Chapter 54
Chapter 54
shi ba. Babu wannan murmushin, babu wannan soyayyar tashi mai kidimata. Kullum daga fada sai hantara. Duk ta bi ta kare a tsaye, ta soma samun tangarda a karatunta. Amma don zurfin ciki irin nata, ko Dina ba ta taba tunanin fadawa ba. Hajiya ta samu yadda ta ke so, domin ta janye hankalin tilon danta kanta. Duk abin da ta ce da shi dashi ya ke amfani, jikin shi har rawa yake wajen bin umarnin ta, ta himmatu da yi wa surukarta karfar baka, mai wuyar magani, wadda ta fi kiyayyar zahiri lahani a zuciyar wanda ake mawa. Duk yadda ya so ya lallame ta su koma asibiti a yi mata aikin amma Mairon ta ki. Idan ya takura mata da nacin maganar sai ta sa kuka. Ga shi shi kuma ba abin da ya tsana irin kukanta da ke soya zuciyarshi. Ta dage akan cewa, ita Allah ne kawai bai nufe ta da samun cikin ba. Ranar da ya nufa Ya ga damar ba ta zata samu ne. "Amma Shi Ya ce 'tashi in taimake ka. Sannan babu cutar da Ya saukar ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta ba. Idan ke ba ki damu ba, ni ina son ganin dan kaina. Tun da rayuwar ba jiranmu ta ke ba, mu muke jiranta". Tana so ta yi tsaki, amma kimarshi da martabarshi sun wuce hakan a idanunta. Dole ta maida tsakinta. "Ni fa babu inda zan je". Duk inda ranshi yake idan ya yi dubu, to ya baci. Ba ta taba yi mishi musu a rayuwarshi irin na wannan lokacin ba. Ya rasa abin da zai mata YA HUCE... Gaba daya ya soma tunanin bokon da ya barta tana yi ne ya sanya ta raina shi... Wannan ne karo na farko da ya kai kararta wajen Habibu tun bayan aurensu. Habibun ya ce, ya kawo mishi ita. Daga ita sai Yaya Habibun a babban falonshi, don Amirun da ya kawota bai zauna ba ya wuce ofis wajen Daddy. Dina na kicin tana kacaniyar shirya abinci. Habibu ya ce "Mairo me nake ji haka? Wai mijinki bai isa ya sa ki abu ki yi ba? Idan ke ba kya son 'ya'yan, to shi yana so. Muma muna so, me kike nufi da ba zaki yarda a yi miki aikin ba?" Ta fashe da kuka, ta ce "Da da ne ya ce na yi abin da yake so, ai zan yi ne, ba tare da kowa ya ji ba. Amma ni ma yanzu ban san me yake nufi da ni ba. Babu magana mai dadi tsakanina da shi sai hantara. Kuma yadda ya ke nunawa kamar ta karfi yake so na haifo mishi dan, sannan ni gaskiya tsoro nake ji, lafiyata kalau inje a jagwalgwala min mahaifa". Habibu ya ce "Likitoci ba za su yi miki karya ba Mairo. Maganar canzawarshi sai ki yi mishi uzuri, yanayin rayuwar kenan, wata rana a sha zuma, watarana a sha madaci! Ba kullum ne mutum yake kasancewa cikin dadin rai ba!". Da kyar Habibun ya rarrashe ta, ta yarda za su je ayi aikin. Ranar litinin Dr. Ma'u ta yi mata aikin. *** Tsawon shekara guda har da doriya, babu wani bayani, wato ba abin da ya sauya bayan yin aikin. Babu ciki ba alamarsa. Dai-dai lokacin da ta kammala rubutun 'project' dinta na kwalin master, sabida kwazon da ta nuna kai tsaye suka ba ta gurbin zama daya daga cikin malamansu, wato 'lecturing' a jami'ar Abuja. Mairo ta debi kudi masu yawa, ta dankawa Yaya Habibu aka soma ginin makarantar firamare da sakandire a kauyen Gurin-Gawa. Sannan ta dauki sauran gaba daya ta mallaka mishi halak-malak, bayan ta warewa Baffa nashi kason. Habibu ya saida gidanshi na kasar America da wasu manyan kadarorinsa ya tada kafadar (Habib Bank) wanda ke gaf da durkushewa. Cikin taimakon Allah sai al'amuran suka soma dai-daita. Amma a ranshi ya dai karbi kudin Mairo ne kawai bai ce mata komi ba, sai dai cikin ranshi ya kudurce juya mata zai yi. *** Hanan Abdulwahab, diyar kanin Hajiya ce, wato Uncle din Amiru da ke garin Gaya. 'Yar kimanin shekaru ashirin da hudu, kyakkyawa ce matuka, kuma tana da irin tsagin su Amiru a gefen hagu da dama na fuskarsu. 'Yan asalin garin Gaya ne su ma, don da Babanta da Hajiya ubansu daya. Mahaifinta tsohon soja ne, wanda ya rike manya-manyan mukamai a aikin soji, har zuwa matsayin da yake kai a yau, wato Major Genaral Abdulwahab Gaya. Gaba dayan karatun Hanan tun daga firamare har jami'a ta yi shi ne a garin Lagos, inda mahaifinsu ya yi aiki a wancan lokacin. Daga baya da ya yi 'retire' suka dawo garin Kaduna da zama, inda suke zaune a halin yanzu. Direban Hajiya Mr. Kademi ne ya je ya dauko Hanan daga filin jirgi, wadda ta sauka karfe hudu dai-dai na yammacin ranar ta Laraba. Hajiya ta yi mata kyakkyawar tarba bayan ta rungumeta tana lale da diyarta. Kamar yadda Hajiyar ta nemi izinin mahaifin Hanan di n kan ya barta ta zo ta yi mata kwana biyu. Sun baje a falon Hajiya suna labari, Hanan ta ce. "Ina labarin brother, yanzu yaran shi nawa ne Hajiya?" Hajiya ta kyabe baki, ta ce. "Babu ko daya". Hanan ta yi murmushi, ta ce. "To ai kin san Turawa ne, watakila ba su shirya fara tarbar 'ya'yan ba". Cikin rashin walwala Hajiyar ta ce. "Ke raba ni da abin haushi, kada ke ma ki bata min rai yanzun nan. Turancin yaci abu kazan ubansa. Ba wani tsarin iyali, juya kawai ya je ya auro". Kwanan Hanan biyu a gidan, amma ba su hadu da Amiru ba, sabida sanda yake shigowa gaida Hajiyar da safe ita ba ta tashi daga barci ba, sabida dai Hanan 'yar hutu ce ta karshe. A rana ta uku ne da ya shigo Hajiya ta je har dakin da ta sauka wanda ya kasance dakin su Rayyah ne kamin su yi aure, ta tasota ta ce ta zo su gaisa da Yayanta. Ta ba ta wani farin kwalli ta ce, ta zizara a idonta, ta yi duk kokarin da zata yi ta tabbatar sun hada ido. Hanan ta cika da mamakin mene ne dalilin Hajiya na yin hakan? Sai dai kuma ba ta jin zata iya kin bin umarnin Hajiyar. Tsaye ya ke a baranda yana amsa kiran Habib cikin wayarshi, a lokacin da Hanan ta fito falon. Ya juya baya hannunshi daya dafe a bayanshi, yayin da ya yi amfani da dayan wajen rike wayar. Hanan ta tsura mishi idanu, wani al'amari mai karfi na fizgarta. Rabonta da Amiru tun wani zuwa da ya yi Kaduna gaida mahaifinta a lokacin yana Washington. Zuwa yanzu ya kara girma da haiba. Duk wasu kamanni na ingarman namiji ya mallake su, kuma kyakkyawa na karshen-karshe. Ya zama 'giant' mai wani irin kyawun halitta na burgewa da ban mamaki. Irin mazan da ba kowacce lafiyayyar mace ce zata iya dauke ido a kansu ba. Gwiyoyinta suka yi sanyi, kuzarin jikinta ya kare, wata irin soyayyar Amirun na tsirga zuciyarta. Ba ta iya ta dauke ido a bayanshi ba har ya juyo. Da farko kallo daya ya yi mata, amma ya rasa dalilin da ya sanya ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66