Skip to content

Chapter 21

Chapter 21

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

lullube suke da dusar kankara. Room heater da ke aiki a dakin bata taimaka ba ko kankani wajen rage azabtaccen sanyin da ta ke ji ba, wanda idan da sabo, to sun saba. Ta hau kwamfuta don duba emails dinta. Bayan ta yi wa sanyi mugun shiri cikin bakaken coat da bakin wandon jeans mai kauri, hand-socks (safar hannu) da leg-sock (safar kafa) duk bakake wul. Sakonnin suka soma bayyana, inda welcome-screen ke tabbatar mata tana da sabbin sakonni guda goma sha biyar. Ta soma budawa, yawanci duk daga Nabilah suke, tana tambayarta abin da ya samu wayarta ta kasa samunta. Ta mayar mata da amsa cewa, ta yiwa Yaya Habibu laifi ya kwace, sai na Ir’eesh inda ita kuma ta ke sanar da ita cewa akwai test' karfe sha biyu na ranar washegari, wato litinin. Sai na wani dan ajinsu Henry baturen Brussels inda yake sanar da ita ya wuce kasarsu don mamarshi ta rasu. Ta taimaka tayi masa wani assignment, ya neme ta a wayarta bai same ta ba. Ta yi mishi ta'aziyya ta tura, sai wani guda daya da ya yi matukar daukar hankalinta, kasancewar an yi shi ne cikin harshen Hausa, da rubutu in italic, sannan babu sunan wanda ya aiko, sai logo na hular ilmi. Ta soma bin rubutun a gurguje. "Nasarar dan Adam a rayuwa, ana gane ta ne tun daga kuruciyarshi. Mutanen da suka samu kansu cikin gwagwarmayar rayuwa daga yarintarsu zuwa giramansu ba sa karewa haka a banza. Ina da yakinin cewa, kina daya daga cikinsu, ci gaba da kokari har sai kin cimma burinki na zama ‘malamar makaranta’, kada ki bari soyayyar da ke zuciyarki ta zamo barazana ga ci gaban rayuwarki. Dora soyayyarki akan turba ta hankali da tunani, ba don fita daga wani kunci ko matsatsi na rayuwa ba". -mai son ki. Ta karanta ya fi cikin 'ya'yan carbi, amma ba ta fahimci me mai sakon ke son isarwa gare ta ba. Wa ya ce da shi tana cikin soyayya ko cikin matsin rayuwa? Ta yi tsaki mai karfi ta goge sakon daga cikin akwatun adana sakonta, amma ba ta iya ta goge shi daga kwakwalwarta da zuciyarta ba. To haka washegari, mai 'logo' na hular ilmi ya sake turo mata da gajeren sako. "........ Some one misses you!". Abin sai ya koma ba ta haushi, wannan karon ma ta goge ba tare da ta ba da amsa ba. A ganinta ko waye, yana son yi mata yawo da hankali ne. Ta so ta fadawa Dina, amma ganin Dinar kwana biyun nan ba ta cikin walwala sai ta kyale ta. Karfe tara na daren ranar, suna bisa tebir dukkaninsu, har yaran, suna cin abincin dare, daga can kicin Lynder ke ta goge-gogenta. Wayar Habibu ta shigo wayar Dina, kar ku so ku ga mazari a wurin Dina garin rawar jiki ta datse kiran da hannunta. Ya sake kira a karo na biyu, wannan karon Allah Ya ba ta ikon amsawa. Muryarshi ba ta fita sosai, kamar mai fama da mura ya ce "Yaya kuke? Ya Mairo da yaran?" Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Duk lafiya muke. Haba Habib? Ka barmu cikin fargaba. Akalla ko mene ne ya faru da kai ka daure ka sanar da ni, sannan ka kulle wayar. Duk kwanakin nan hankalina a tashe ya ke". Ya ce "Ki yi hakuri, bana cikin hayyacina ne, I don't want to lose AMEERU. (bana so in rasa Ameeru). Ki debo passport dinku a dakina, daga gobe zuwa jibi ku nemi jirgi ku taho, ki kai yaran gidan Sultana sabida makaranta, ku taho ke da Mairo". Dina ta kidime "Lafiya? Me ya faru da Amirun?" Bai ba ta amsar ko daya ba, ga dukkan alamu kuka Habibun ke yi kasa-kasa, wanda ba ya so ta jiyo. Hankalinta idan ya yi dubu ya tashi. Ba kankanin abu ke sa Habibu kuka ba. Kada Allah Ya sa abin da ya darsu a zuciyarta yanzun ya zam tabbatacce. 7/29/21, 11:15 PM - Kawata: 666667778888 Ranar Litinin. Tun asuba da Mairo ta tashi ta yi sallah ba ta koma bacci ba, ruwa ta taro a famfo ta yi wanka ta shafa mai, ta sanya uniform dinta ta shirya tsaf ta zauna jiran fitowar Baffa. Ba shi ya fito ba sai karfe takwas dai-dai na safe. Ya yane labulen dakin su Mairo cikin sallama ya ce "Ya ya kin gama kimtsawa mu tafi?" Ta ce "Na gama Baffa tun dazu". Ya sa hannu ya daukar mata katuwar jakar, ita kuma ta dauki karamar suka fito. Ta leka dakin Habiba da Hajara ta yi musu sallama suka amsa duk cikin yanayi daya, wato a yatsine, don ita Habiba ba ta so wannan komawa makarantan na Mairo ba, so ta ke abar musu ita tai ta yi musu bauta, don Ladidi ko za a kashe ta ba zata yi musu bautar da Mairo ta yi musu ba cikin kwanaki ukun da ta yi tare da su ba. Shi kuwa Baffa Allah-Allah yake ya maida Mairo makaranta don ta huta da kwarzabar su. Idan ya tuno daga wannan zangon Mairo ta gama makaranta hankalinsa tashi ya ke. Ya soma tunanin da ta gama makaranta idan ta samu masoyi zai ganganda ya yi mata aure, idan ma ba ta samu ba ko cikin mutanensa ya nemi wani wanda ya yaba da hankalinsa ya ba shi ita, shi dai ta bar gaban su Habiba, sai hankalinshi ya kwanta. Ya bude boot ya zuba kayan, ita ma ta sanya jakar hannunta. Ya bude kofar wajen mai zaman banza ta shiga ta zauna, sannan ya zagaya shi ma ya shiga ya tayar da motar suka mika kan titi. Karfe goma dai-dai suna cikin Minjibir, duk wasu shige da fice na dawowar dalibi Mairo da Baffanta sun kammala cikin dan lokaci. Suka yi sallama da Baffan ya kada kan motarshi ya tafi, ita kuma ta nufi ajinsu. Tun daga nesa ta hango Uncle yana rubutu akan allo, wani irin dadi da farin ciki suka ziyarci zuciyarta. Ji ta yi tamkar Baba da Innanta ne suka dawo. Daga can mazauninsu Nabilah ta hango ta, ta kuwa sheko da gudu ta rungume ta, ba tare da la'akari da cewa akwai malami a cikin ajinsu ba. Ya dakatar da rubutun ya juyo, juyowar da ta ke nufin al'amura da dama a gare su a wannan ranar. Mairo ba ta iya ta hada ido da Uncle ba saboda matsanancin kwarjinin da ya yi mata a yau, shi kuma kokari yake ya kalli cikin kwayar idanunta cike da tuhuma da tarin laifuffukanta gareshi. Ya mannawa Nabilah harara ba shiri ta koma cikin nutsuwarta, kai tsaye Mairo ta wuce wurin zamansu shi kuma ya cigaba da bada darasi cikin wani sabon kuzari da nishadi gami da wani karfin gwiwa da ya same shi duk a lokaci daya. Aka fita break amma ita da Nabilah ba su fita ba, sun nutsa hirar bayan rabo. Nabilah ta ce "Yaya Inna? Kusan kullum sai na yi mafarkinku Mairo, tun bayan rasuwar Baba nake jin tausayin Inna, ina gayawa Mamana da Daddy. Dama idan kika yi sati baki dawo makaranta ba zan bi sawunki ko makaranta ta yi min izini ko ba ta yi ba". Idanun Mairo suka kawo kwallah, ta ce

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66