Chapter 57
Chapter 57
ya sake ki ba. A matsayinmu na musulmi, ma'abota imani da yarda da kaddara, muna da tabbacin cewa, duk abinda ya faru damu da sanin Allah. Shine mai sanya cuta, kuma shine mai yaye ta. Don haka muna da kyakkyawan zaton Zai tashi kafadar Amiru, a lokacinda ya so. Ya cigaba da gudanar da al’amuran kyakkyawar rayuwarshi. Inda rabon zaku komawa auren ku, to da yardar Allah zaku koma. Amir bai yi haka ba Mairo, sai bisa tirsasawa. Ya kamo hannunta ya rike cikin nashi, ya ce. "Mairo mun rasa Baba, mun rasa Inna, amma mun hakura kan ba yadda za mu yi. To haka da muka rasa auren Amiru, zamu yi hobbasar yin tawakkali. Mu ci gaba da jure jarrabawoyin da Ubangiji ke yi mana a rayuwa, har mu cinye jarrabawarmu. Don haka ki yi hakuri kamar yadda na yi hakuri, iyayenshi da 'yan uwanshi suka yi, kan halinda yake ciki. Kuma Alhamdulillahi yana gane mutane yanzu saidai ya ki asibiti. Hajiyar Amiru dasu Nina suna can suna ta nemanki, suna neman inda za su ganki su nemi gafarar ki sun rasa. Ta yi nadama/sunyi nadamar abin da suka yi mana. Yafiyarki su ke nema Mairo. Afuwata suke nema da hawayensu. Sun gurfana kan gwiwoyin su a gabana don na yafe musu. Sannan sun samu Daddy sun bayyana mishi duk abinda suka yi mana, yayi mamaki nima nayi mamaki, ya saba musu sosai kuma sunyi nadama ta gaskiya akan ki Mairo. Yace dasu ai ga sakayya nan sun soma gani tun a duniya, tunda Amirun na neman rasa ransa a kanki. Wallahi Mairo tun bayan tafiyar ki ko kofar gida Amiru bai kara takawa ba, yana gidan ki, daga dakin ki sai falon ki. Hajiya in kin ganta a halin yanzu dole ki tausaya mata, watanta daya a Gaya ya koreta, kiris ya rage ya saketa saida nasa baki tukunna ya hakura. Ta ce ki yi wa Allah ki kula mata da abin da ke cikinki. Sabida na gayawa Daddy kina da ciki shikuma ya gaya musu. Sabida haka ki kwantar da hankalinki, don a samu daidaituwar B.P dinki, don hawan jini hatsari ne ga mai juna biyu, kuma jininki ya hau, don haka ki taimake ni Mairo, kada kema na rasa ki……...bani da Uwa, bani da Uba, sai ke da abinda zaki haifa…." Hawaye sharrr! Suka zubo daga idonsa. Ta kai hannu tana share masa, ita ma nata suna zuba. Cikin rishin kuka ta ce. "Ka daina kuka Yaya Habibu, na yi maka alkawarin zan kwantar da hankalina tunda yana raye". Ya ce, "To tashi ki ci abinci, ko dan cikinki ya samu. Bai kamata ki dinga zama da yunwa ba, plzzz... Mairona!". Ta ce "To ba ni in ci". Ya bude kular da ke gabanta, ya zuba mata faten dankalin Turawa, wanda ya ji tsokar naman kaji ya yi lugub. Ya mika mata a faranti, ya cika tambulan da (fresh milk) mai sanyi ya mika mata. Ta karba ta soma ci sosai har tana taune harshenta sabida yunwa. Dina ta shigo rike da kwandon kayan abinci, suka zauna akan kilishi suna ci ita da Habibu. Mairo na kallonsu tana raya abubuwa a ranta, wato ranar da aka kaita gidan Amiru ya takura mata sai ta ci abinci akan idonsa. Ta kai hannu da sauri ta goge hawayen da suka kara shimfido mata, don ba ta son Yaya Habibu ya gani, ranshi ya baci. Amma ta riga ta san kuka ta dinga yinshi kenan, har karshen rayuwarta. Tunda yanzu itada Amiru sai dai a TUNA BAYA……Yaya zatayi da dimbin soyayyar shi data kankanewa zuciyarta???? An sallami Mairo ranar wata asabar bayan likitocinta sun tabbatar komi nata ya koma dai-dai. A lokacin cikinta ya cika watanni shidda cif, wanda ya yi dai-dai da cikar Amiru watanni hudu yana jinya. Suka dawo gidan su Dina, inda a washegari Habibu da Dina suka yi shirin tahowa gida Najeriya. Gidan ya rage daga Mairon sai Hajiya da masu aiki, don Abban Dina bai cika zama ba sai a weekend, kullum yana ofis. Bata tashi daga inda ta yi sallolin farilla guda biyar, ba tareda ta yiwa Amiru addu'ar neman lafiya daga Ubangiji ba. Hajiyar Dina na kula da ita yadda ya kamata, ko Innarta iyakacin kulawar da zata yi mata kenan. Watan Hajiyar Dutsinma biyu tare da su jikinta ya yi kyau ta koma gida. Kwanaki na mirginawa su zama watanni, har watan Aprilu ya kama, wanda shi ne EDD dinta. Sai dai Mairo ba ta yarda anyi mata ‘scan’ ba. Ranar wata alhamis nakuda ta tashi cikin dare, haihuwa gadan-gadan. Don haka ba da bata lokaci ba Hajiya ta tuka su da kanta suka nufi asibitin da ta ke awo, nan da nan aka karbe ta a (labour ward), nakuda ta tsayin awanni uku cur, kan Hassan ya bullo, kamin likitocin su yi wani yunkuri, shi ma Hussaini ya biyo dan uwansa. Aka turota dakin hutu, Hajiya na rungume da jariran tana yi wa Allah sarkin halitta tazbihi, sabida kamar Amiru ya yi kaki ya tofar. Sannan ‘identical twins’ irin wadanda banbacesu zai yi wuya. Sai dai da alama Hassan kalar Babanshi ne, wato (choculate), yayin da Hussaini ya debo hasken fatar Mairo. A take Hajiya ta yi waya ta sanar da Habibu, ya yi hamdala ya kuma nemi wayar Alh. Abdurrahman ya sanar da shi, don haka a karshen satin suka dungumo har Hajiyar Amiru dasu Sabah suka iso Malaysia. Farin ciki a wajen Hajiya Aisha da Alh. Abdurrahman abin ba’a cewa komi. Hajiya har da kukanta na nadama, ga dai ‘ya’ya ba daya ba har biyu Mairo ta Haifa, duk kunyar Mairon ta isheta, ta kama 'yan jikokin ta rungume tana yi musu addu'a, ji take kamar Amirun ne ta rungume a ranar data haifeshi, sai dai dukkaninsu babu mai ra'ayin a yi wani taro sai addu'a da kowa yake yi wa mahaifinsu, wanda har zuwa lokacin ke kwance cikin halin jinya. Yara sun ci sunan Habib da Amir, babu kuma wanda ya yarda da a sakaya. Ana kiransu da sunansu abinsu. Bayan su Hajiya sun koma Mairo ta ci gaba da rainon 'yan biyunta cikin koshin lafiya da taimakon (Nanny) Bamaleshiya da Hajiya ta daukar mata. Kamin watanni hudu sun cika sun yi kiba, sun yi bul kamar 'yan watanni goma sabida samun kulawa da ruwan nono isasshe. A lokacin ne kuma 'addmission' dinta na yin PhD ya fito a 'university of Malaya'. A satin da zata fara karatu, Yaya Habibu ya zo Malaysia. Yace tayi shiri suje Najeriya ta kaiwa Amiru ‘ya’yan shi ya gansu. Don ya samu sauki har ya soma zuwa ofis. Daddy ya samo mishi aiki a CBN. Don shi Habibun bai yarda su sake yin hadin gwiwar ba kamar yadda Daddy da Amirun suka bukata, yace saboda halin rai. Ya kuma ce da Daddy akwai kudurin da yake dashi a kan bankin nan bada jimawa ba. Amma ba wai don yayi fushi da abinda Hajiya tayi ba. Mairo bata son wannan tafiyar sai don Yaya Habibu ya matsa mata. Amirun ne bata son gani, don bata son duk wani abu da zai taba zuciyar ta a halin yanzu. Ta riga ta sanyawa zuciyarta YAKANAH (sunan littafin Takori mai zuwa). Ta koya mata dangana,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66