Skip to content

Chapter 22

Chapter 22

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

"Innar ma na rasata Nabilah ... Ba ni da kowa a yanzu sai Baffana sai Allah da Ya halicce ni. Na zama marainiya Nabilah, ba uwa ba uba…...."Hawaye suka kece mata, ta dukar da kanta cikin cinyoyinta ta ci gaba da kuka. Nabilah ma sai ta sa kuka, tana tuna Inna da kirkin da ta yi mata. Sun dauki mintuna suna kuka, kamar wasu kananan yara. Ba su san yaushe Uncle ya shigo ba, har ya tsaya a kansu. Ya sanya hannu ya kwankwasa desk din da suke sunkuye. Duk hirarrakin da suke yi ya ji su, ya rasa inda zai sa kansa da tausayin Mairo. Ba kankanin abu ne ke sanya Junaidu kuka ba, amma a yau ya ce Maryama I cannot control my tears……….."Suka dago ido suka dube shi cikin ido, Mairo da Junaid ke kallon juna, irin kallon da ba su taba yi a rayuwarsu ba. Wani muhimmin al'amari na samun muhalli cikin kwayar idanunsu. Nabilah sai ta bude baki, galala! Tana kallonsu, tana cewa cikin ranta "A yau dai, dole Mairo ta yarda Uncle Junaid yana sonta……..". Mairo kwana ta yi ba ta yi barci ba, baya ga dacin mutuwar iyayenta da ya dawo mata sabo fil, sai kuma SOYAYYAR Junaid da ke dawainiyya da zuciyarta, amma ta kasa ganewa, sabida kuruciya da wauta. Ga dai zahiri al'amarin ya sauya, amma ta sanya kafa tana takewa da gan-gan. A ganinta mai Junaid zai ci da 'yar kauye kamarta? Sai dai ta ce zuciyarta na yaudararta, tunda shi din bai furta ba. To ita ma ba zata taba yarda da tunaninta ba. Shirye-shiryen jarrabawar fita ya kankama. A wannan dan tsukin Uncle ya takura musu matuka da karatu, musamman akan lissafi (mathematics) da Ingilishi (English). Burinsa kawai Mairo ta lashe dukkan takardunta. Ta gama makaranta with flying colours', ta samu gurbi a babbar makaranta, ta yi karatun da zata dogara da kanta cikin kowanne hali. Idan hakan ta faru to shi kam Alhamdu lillahi... Ya sauke nauyin alkawarin da ya daukar wa Malam Bedi, sannan ne yake jin zai fallasa mata soyayyar shi, don haka wannan ba lokaci ne da ya dace ya fallasa asirtacciyar soyayyarsa ga Mairo ba. Ya manta masu iya magana sun ce "A BARI YA HUCE... Shi ke kawo da rabon wani. Ba ta da abin da zata ce da Uncle Junaidu sai godiya, domin da taimakonshi da kwarin gwiwar da ta ke samu daga gare shi ne ta zana jarrabawar Jamb, Waec da Neco cikin kwanciyar hankali, tamkar ba jarrabawa ta zana ba, sabida yadda komi ya zo mata da sauki. Sai dai kuma wannan gama jarrabawar na nufin al'amura da dama cikin rayuwarta. Rabuwa da UNCLE JUNAIDU? Wani muhimmin al'amari ne da ke cinta a zuci, da zuciyar ba zata iya jurewa ba, da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Ina ma Uncle zai ce yana sonta ya aure ta? Ya rabata da rayuwar maraicin da zata je ta fada a gidan Baffanta? Hawaye suka ciko idanunta. A karo na farko da zuciyarta ta kawo shawarar ta nemi Uncle ta roke shi ya aureta, ya tserar da ita daga rayuwar kunci da zata je ta fada, ko da ba ya sonta. Ta shiga neman Uncle cikin makaranta, lungu-lungu, sako-sako, abun kamar wasa ko mai kama da Uncle babu. Tuni dalibai sun soma tafiya, don duk wacce ta fito daga last paper daukar kayanta ta ke ta tafi, bayan anyi sallama da kawaye da abokan arziki. Tana tsaye nan cikin tashin hankali Nabilah ta iskota, "Ga can Baffanki ya zo daukarki yana ta aike a nemo mishi ke". Hankalinta ya kara tashi da ta tabbatar a yau zata tafi ne, tafiya ta har abada daga Minjibir, ba tare da ta yi sallama da Uncle ba, wani mutum daga cikin mutane biyu da ke ba ta farin ciki da buri (hope) a cikin rayuwarta. Tabbas yau ya sauke nauyin alkawarin da ya yiwa mahaifinta. Ta kammala makaranta cike da kyakkyawan zaton samun nasara. Muhimmin al'amarin da ke dawainiya da zuciyarta akan Uncle, ta ke so ta sauke, amma babu Uncle a cikin Minjibir, babu alamarsa. Sai ta sa fuskarta cikin tafukanta ta soma shesshekar kuka. Nabilah ta rungume ta suka ci gaba da kukan tare, sai dai ita Nabilah ba ta san hakikanin dalilin kukan Mairo ba. Ita kuka ta ke na kewa da rabuwa da Maironta, yayin da Mairo ke kuka na tausayawa rayuwarta. Ta kullaci Uncle mummunar kullata, (irin kullatar data yiwa Habibu) ta tuhume shi da YAUDARA da wasa da rayuwarta. Ba tasan inda za ta ganshi ba, ta gaya mishi shi kadai zuciya da ruhinta ke so. Ya taimake ta ya aure ta koda BA YA SONTA. Shi kadai ne namijin da ta ke jin zata iya aure a rayuwarta. Shi kadai ne ta ke jin zai kula da rayuwarta a bayan idon Baba da Inna. Shi kadai ne ta ke kalla ta ji shi kamar Yaya Habibu. Yau shekaru dai-dai har shidda dai-dai da rana daya zuciyarta ba ta taba hutawa da kaunarshi ba. A da kam ba ta gane ba, amma yanzu ta yarda ta amince da mahaukaciyar soyayyar da ta ke yi wa Uncle Junaidu. A yau da ta yanke shawarar fada masa don su tallafi rayuwar juna ta neme shi ta rasa. ***** K arfe hudu dai-dai na yammacin ranar ta litinin suka iso gida, inda direban su Nabilah da ke biye da su don ya ga gidan ya juya da Nabilah, da alkawarin bayan sati zata zo su je da Mairo gidansu, don ba ta taba zuwa ba. Tun daga soro Mairo ta soma cin karo da kwanuka, da busasshiyar miyar kuka a jiki. Gabanta ya ci gaba da faduwa don ta tabbatar ita da rayuwar farin ciki, sun yi hannun riga ke nan. Ta fado cikin wata sabuwar rayuwa ta MARAICI, wadda Innarta ta ke jiye mata. Ta tabbata Inna tasan rashin kirki na matan Alhaji Abbas shi yasa a lokacin rayuwarta ta ki yarda ta zauna da su. Mai za a yi da hali irin na Hajara da Habiba? Sai Allah Ya kyauta. Karatu dai an kare shi, yanzu zama ne za a yi na din-din-din. Kowacce waina za a toya? To bari mu bi Mairo da iyayen rikon nata mu gani. Habiba na daki lokacin da suka shiga, sai Hajara ce a tsakar gida tana tankaden garin tuwo. Baffa ne a gaba rike da jakar mairo, ita kuma ta biyo bayansa rike da wata jakar. Hajara ta amsa musu sallama fuskarta ba yabo ba fallasa. Bayan haka ba ta kara tofawa ba. Baffa cike da takaici ya ce "Hajara baki ga 'yar taki ba ne, ko sannu da zuwa babu? Ai ba a haka". Ta cira kai ta jefe shi da harara, "Cewa za ka yi tashi ki yi tsalle 'yar gaban goshina ta dawo, ba sannu da zuwa ba". Jin cece-kucensu sai Habiba ta leko. Ita kam tayi fara'a ta ce "Ah! 'Yan makaranta an dawo? Lale-lale". Ko ba komai ta samu jakar da zata yi ta yi mata bauta. A dakinsu ta cimma Ladidi ta yi dai-dai sai sharar barci ta ke, dakin kaca-kaca ko'ina kayan Ladidi ne a watse, nan pant, can brazier dukun-dukun da su. Ba ta

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66