Skip to content

Chapter 46

Chapter 46

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

bazata iya yi masa wannan bayanin ba. Sako riko ta yayi da karfin da yafi na dazu, ya juyo ta sannan ya sa hannu ya dago habarta. Yana iya ganin kyallin dake cikin idanunta wadanda ke cike taf! Da soyayyar data mamaye su. Soyayya mai cike da kauna mara algus or material attachement. Zaiyi rantsuwa bai taba ganin wannan yanayin cikin kwayar idanunta ba, wani yanayi da yake matukar jira, yake kuma da yakinin zai iya cigaba da jiran zuwansa cikin idanun Mairo har nan gaba da shekaru goma kafin ya yarda ya hada shimfida da ita. "To yanzu fa? Mairo! Mairo yanzun kina sona?" Amiru ya tambaya, da wata murya tamkar ba tashi ba. Sai ta yi murmushi, irin wanda bai taba gani bisa siraran labbanta ba. Wannan kadai ya tabbatar mishi da cewa, ya gama mallakar soyayyar Mairon, saura da me? A take shi ma ya soma mallaka mata ta shi. Cikin wani irin salo mai ban mamaki da Mairo ba ta taba tunanin akwai irin wannan soyayyar a duniya ba. Koda a duniyar karance-karancen novels dinta kuwa. Su Hajiya Mairo, tun ana dauriya, ana cijewa, cikin bin shawarwarin uwardakin ta Dina, har lissafin ya soma kwace mata......aka kai ga gejin kiran Anti Dinah, Baffa, da Yaya Habibu su zo su kawo taimako. Yau har Ladidi da Nabilah sun sha kira don tana ganin karshen rayuwarta yazo! Shi kanshi Amirun ya rasa control din kansa, ta yadda har zai yi tunanin cewa Mairon virgin ce, ba kamar matarshi ba. Tunda yake a rayuwarsa bai san akwai Hurul-eeni tun a duniya ba. Bai san aure iri-iri ne kuma suna ya tara ba. Don haka bai farga da aika-aikar da ya yi ba, sai da ya duba ya ga Mairon ta sume mishi. Ba ita ta dawo hayyacinta ba sai da sanyin ruwan 'ragolis' ya ratsa kwanyarta, da sauran sassan jikinta. Ya rungume ta sosai, tamkar ya tsaga kirjinsa ya sanyata, cikin shauki ya ce "Mairo kar ki gudu ki barni! Mairo ki ci gaba da zama da ni ko ba kya sona, ni ina sonki da dukkan ruhi na! Ki rike naki son ko bazaki bani ba! Zan zamo ‘impotent' a duk ranar da kika guje ni, ko kika juya min baya...!" *** MAIRO A GIDAN AURENTA! Zuwa yanzu, wato watanni biyu a gaba, Mairo an zama manyan mata, an iya komai na kula da miji. Ta iya daukewa mijinta lalurar da mata hudu ba zasu iya dauke masa ba. Soyayya, kauna da shakuwa ke kara kamari tsakaninta da mijinta. Ga kauna da kulawa da ta ke samu daga surukanta kamar su suka tsugunna suka haife ta. Cikin wannan dan tsukin Amirun ba ya samun zama sosai, sabida shirye-shiryen bude bankinsu da suke yi shi da Habibu. Shi Habibun ke tafiyar musu da komi ta can, shi kuma yake tafiyar da komi ta nan. Gaba daya ya mance da wata Harrit da ya sanya lambarta a (divert call), sannan a ka'idarshi bai daukar wayar da bai san lambar ba. Al'amuran gabanshi kadai sun ishe shi, sannan Mairon shi kadai ya sanya a gaba, a yadda yake ji cikin ransa, ta ishe shi rayuwar duniya da lahira. A wannan daren na ranar talata shiri yake don tashi zuwa Washington a washegari, domin mika takardar yin retire daga aiki a World Bank, a gefe guda kuma ga Mairo ta dira shagwaba ita dai sai ya tafi da ita ta ga Yaya Habibu da Dina. Ya kamo hannunta ya ce "rigimarki yawa gare ta Mairo, na fada miki Washington za ni ba Michigan ba. Kuma ba dadewa zan yi ba, karkari na yi sati biyu. Ina duba yiwuwar komawarki makaranta, idan komi ya dai-daita gidan Habibun zan barki ki zauna gaba daya". Ai da jin haka ta yi tsalle ta dane shi cikin nuna farin cikinta a fili. Inda shi kuma ya juyo ta gareshi ya bi ta da deep-kisses tsakiyar bakinta, wuyanta, da idanunta; mai nuni da cewa, lallai zai yi kewarta. Ita da Sabah suka yi mishi rakiya filin jirgi a asubahin washegari. A gaban Sabah ya rungume ta yana fada mata wasu irin kalamai masu rikirkita kwakwalwa cikin kunnuwanta. Sabah sai ta sa mayafinta ta kare fuskarta tana murmushi. A zuciyarta kuwa addu'a ta ke, Allah Ya ba ta miji irin Yayanta. Yana sauka a Washington ya tarar tuni Raymond da Franklyn suna jiran isowarshi, don haka suka zubo jakarshi a bayan mota suka nufo cikin gari. Kai tsaye gidanshi suka nufa suna tafe suna yi mishi bayanin muhimman abubuwan da suka gabatar (in his absence), ci gaban da aka samu da shortcomings din duk da ya biyo baya. Suna sanyo hancin motarsu a farfajiyar gidan ya ga bakuwar mota kirar (Ferrari 458) kusa da ta Harrit. Bai kawo komi a ranshi ba, don ya yi zaton baki ne Harrit din ta yi kasancewarta ma'abociyar hulda da jama'a, don haka ya yi amfani da mukullinshi ya bude kofar. Su Raymond suna daga waje suna magana. Ya ratsa falon babu kowa, ita ba musulma ba, balle ya yi mata sallama don haka kai tsaye ya sanya kai 'bed-room' dinsu. Idanunshi kuwa suka yi kyakkyawan gani. Harrit ce kwance tare da wani bature dan uwanta haihuwar uwarsu-ubansu cikin halin turmi da tabarya. Ya tsaya kawai yana kallon tashin hankalin da bai taba gani a rayuwarshi ba, wanda a take ya tabbatar ba komi ba ne, hakkin iyaye ne da son zuciya suka jawo mishi (al'ummar musulmi irin Amiru sai a yi hattara, kafiri har gobe kafiri ne, duk soyayyarsa gareka kuwa, kuma babu soyayya ta hakika tsakaninshi da musulmi sai yaudara da soyayyar manufa). Jikinsu ne watakila ya ba su ana kallonsu, su duka suka juyo a razane, amma abinka da nasara da babu digon kunya ko tsoron Allah a tare da shi, sai suma suka zuba mishi idanun. Ya yi saurin dauke idonsa ya fito falon ya barsu a nan. Ya zauna cikin kujera yana fidda wani irin wahalallen numfashi yana fesarwa da kyar, yana shaka da kyar. Idan wani ya fada mishi Harrit zata yi mishi haka ba zai taba yarda ba, ya godewa Allah da bai taba kusantar Harrit ba tare da ya yi amfani da kwaroron-roba ba. A take ya fiddo takarda ya dora biro ya rubuta mata sakin aure kamar yadda addininshi ya tanada. Ya leka waje ya kira Raymond da Franklyn ya ce, ya ba su minti goma su fitar da duk wani abu da ke cikin gidan su loda mata shi a waje. Ya leka dakin ya cilla mata takardar sannan ya kara fadi mata da bakinsa cewa ya sake ta saki uku. Ko babu sakin dama auren ya riga ya gurbata a nashi addinin. Ya kuma sanar da su minti goma suka kara yi mishi cikin gida 'yan sanda ne za su raba shi da su. Harrit sai kuka ta ke tana ba shi hakuri, ta kama kafafunshi ta rike tamau! Jan gashinta (blonde) ya baje a bayanta da fuskarta kamar na mahaukaciya. Tuni kwarton nata ya gudu, ta gaban Amiru ya rarrafa ya wuce da rigarsa a hannu, da ya ga ya iso kofa lafiya sai ya taka da gudu iya karfinsa ko motarshi bai dauka ba. Su Raymond ne ke cika

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66