ta ke fuskantar kyawawan halayensa a hankali. Wadanda ada bata yi tsammani ba. In tayi la’akari da irin tsarin rayuwarsa da bigiren da yake rayuwa a ciki, da kuma irin mutanen da yake hulda da su. Ko su Raymond sun isa su dulmiyar dashi cikin dabi’un nasara. Sai ta tadda akasi ga tunaninta. Da farko dai ta fahimci Amirun ba’a kada shi a magana, ko me ka gaya masa zai baka amsa daidai da maganarka, ko ya baka wadda ta fita daraja, kuma ba shi da munafunci, kai tsaye yake fadin abin da ke cikin zuciyarshi ba tare da la'akari da cewa, zai yi wa mai sauraronsa dadi ba ko a'ah? Sannan Amiru mutum ne mai kula da sallah, da ba ta dukkan hakkokinta. Har ga tabon sujjada nan rangadede a kan goshinsa. Ga son 'yan uwansa da iyayensa da kulawa da su, irin mazan da duk son da suke wa mace ba sa hada shi da na iyayensu. Yana da ban dariya, yana da barkwanci, sai dai idan miskilancin ya motsa ya fi mahaukaci ban haushi da takaici. Ba ta kai ga gama tunaninta ba ta ji yana zungurin kugunta da mukullin mota. Ta juyo a hankali tana kallonsa, soyayyarshi na kara kamari a tare da ita. Kamar yasan me ta ke tunanin, ya kamo hannunta ya rike cikin nasa, ya kwantar da kai a kafadunta, ya dora mata dukkan nauyin jikinshi... "Mairo kada ki bar ni. Ba ni da harshen da zan fada miki adadin soyayyarki da ke cikin zuciyata. Ban taba son wani abu a rayuwata kwatankwacin yadda nake sonki ba, idan kika dauke iyayena. Ban taba yin soyayya ba Mairo sai a kanki. Nasan kin aure ni ne ba bisa son ranki ba, amma......" Ta yi hanzarin kai yatsunta ta toshe mishi baki. Ta kankame shi sosai jikinta yana rawa. "Kayi min alfarma kada ka kara yi min wannan zargin, domin kuwa Allah shaidata ne akan cewa na aureka ne da zuciya daya, cikin amincewa kaina cewa, kai ne mijin da Allah Ya zaba min; kai ne zabin Allah a gare ni. Daga lokacin da na fara ganinka, na ji wasu abubuwa sosai a zuciyata. Duk da soyayyar Uncle dina da nake fama da ita a wancan lokacin hakan bai hanani ba ka wani muhimmin gurbi a zuciyata ba, gurbi na ‘auratayya’ ba soyayya ba. Na kalubalanci tunanina ne a lokacin da cewa yaudara ce. A hankali na gane hakan ma ba ya zuwa sai da soyayya! Soyayya ta da Uncle Junaid wani abu ne da ya shude a wata rayuwata ta can a baya..., Past is past Ameeru, and you are my present...!!!" Amiru ya wani irin kankame Mairo yana mata sumba mai tsayi da zurfi, tsayin wani lokaci mai tsawo, kamin su samu nutsuwa cikin zuciyoyinsu. A yau ya samu wani irin kwanciyar hankali irin wanda bai taba samu ba tun haduwarsa da Mairo. Tada motar yayi suka harba kan titi. Ba su tsaya ba sai a shagunan da ke karkashin 'Sommerset mall'. 8/6/21, 1:16 PM - Kawata: 55555555555 Shi kadai ya shiga ya yo musu duk sayayyar da zai yi. Ta duk abinda zasu bukata na kwana uku. Ya bar Mairo cikin motar. Tsabar kishi irin na Ameer bai yarda da shiga da Mairoßs irin wadannan wuraren ba, bai tsaya a ko'ina ba sai a otel din 'Hyatt Regency' inda Amirun ya yi masauki. Hotel ne na manya, na daga wane sai wane. Ta dube shi a razane, a sanda ya kashe motar, sanda ta fahimci cewa a otel suke. Kamar ta yi kuka ta ce. "Haba don Allah? Me zan ce da Anti Dina?" Ya langwabar da kai abin tausayi a masangalin kujerarsa, tsayin lokaci bai ce mata komai ba, a cikin lumsassun idanunshi kadai ta gama samun amsar duk wani uzurin sa da dalilinsa, da kyar ya ce. "Ba kya tausayina ko Mairo? For quite a week kenan ina suffering. Sabida ke nazo, tun daga Nigeria har Michigan. Sannan idan na tafi na barki zan jima ban zo ba, sai kun yi hutun karshen semester, ban sanki da halin rashin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66