Chapter 29
Chapter 29
Ya ce "Eh ita ce Aunty Mairo". Ya matso jikin Mairo ya jingina da kafadunta, ita kuma sai kokarin daukar takwararta ta ke, amma ta ki, ta like jikin babanta. Ya ce "Ai ita kiwar tsiya gare ta, wanda yake kulaki ba ki kula shi ba". Ta yi murmushi ta ce "Abbana, Muhammad". Ya yi murmushi ya ce "Anti Mairo za ki je gidanmu?" Ta ce "Insha Allahu". "Za ki yi min tatsuniyya ta gizo da koki irin wadda Daddy ke mana?" Ta ce "A'ah, ni ban iya tatsuniya ba, ni sai dai na karanta maka labarin jaruman maza, irin su Ilya dan mai karfi, da Malukussaif Ibn Ziyyazanun". Ya yi dariya ya ce "Ni kuma zan tuka ki a jirgina (helcopter) wanda Daddy ya sayo min". Ta rungume shi ta ce "To Abbana". Baffa ya ce "Amma Habibu na yi mamaki da ka iya yin wadannan shekarun ba ka waiwayi gida ba, ko gaisuwa ce ai ka aiko mana, idan ba ka zo ba (a lokacin ba kowa ke da wayar hannu ba, sai wane da wane)". Habibu ya ce "Kuskuren da na yi ke nan, amma kusan kullum ba a rasa masu zuwa Najeriya daga Malaysia. To sai dai ita kanta Maleshiyar na dade da barinta, tun bayan da na kammala karatun digirina na farko. Dina abokiyar karatuna ce, diyar Ambassadan Nijeriya a kasar Maleshiya. Mun dade muna soyayya, mahaifinta ya so mu dawo gida ayi auren gaban iyayena, na nuna masa ni ba yanzu zan koma gida ba, ina da babban uzurin da ya rabo ni da gida, idan na koma mawuyaci ne Babana ya barni na dawo. Don haka ya tsaya tsayin daka har muka yi aure. Da taimakon mahaifinta na samu aiki na wucin gadi (temporary) ina yi a wani kamfanin kera takalman fata. Na dade ina aiki a nan kuma na samu alheri yadda ba kwa zato. Daga baya wani abokina Amiru da taimakon mahaifinsa ya yi min hanyar da na samu gurbin karo karatu a Michigan din Amurka, akan kwamfuta da duk abin da ya shafe ta. Ina gamawa ba da jimawa ba na samu aiki a Bankin Barclays reshen kasar Amurka, don haka muka koma can. A can aka haifi Alhaji da Mairo, Muhd ne kadai aka haifa a Kuala-Lampur (Malaysia). To kun ji, don haka bazan dade ba, don wajen aikina suna bukatana, ina so zan tafi da Mairo". Mairo ta yi azamar dago kai ta dube shi, da gaske ya ke ko wasa ya ke? Babu alamun wasa ko kankani a fuskar Habibun. Shi kuma ya kafa mata ido cike da tsoron, kada ta ce ba zata zauna da shi ba. Shi kam nan duniya bai ga abin da zai sake raba shi da 'yar uwarshi ba, wadda ta rage mishi kwal a duniya. Baffa ya ce, "Anya a yi haka? Ni dai na fi so inyi mata aure, hankalina zai fi kwanciya. In lissafina dai-dai ne shekarunta goma sha takwas cif, aure shi ne ya dace da ita". Cikin murmushi Habibu ya ce "Ta fitar da mijin ne?" Ya fadi yana kallon Mairon, ta yi hamzarin sunkuyar da kanta. Baffa ya ce, "A'ah, ita ko zancen nan da samari irin na su Ladidi ba ta yi, idan ka ganta ta fita, to muhimmin abu ne ya fitar da ita. Amma akwai wani abokina Alh. Salisu da ya yi min maganarta tun wancan watan na ce ya dakace ni sai na yi shawara da ita tukunna". Habibu ya ce "Har nawa Mairon ta ke? Ka yi hakuri Baffa ka ba ni ita makaranta zan sa ta, idan ta soma ko ba ta kare ba idan mijin ya fito sai a yi auren, amma Alh. Salisu ai ya yi mata tsufa". Baffa ya ce "Ni ma abin da na yi la'akari dashi kenan, shi yasa ban baiwa zancen wani muhimmanci ba, sai ka yi mata fasfo ku tafi, Allah Ya sa hakan shi ne alkhairinta". Habibu ya ce "Amin". Ya dubi Mairo ya ga ta sunkuyar da kai, ba ta dago ba ya ce "Mairo ko ba kya son zama da ni da 'ya'yanki?" Ta yi murmushi ta ce "Mamarsu zata yarda?" Shi ma ya tayata murmushin, ya ce "Kada ki damu. Dina mace ce mai fahimta, ga kirki da hankali. Na yi mata kyakkyawar shaida. Ta sanki, ta san labarinki ba tun yau ba. Ta fi ni damuwa da a dauko ki, ina gaya mata akwai lokacin da nake jiran isowarsa ga shi Allah Ya kawo". Baffa ya ce "Ita tana ina?" Ya ce "Tana garin Dutsinma, can home town dinsu, gobe insha Allah zan je na dauko ta". Rahma diyar Hajara ta shigo da kular abinci da farantai ta aje ta fita, Mairo ta matso ta zubawa Habibu, ya karba yana cewa, "Yaushe rabona da cin dan wake?" Baffa ya yi dariya ya ce "Ai ga Mairo nan sai ta dinga yi maka dan wake, idan matarka ba ta iya ba". Ya ce, "Tana yi min na fulawa (gudun kurna), amma ba irin shi nake so ba, wannan da ake yi da rogo da kuka shi na fi so, don ya fi sulbi, yafi saukin wucewa a makogaro". Mairo ta zuba filet daya da yaran ta ja su suna ci, Baffa na bai wa Habibu labarin bayan rabo. Habibu ya kammala ya ajiye farantin, ya tsiyayi ruwa a jug ya sha, ya ce "Na zo da ma'aikata Baffa, gobe insha Allahu za a rushe gidannan a yi ginin zamani yadda su Inna Habiba da sauran yara za su fi sakewa". Baffa ya yi murmushi ya ce "Allah Ya ba da iko Habibu". Ya juya ga Mairo ya ce "Je ki share min dakina na zaure, anan zan sauka zuwa gobe, yaran ki kwana da su, ni zan shiga cikin gari wajen tsoffin aminai, gobe idan Allah Ya kaimu sai mu je can immigration maganar fasfo". Ta ce "Ita kuma Anti Dinan a ina zata sauka idan ta zo?" Ya ce "Tana da inda ya fi nan ne? Duk nan zamu sauka". Ta tasa yaran a gaba suka nufi cikin gida. Habiba da Hajara dai duk kunyar Habibu ta ishe su, sakamakon rashin arzikin da suka san suna yi wa Mairo. Ba su taba zaton Habibu zai dawo ba, ga wata irin galleliyar mota da ya iso da ita mai nuni da lallai Habibu ya kama kasa, ga 'ya'ya firda-firda kamar 'ya'yan kajin gidan gona, da gani babu tambaya iyayensu sun gama samun nasibin rayuwa. Habiba ta karbi 'yar daga hannun Mairo, ta sa zani ta goyata, ta ce da Mairo "Ladidi har yanzu shiru, ina kika barota ne?" Ta ce "Tana can asibitin ta ce zata dan jima". Baffa ya fita ya dawo da gyararrun kaji guda goma, ya ce a yi wa Habibu girki. Mairo ta je ta share dakin Habibun da ke soro, ta kunna turaren wuta ta gyare ko'ina. Ta shigar da kayan Habibun, bayan ta ware kayan yaran. Daga Hajara har Habiba sun shiga hankalinsu musamman ganin yadda ake sauke buhunhunan shinkafa, katon-katon na taliya, garewanin mai, katon na juices, na gwangwani da na kwali, buhunan sugar, doya, dankali da sauransu, duk aka jibge musu a store. Ladidi ba ta dawo gidan ba sai dare,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66