Skip to content

Chapter 20

Chapter 20

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

ta fito gaban ajinsu ta tsaya rike da takardu, domin wani abu ne da ta kware a kai, wanda Uncle Junaid ya koyar da ita, wato dabarun speech in public, ba tare da jin ko da dar a zuciyarta ba. Ta soma feso sassanyan Turanci daga makogaro zuwa harshe, sannan siraran labbanta su furta. Kai ka ce diya ce ga Herbert Spencer. Tana bayani ne akan Segmund Freud's stages of psycho-sexual development, tana farke theory tana yin kaca-kaca da ita tun daga phallic-stage... Anal stage... da 'yan uwansu. Sannan ta koma kan SOCIAL CLASSES; the BOURGEOISIE and the PROLETARIAT………. !!! Habibu da ke cikin 'yan ajin ya sanya mask (fuska) sai ya soma kuka. Sannan ya taso ya fito, zuciyarshi cike da alhinin ina ma ace... Malam Muhammad Bedi, zai dawo duniya yau ya ga Mairon shi na koyar da turawa, da sauran jinsin al'umma. Don haka Mairo yau da ta dawo gida ta ga sauyi sosai daga Yayan nata. Domin dai ya tabbatar ta tsaida hankalinta tana karatun, kamar yadda yake so. Yaje makarantar ne ya shiga cikin ‘yan ajinsu don yayi supervising hakan. Shi da Dina ne cikin three seater suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Ya daga kai ya dube ta yana murmushi, a lokacin da tayi sallama ta shigo. "Mairo 'yan makaranta......Mairon Dina….. Mairon Yaya Habibu". Ta yi murmushi, har kumatun ya lotsa. Za ta wuce cikin daki ya ce. "Zo zauna, mota zan sake miki". Da hanzari ta dago ta dube shi. Ya daga mata gira (in affirmation) watau cikin tabbatarwa "Gaya min duk irin motar da kike so ni kuma na yi alkawarin zan yi kaffara in saya miki. Sannan ki mai da walwalarki kamar da, bana son ganin wannan shiru-shirun da kika koma. Sannan Dina ta fada min ko hira kin daina yi da ita, kullum sai karatu. A dinga rage karatun, a dinga baiwa zuciya da kwakwalwa dama su huta, sai karatun ya fi zaunawa sosai. Zan tafi Nigeria gobe, akwai muhimman al'amura da zamu gabatar ni da Amiru a Abuja, zan yi sati daya, me kike so in kawo miki? Dina ta rubuta min kayan abincinmu na gargajiya su kuka, daddawa, rogo, kubewa da sauransu. Ke kuma fa?" Ta yi murmushi kanta a kasa ta ce, "Ladidi nake son gani". Ya ce "Ai an yi mata aure. Kina ganin zan rabo mace da gidan aurenta ne na kawo ta? Ai mijinta ba zai so ba, ki yi hakuri ki kare karatun gida za mu koma gaba daya. Gobe sai ku je da Dina ki zabo motar da kike so, zan bar komai a hannunta". Ta yi godiya, ta kama hannun Little Mairo suka nufi dakinta. Dina da Habibu suka bita da kallo, dukkansu ba haka suke son ganinta ba. Gaba daya ta sauya, tun ranar da Amiru ya tafi, daga daki sai daki, daga littafi sai littafi na gaggan malaman sociology. Habibu na addu'ar Allah Ya sa ba sociology'n ne ya soma taba mata kwakwalwa ba. Shi yasa tun farko bai so ta zabi wannan kwas din ba, amma ta dage ita nan duniya shi ta ke so, ba don komai ba sai don ta zama Uncle Junaidu. Ita Dina da yake tasan dawan garin, wato Mairo ta soma kamuwa da matsananciyar soyayyar Amiru sai ba ta damu sosai ba. Habibu ya daga Nigeria a washegari, da tsarabar Baffa da iyalinshi rankatakaf! Da aiken Mairo ga Ladidi. Ita da Dina suka shiga gari suka yo cefanen kayan abinci da kayan amfanin gida da ya kare, sannan suka nufi wani kamfanin motocin (General Motors) dake nan cikin Michigan ta zabi mota irin tata ta da, watau GMC Terrain ruwan makuba, suka shirya payment Dina ta biya, ta karbo rasidi da takardun mota aka biyo su da ita gida. Duk a kokarinsa na son farantawa 'yar uwarshi, yana sauka a gidan Baffa ya kira wayar Dina, ko gaisawa ba su yi ba, ya ce ta hada shi da Mairo, ga Ladidi ga Baffa. Farin cikin da Mairo ta samu kanta da jin muryar Baffa da Ladidi ba zai fadu ba. Sun dade suna hira, inda Ladidi ke sanar da ita tsohon ciki ne da ita, ta yi mata fatan sauka lafiya, sannan ta baiwa Dina suka ci gaba da hira ita da Habibu. Washegari Dina ta kira shi don su gaisa, amma wayarshi a kashe, sai ba ta damu ba, ta ci gaba da ayyukan gabanta. Karfe biyu na rana agogonsu na can, ta sake gwadawa ko za ta samu, amma wannan karon ma an sanar da ita wayar a kashe ta ke. Yinin ranar zungur, haka ta yi ta nemansa amma ba ta samu Habib ba. Abu kamar wasa, har kwana uku ba su samu wayar Habibu ba, sannan ita ma idan ta buga ba ta shiga. Hankalinta ya tashi, amma ba ta bari Mairo ta gane ba. A rana ta hudu ne dabara ta zo mata. Ta kira layin Baffa, bayan sun gaisa ta ce, ko yana da labarin Habibu? Sun kasa samunshi a waya. Baffa ya yi gyaran murya ya ce "Tun ranar da ya zo, ya samu sakon cewa amininshi Amiru ba lafiya, don haka ya tafi Abuja wajenshi ban san halin da suke ciki ba". Dina ta yi zugum! Da waya a hannu, tunani iri-iri babu wanda ba ta yi ba. Ba ta fatan ya kasance ciwon Amirun yana da alaka da soyayyar Mairo. Ta sanshi bai iya daukan al'amuran rayuwarshi da wasa ba. Idan ya ce, yes to da gaske yana nufin yes din, babu gudu babu ja da baya, raba shi da abin nan da yake so sai wani babban ikon Allah. Sannan Amiru mai-nasara ne, bai taba sanya abu a gabanshi ya kasa samu ba. Jin motsin fitowar Mairo daga kicin ta yi azamar sauke taguminta ta kakaro murmushi, wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce "Baffa yana gaishe ki, yanzun nan muka yi waya da shi". Ta aje farantin da ke hannunta akan centre-table, ta ce "Ina amsawa. Ni Yaya Habibu lafiya dai ko? Tun ranar da ya tafi har yau ban kara jin wayar shi ba". Dina ta shirga karya "Am, eh, ya kira kina barci ne shi yasa ban tashe ki ba". Ta ja farfesun kifin da Mairo ta aje mata, ta soma shan romon da cokali. Tana satar kallon Mairo ta wutsiyar idonta. Wadda ta maida hankali ga labaran CNN da Mu'azzam Kanti, ke kwararowa. (Alkawari bayan rai). Amma a zahiri ba sauraronsa ta ke ba, kewar dan uwanta ne ya dame ta, da rashin jin dadin rayuwar ko ta yaya, da ta samu kanta a ciki. Ba ta rasa ci ba, ba ta rasa sha ba, mai kyau kuma mai dadi, amma zuciyarta a kuntace ta ke babu dadi. Tana ji a jikinta wani bakon al'amari mai GIRMA na shirin faruwa da ita, wanda ba zata ce mene ne ko na mene ne ba. Washegari da asuba bayan ta idar da sallah, ta yi azkar din safiya kamar yadda ta saba. Ta yaye labulen dakinta tana kallon yadda snow ta yi musu lullubi. Amma hakan bai hana Bature yin harkokin gabansa ba. Yau ranar ta kasance lahadi, don haka ba zata je makaranta ba, kai kofofi da tagogin gidan ma duk

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66