Chapter 42
Chapter 42
ba wajenka na zo ba?" Ya lumshe ido a hankali, tsayin mintuna biyu bai bude ba. Dr. Fredrick ya zame ya fita, don ya lura Amirun ba zai iya yi mata magana ba idan yana kallonsu. Ya sake bude ido a hankali ya dubeta, da wani irin sassanyan kallo. Ta yi hanzarin sunkuyar da kanta, sabida wasu irin allurai da ta ji suna bin jinin jikinta. Hawayenta na diga a kasa dis-dis. Ya tara hannu ya taro hawayen, ya ce "Wannan hawayen kuma na mene ne? Ni da kika ce ba kya so na? Ban yi kuka ba, sai ke?" Muryarshi bata fita sosai, ba don tana kusa da shi sosai ba, da ba zata ji shi ba. "How dare you want to me to believe you (ta yaya kike so in yarda da ke cewa) kin zo sabida ni ne? Bayan kin fada min ga wanda kike so, ni ba kya so na? Na hakura na tafi, don me Habibu zai takuraki ki biyo ni? To me kika zo ki yi min? Kin zo ne ki kara min ciwon, ko kin zo karasar da ni zuwa kushewata ne?" Ta dago sosai ta dube shi, ya yi saurin kauda kai, don ba zai iya jurar kallon tsakiyar idanunta a wannan lokacin ba, wadanda suke kamar 'magnet' cikin nashi idanun, suke kuma sanyaya mishi zuciya, tare da karya karfin zuciyar duk da yake rikewa da jarumtar zucin duk da yake takama da ita. Har yake ganin zai iya jayayya da ita, ga shi tun ba a je ko'ina ba, ta fara karya lagon zuciyarshi. Ta ce a sanyaye "Har airport na bika, dai-dai lokacin da jirginku ya tashi. Ban ce lallai ka yarda da ni ba, amma Allah shaidata ne!" Ta juya zata fita, har ta kai bakin kofa, ya tattara iya sautin da ya rage mishi a makoshi ya ce "Mairo!" Ta dakata, hannunta jikin marikin kofar, amma ba ta juyo ba. Ya yi tari kuful-kuful! sau uku, kamin ya ce "Fushi kika yi? Za ki sake tafiya ki barni? Ciwon sonki ya karasa ni? Ki yi hakuri idan na fadi wani abu wanda ya bata miki rai, zafin sonki ne ya kawo hakan. Dawo ki zauna tare da ni, ina jin wani sanyi cikin zuciyata, a dalilin tsayawarki tare da ni. Ki yi wa Allah, kada ki sake barina, har zuwa karshen rayuwarmu. My life has no meaning…... Idan na rasa soyayyarki. I’m impotent….idan ba tare dake ba! Bana son Habibu ya takuraki ki aure ni, soyayyarki na ke nema, ba da tursasawar wani ba". Wannan lokacin ba ta ce komi ba. Ta rasa abin da zata ce, ta kasa tantance shin abin da ta ke ji game da Amirun cikin zuciyarta da illahirin gangar jikinta a halin yanzu, soyayya ce ko kauna ce? Idan kauna da soyayyar ne baki daya, to shi kuma Uncle Junaidu fa? Shi kuma me ta ke masa idan ba so da kauna ba? Idan haka ne ke nan MAZA BIYU ta ke so ko yaya ne? Soyayya guda daya ce, wadda a halin yanzu ba ta san ko ta waye ba, don haka ba zata ce ba. Amma data tuna halin da Amirun ke ciki, yana bukatar lallashi da kauna daga gareta a daidai wannan lokacin kamar yadda likitanshi yace, sai ta dawo kujerar da ke fuskartarshi ta zauna kanta a kasa. Kamun kai da kunyar Mairon, su ne manyan al'amuran yarinyar da suke kara masa kaunarta. Ya tabbatar ba zata taba bude baki ta ce, tana sonshi ba, sai dai idan su kwana a hakan, wannan din ma ba karamin burge shi ya yi ba. Domin duk yarinyar da zata budi baki gatsar ta ce da namijin da bai zamo mijinta ba, ina sonka. To wallahi ba matar aure ba ce. Inda Allah Ya ceceta daga kaifafan idanun Amirun, shi ne shigowar Yaya Habibu, Dr. Fredrick da dattijon da a yanzu ta gane shi ne Alh. Abdurrahman Gaya. Mahaifin Amiru. Cikin murmushin jin dadin ganin dan nashi cikin yanayin da ya bashi mamaki, zaune sosai bisa gadon ya zuro kafafunshi kasa. Fuskarshi cike da walwala da yalwataccen murmushi ya karaso gare su, shima Amirun murmushin yake yi. "A'ah sauki ya samu, lallai, kai Mairo ta iya jinya!". Amiru ya harare ta, ya ce "Ni ba wani jinyata da ta yi, sai kuka ta ke yi mini. Kai Yaya Habibu mai yasa ka takurata ta zo? Me ya hada ciwona da zuwan Mairo Nigeria? Alhalin karatu take yi? Da ka kyale ta ai zan samu sauki ne a hankali cikin yardar Allah". Habibu ya harare shi ya ce "Kwarai fa, shi yasa na ga kamin ta zo ana ta janyo maka numfashi". Duk suka yi dariya ban da shi Amirun. Da kalaman Habibu suka jefa shi a tunanin anya ya cika namiji? Anya shigowar Mairo rayuwarsa bata maida shi mace ba? Dr. Fredrick ya ce "Ya ci abinci Mairo?" Ta girgiza kai, sannan ta dubi kular abincin da ke kan lokar jikin gadon, ta dauko ta bude, farfesun kaza ne da ya ji kayan kamshi, a daya kular 'chips' ne da soyayyen kwai. Tana son ta tambaye shi wanne zai ci a ciki, amma kunya ta hana ta, don haka ta zuba kowanne kadan cikin faranti daban-daban ta mika mishi. Dai-dai sanda ya debo shanyayyun idanunshi ya dora a kanta, sannan ya mika hannu ya karba. A hankali ta ce "Ba zaka wanke baki ba?" Cikin kankanuwar murya shima ya ce "Kin bani abin wanke bakin na ce ba zan wanke ba?" Ta ce "Ai ban san inda ya ke ba". Alh. Abdurrahman da kansa ya bude lokar ya fiddo sabbin burushi da makilin ya mika mata, ta bude ta shafa jikin burushin, Yaya Habibu ya mika mata roba. Tana zuba mishi ruwan robar 'swan' yana wankewa har ya gama, sannan ya soma cin abincin. Shi kanshi likitan ya yi mamakin yawan abincin da Amiru ya ci, wanda tunda aka kawo shi sai yau ya ci, “lallai so ba dama”. (Ya ce a zuciyarshi) sai ruwa ake kara masa mai dauke da sinadaran abincin maras lafiya. Hajiyar Amiru ta shigo, bakinta ya kasa rufo, ganin Amirunta na cin abinci, alamun sauki sun bayyana sosai a gare shi. Ta ce "Kai masha'Allah, har abinci ake ci? Lallai sauki ya samu (don ita ba ta san musabbabin ciwon Amirun ba)". Ta kalli Mairo da fuska ma'abociyar walwala, ta ce "Ina muka samo 'yar kyakkyawar budurwa?" Mairo ta dukar da kai, Alhajin ya ce, "Kanwar Habibu ce, kuma surukarki insha Allahu". Murmushinta ya fadada sosai zuwa dariya, ta ce "Da gaske?" Ta juya ta kalli Habibu "Na ce da gaske ne Habibu?" Ya yi murmushi ya ce "Idan Allah Ya yarda". Kunya a wajen Mairo, kamar ta nutse cikin kasa. Hajiya A’isha ta kamo hannunta ta rike cikin nata cike da matsananciyar kauna da kulawa. Ana haka Dina da wasu daga cikin kannen Amiru suka shigo, don haka dakin ya yi albarka, ba masaka tsinke, wanda ke nuni da lallai Amiru dan dangi ne. Kowa na fadin albarkacin bakinshi. Akan yanayin jikin Amirun. Ba su bar asibitin ba sai dare, aka barshi da Habibu wanda shi yake kwana da shi. *** 8/5/21, 3:11 PM - Kawata:
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66