Chapter 61
Chapter 61
sai ki dauke shi a hakan, wato kudurar Allah, ta fi ga haka". Ta jinjina kai, ta ce "Kwarai kuwa". Suka maida idanunsu akan Habib da Amir, wadanda ke ta dabdalarsu cikin dakin, dukkaninsu sai suka yi murmushi, yaran suka burge su. "Kuruciyarsu na da ban sha'awa". Ya fada a zuci, bai san cewa a fili yake fadi ba. "Kamar kuruciyar Mairo, Mairon Baba da Inna, Mairon Kausar da Nabilah…….." Ta yi dariya ta juyar da kanta. Wani ala’amari mai girma na cin zuciyarta. Sai dai ba irin wanda take ji a tsohon mijin ta ba. Ya kura mata ido, zuciyarshi na harbawa. "Ina labarin Nabilah da Yaya Habibu?" "Nabilah tana nan Kano, 'ya'yanta biyar. Yaya Habibu yana Abuja". "Nima na yi aure Mairo. A lokacinda na riga na sallamawa zuciyata cewa na rasa ki, bazan same ki ba, kin riga kin yimin nisa, kin zama matar wani na. Wanin da nake da tabbacin ko mutuwa yayi bazai tafi ba tareda igiyoyin aurenki ba. A halin yanzu Ina da 'ya'ya biyu, tareda ‘yar uwata Ikhlas. Sai dai har wannan lokacin da tunanin Mairo nake kwana nake tashi. Sannan dashi nake ‘functioning, will you believe it?” Ta dago fararen idanunta ta haske shi da su. Tace “sabida me Uncle?” Babu jinkiri, babu inda-inda ya rausayar da kai ya ce "sabida Soyayyarki Mairo! Soyayyar da na ke yi miki a wancan lokacin Mairo, ta zarta hankali, ta zarta duk wani kokarin hankali na ya fassarata. Mahaukaciyar soyayya ce Mairo, wadda ta makantar da ni daga daga ido na dubi sauran mata. Ta dakusar da hasken mata ta Ikhlas daga cikin idanuna. Na tabbatar tunda na rasa Mairo, to bazan samu makwafinta ba. Don haka ne Hajiya tasha wuya da fari kamin inyi aure. Don nasan ko na yi, to bazan baiwa matar hakkokin da addini ya ce na ba ta ba. Ba zan iya sallama mata zuciya da gangar jikina ba". Ya taso ya tsugunna a gabanta, yana so su hada ido, amma ta ki hakan. Ya dora hannunshi akan tafin kafarta. Ta lumshe ido a hankali ta bude su akan yatsun hannunshi da ke bisa tafin kafarta. Ya dauke hannunshi ya zauna sosai a gabanta, ya ci gaba da cewa. "Hajiyata ta shiga tashin hankali mai yawa, ta yi kuka, ta yi rokon duniya akan na yi aure, na kasa Mairo. Daga baya sai malamai ta sa suke yi min rokon Allah, sun tabbatar mata da zan yi aure, sai dai da sauran LOKACI, tunda zuwa yake. Daga baya sai ta koma nasiha, amma zuciyata ta riga ta bushe. Na tabbatar mata idan dai ba so ta ke na auri matar na dinga daukan alhakinta ba, to ta kyale ni. Haka ta hakura ta zuba min ido, amma ta ce ba ta fasa yi min addu'a ba. A yau ina da yakinin Allah Ya amsa addu'arta. For the first time da na ke ji a jikina LOKACI ya zo da zan yi AURE ba irin na Ikhlas da ya zamto hadin iyayen mu ba. Wanda akayi ba tareda anyi shawara dani ko neman yarda ta ba. 8/9/21, 12:19 PM - Kawata: 66 khlas diyar kanin mahaifina ce da Hajiya ta nema min aure bayan na kammala phD dina. A yanzu haka muna da Maryam (namesake) dinki da Sabir. Yau ne na ji wani 'feeling' a zuciya ta mai tuna min da cewa nima namiji ne KAMAR SAURAN MAZA. Wadanda ke da buri a rayuwa, da kuma ‘hope’ (fatan) cikar burin nasu. Shin za ki tallafe ni Mairo? Ki auri tsoho in his fourteeth?" Hawaye na gudu a kundukukinta, ta ce. "Uncle Junaidu idan ka kira kanka 'tsoho' ni kuma na kira kaina me? Tsohuwa?? (second hand)? Ka bazawara...???" Ya yi saurin kai hannu ya toshe mata baki ba tareda yayi niyyar hakan ba. Da sauri kuma ya dauke hannunsa... "Ni har gobe a Maironki na sanki, koda kuwa ace ke kika haife B.U.K baki dayanta…..." "Idan haka ne, ni ma har gobe a Uncle Junaidu na sanka, bana son kara jin wannan kalmar ta fito daga bakinka 'tsoho’. Ya yi murmushi, ya ce. "Da dai ana sakewa tuwo suna ne Mairo..." Ta ce "Ni ma ban ce a sake masa ba, a barshi a tuwonsa, don haka zauna a Uncle Junaidunka ba V.C Junaid ba, na zauna a Mairona…....". Suka bi junansu da kallo, kallon yarda, so da kauna da aminci. Gaskiyar masu iya magana da suka ce, 'Soyayya ba ta tsufa, sai dai msoyan su tsufa’. Don haka sai mu bi JUNAID da MAIRO da fatan ALHERI. *** Alhaji Abdurarhaman ne ke zarya tsakanin falonshi da falon Haj. Aisha yana duba agogon hannunshi, yana kuma azalzalarta kan ta yi sauri ta shirya jirgi ya kusa tashi, wanda zai tashi dasu zuwa Kano a sanyin safiyar ta ranar litinin. Amiru baya nan ya je China, don shigo da wasu kwanfutoci sabon shigowa, Zuwa wannan lokacin ya yarda da nadamar ‘ya’yan nasa, da cikar YAKANAH da jarumtakar Amiru. Shekaru uku kenan da rabuwar shi da Mairo ba tare da ya kara sanya ta a idanunshi ba. Ya tattara karfin zuciyarshi ya karbi rayuwa ba Mairo, yana ganin lokaci ya yi da ya kamata yai surprising din sa, da abin da zuciyarshi ke ciwo dominta. Da abinda rayuwarshi ke muradi......... Duk wasu experiments.......... da ya dora shi a kansu...... bai fadi ko daya ba!!!. Sannan Mairo ta kammala karatunta cikin kwanciyar hankali, duk wasu burirrikan rayuwarta ta cika su, kamar yadda dan uwanta ke so. Ya kira Habibu a waya ya ce su hadu a Kanon gidan Baffa suma za su taho yanzu. Amina ta fito daga daki cikin shiri itama ta ce, “Daddy don Allah zan biku Kanon, ina son ganin Amir da Habib”. Ya ce “Wuce muje Amina ‘yar albarka”. (Amina mijinta ya rasu ne, a yanzu haka zaune take a gida). Hajiya ta fito cikin shirinta, suka nufi cikin chevrolet din Daddy zuwa filin jirgi, inda suka tarar jirgin ya kusa cika, don haka suna shiga ana rufe jirgin. Ba da jimawa ba ya soma keta hazo ya lula cikin sararin samaniya. Suna isa Airport din Malam Aminu, suka tarar da Habibu ya riga su isowa, ya kwashe su zuwa Yakasai gidan Baffa. Daidai lokacin da Mairo ta yowa Uncle Junaid rakiya zai tafi, tana dauke da Amir yana dauke da Habib. A kuma daidai lokacin da Habibu ya sanyo hancin motarsa wadda ke dauke da su Daddy harabar gidan. Daga Habibu, Daddy, Hajiya da Amina babu wanda zuciyarshi ba ta buga ba da ganin Mairo da wannan sankacecen mutum, ma’abocin zati da kamala, da kwarjini bayananne daga sarkin halitta. Karo na farko da Uncle Junaid ya dora idonshi a kan Yaya Habibu da baya bukatar a gabatar mishi, sakamakon tangamemen hotonsa dake sitting room din Baffa. Shima Habibu a take ya gane wannan shi ne JUNAIDUN MAIRO, da Baffa ya kyankyasa mishi a waya, cewa ya dawo neman auren Mairo. Jikin Habib a sanyaye ya fito daga motar, gwiwoyinshi kamar an rarrade su da murfin kwano. Suka yi hannu da Uncle ya yin da Uncle ya kai gwiwoyinshi kasa yana gaida Alh. Abdurrahaman. Amina ta mika hannu ta karbi Amir a hannunshi suka hada ido da Junaidun. A take
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66