Chapter 37
Chapter 37
Ta karbi 'Soyayyah' a hankali zata rikide ta zama 'Kauna'. To gashi soyayyar ma zata tafi ta barta da tsammanin warabbukanta wanda bata fata…….… Koda ta iso airport din ko kulle motar ba ta yi ba, a jikin motar ta bar mukullin. Da gudu ta sheka cikin reception tana dube-dube, babu Amiru, babu ko mai kama da AMIRU. Ta karasa terminal bayan ta hankade ma'aikacin da ke kokarin hanata shiga. Dai-dai sanda aka rufe kofar jirgin (Lufthansa), wanda zai tashi zuwa kasarmu mai dumbin albarka. Ba da jimawa ba kuma ya soma ruguginsa mai gigitarwa bisa kwaltarshi. Kafin ya dai-daita sosai, a sararin samaniya. Mairo ta durkushe a nan tana kuka, kukan da ta dade batayi irinsa ba tun bayan rashin BABANTA da INNAR TA. Fita yake tun daga karkashin zuciyarta. Amiru ya tafi tareda dukkan farin cikin da ta samu cikin Michigan wanda Habibu ya dade kafin ya assasa. Bai shigo rayuwarta da sauki ba ashe! Ashe ya shigo ne don ya rusa komai . Ya tafiyar da sauran karfin zuciyarta. Ya dawo da rayuwa unbearable kamar Uncle Junaidun? Meyasa ita ba ta da sa’a ko kankani a soyayya ???. Ji ta yi kamar an tsugunna a gabanta, kamin ta dago kuma, an kai hannu a hankali an dafa kafadarta. Don haka ta dago idanunta jage-jage da hawaye... don ganin ko wane ne wannan??? Masha Allahu La Kuwwata Illa Billah! Mu biyo Mairo da Amiru da Junaidunta a littafi na uku. Kafin nan ina sauraron ra'ayoyinku kan jaruman namu, AMIRUN ko JUNAIDUN??? Maman SAFAH da MARWA ce. 07030137870 8/3/21, 12:25 PM - Kawata: 444 Ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wane ne wannan? Da haka kawai zai zo ya dafata? Ko ta ce da wani tana neman taimako ne? Wa za ta gani? Yaya Habibu ne! Cikin matsanancin mamaki ya ce, "Mairo?" Ba ta amsa ba, illa ta bi shi da kallo, da jajayen, idanunta. Ya sake cewa "Me ya kawo ki nan? Ina za ki je?" Nan ma shiru ta yi masa, sai kallonsa ta ke kamar ta rufe shi da duka don haushi. Ya ishe ta da tambaya, ya barta ta ji da kukan zuci, da takaicin da ya dame ta. Don ji take kamar Amiru ya bula mata kura, ya ja motar rayuwarshi, ya barta. A nashi bangaren, shima Habibun, haushi ne ya kama shi, ya ce "Kina ji ina magana kin yi kunnen uwar shegu da ni? Na ce me ya kawo ki nan, kuma gurin wa kika zo? Ina zaki je?" Nan ma shiru ta yi masa, kamar da dutse yake magana, kuma ba ta dauke idanunta daga kanshi ba. Ta kafe shi dasu kurrrrr! Kamar shi ne ya kori Amirun. Iyakar fusata Habibu ya fusata, ya fizgi hannunta suka fito harabar adana motoci na airport din, yana baza ido don gano inda ta yi fakin. Daga can ya hango motar ta yi mata wani banzan fakin a inda aka rubuta no parking, Security ne cikin fararen kayan ma'ikatan gurin tsaye jikin motar, wato sun kamata. Ya yi tsaki, tsut…, suka doshi wajen, har yanzu yana rike da hannunta, sai janta yake kamar kayan wanki. Ya mika hannu ya zare makullin ya soma ba su hakuri ya nuna musu Mairo ya ce ga dukkan alamu ba cikin nutsuwarta ta ke ba, su yi mishi uzuri su ba shi motar. Abinka da malam bature da bai san cin hanci da rashawa ba, gami da bin ka'ida da dokar duk da aka shimfida masa, kememe sun ki yarda, sun dage dole su dangana da ofishinsu in har suna son motar su, don a ka'ida mai matsala a kwakwalwa, ba a yarda ya tuka abin hawa ba, ya ce lafiyarta kalau, tension ne kawai, suka ce idan haka ne ke nan tana sane ta karya musu doka? Don haka dole su dangana da ofishinsu, amma ba zasu bada motar ba. Cikin matsanancin fushi, Habibu ya dubi Mairo "Kin kyauta, kin ga abin da kika jawo min ko? Yau shekaruna goma cur cikin kasar America, ban taba zuwa ofishin 'yan sanda ba, don haka sai ki bi su ku je, ki yi musu bayanin dalilinki na karya dokarsu, tunda ni kin yi min banza, sai ki je ku karata.......” Ya cika hannunta zai tafi, ta riko bayan rigarsa tana kuka. Ya ce "Wallahi bazan je ofishin 'yan sanda ba, sai dai ki hakura da motar, ki bar musu mu tafi, kuma wallahi-wallahi ba zan sake siyan wata ba". Ta ce ta yarda, don haka suka bar motar a nan, suka nufi motar Habibun. Allah Sarki, dan uwa rabin jiki! Sun yi nisa sosai danja ta tsaida su, ya saci kallon Mairo da ke kujerar gefensa, ya ga har yanzu kuka ta ke mara sauti, ta rufe fuska da mayafinta. Sai ya hadiye fushinsa, ya soma lallashinta cikin dabara. "Ni dai idan don na tambaye ki inda za ki ne kike min wannan kukan, to ki yi hakuri. Mantawa na yi, ashe fa Amiru ya fada min ba kya son tambaya. Ban da abinki Mairo, idan wajen Junaid kike son zuwa, jirgi ya tashi ya barki, ai sai ki fada mini, na yi miki booking din wani, amma ba ki sunkuya cikin dubban mutane kina rafka kuka ba, kamar wata mai tabin hankali. Yana ina Junaid din? Nigeria ko Russia?" Cikin kuka ta ce "Ni fa tunda na yi maka wancan alkawarin, ban sake tuna zancen Uncle Junaid ba". Ya ce "To ina za ki? Ko AMIRU kika biyo?" Hantar cikinta ta karta, ta rasa me zata ce masa, don haka ta ja bakinta ta yi shiru. Habibu ya kuta ya ce "Hakan da kike yi, kina ganin mutumci za ki sayawa kanki? Shi wancan bai ce yana sonki ba, sabida neman gindin zama kika kwashi jiki kika je gidansu don rashin hankali da rashin mafadi. Shi wannan da ya ce yana sonki, kin ce ba kya sonshi, sabida kar ki ci amanar wanda bai ce yana sonki ba. Ya hakura ya bar miki kasar ma baki daya ba garin ba. To uban me kika biyo shi ki mishi? Da kin same shin me za ki ce masa? Yi hakuri na tuba, ka zo ka aure ni ko me? To ni bana son rashin hankali da rashin mutunta kai, aikin zubar da kima, da wulakanta kai. Kin riga kin ce ba kya sonshi, to a barshi a hakan. Allah Ya kawo miki wanda kike so. Don wanda ya ce ba ya sonka tun farko, daga baya ya dawo ya ce yana sonka, to akwai dalilinshi na yin hakan. Wato za ki yi A RASHIN UWA... akan yi UWAR DAKI...? To ba da abokina ba! Idan auren kike so ki yi, ki je ki nemo Junaidun, tunda ba kya son karatun da nake sonki da shi. Abu na dan lokaci kalilan, ba zaki maida hankali akai ba, mazan nan da kike gani, dukkansu matsala ne, shi kansa auren idan ba a tsaya anyi shi cikin nutsuwa ba, babu inda ya ke zuwa. Don haka yarinya, kama kanki. Wayar ma daga yau ba zaki sake rikewa ba, kamar yadda babu ke babu tukin mota. To kin ji". Dai-dai lokacin da ya yi fakin a harabar gidansu, ya juya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66