Skip to content

Chapter 55

Chapter 55

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

kasa dauke idonshi a kanta. Don sai ya ganta kamar Mairo, idanunta, bakinta da karan hancinta duk sun rikide sun koma na Maironshi sak! Har ya ke jin yafi son wannan Mairon, akan wadda ya baro a gida. Sakon Hajiya ya yi aiki sosai, ya hada wata matsiyaciyar soyayya, mai wuyar fassarawa. 8/8/21, 1:23 PM - Kawata: 55 Tsayin watanni biyu Alh. Abdurrahman na jinyar tilon dansa, ya na kwantar masa da hankali ta hanyar bashi misalai da al’amuran rayuwa kala-kala. Don ya yaye wa kanshi damuwar daya sanyawa zuciyar shi. Yana kuma karantar abubuwanda ke faruwa a cikin gidanshi musamman Hajiya A’isha daya digawa gundumemiyar ayar tambaya. Sabida yadda ta fita hayyacinta da rashin lafiyar Amiru, sai surutai take mai tonawa kai asiri, wani zubin ta hada da su Nina tace su suka angizata, ta zazzagesu tayi musu mugun kalami tana cewa sun cuce ta. Bai tambayeta komai ba, kuma bai tambayi Amiru mai yasa ya saki Mairo ba. Wanda rayuwar sa ke hannun Allah. Dr. Fred yana zuwa gida akai-akai yana kula dashi. Ya ki yarda a maida shi New-York. Yace da Daddy in ma mutuwarce, to yafi so ta dauke shi a dakin da yayi rayuwa da Mairo. A yau Ambasadan Malaysia yazo ganin sa, ta dalilin Habibu da Amiru Daddyn Dina da Alhaji Abdurrahman suka kulla abota. Alh. Abdurrahman yayi masa kyakkyawar tarba, shikansa saida ya zubda hawaye ganin halin da Amirun ke ciki. Ya koma Malaysia cike da alhini inda ya tarar da Mairo da tata sabuwar matsalar har yau ba sauyi. A wannan satin da surutan Hajiya suka ishi Alh. Abdurrahman, yayiwa ‘ya’yan shi mata gabadaya waya, na ciki dana waje, yace yana so su hallara a ‘family meeting’ ranar asabar mai zuwa. Sannan ya kira Alh. Abdulwahab Baban Hanan shima yace yana so Hanan tazo ranar asabar. Alhaji Abdulwahab wanda ke cike taf da fushin sakin da Amiru yayiwa Hanan sati daya da aure ya gintse fuska yace “ince ko lafiya? Bayan an riga an saketa?” Daddy yace lafiya kalau, ‘meeting’ zasu yi tare da ita. Ya gaya mishi bai san abubuwanda suke faruwa a gidan ba, yana so ya sani ne, inda halin gyara ayi gyara. Yace Hanan zata zo albarkacin ka, amma babu batun gyara. Don dama Hanan tana da mai sonta tuni, mutunci da ‘yan uwantaka aka diba aka bawa Amiru. Tunda kuma yace baiyi, to Allah ya hada kowa da rabonsa na ALHERI. Jikin Daddy a masifar sanyaye, da mamakin wai itama Hanan an saketa. To shi yana ina aka yi duk wannan kazamin aiki? Lallai Hajiya ta bashi mamaki. Ya kuma soma zargin koma menene itace ummul-haba’isi, haka kawai za’a kashe masa Da a banza. Habibu bai bar jinyar Amiru ba, duk da tabbacinsa na sakin Mairo da yayi. Duk da zafin hakan dake ranshi. Duk wai wata kusan tafi wata kusan. A wurinshi ba Mairo ce ta hada shi da Amiru ba balle ta zamo silar rabuwarsu. Allah ne ya hada su, ya sanya kaunar juna da soyayya a tsakaninsu, ba kuma zasu rabu a dalilin ta ba. Ko ba komai Amiru ya wanke mishi zuciya da baiyi mummunan saki ba wanda Allah baya so. Yayi kokari ya karanta hargitsatstsen rubutun ya ga saki daya ne. Kullum kafin ya fita ofis zai zo, haka in ya tashi yana nan tare dashi har goman dare. Amiru yana shaida kowa, amma baya magana. Sai bin kowa da ido. A ganin shi rayuwar bata cancanci a cigaba da itaba, ba tare da abinda zuciya da gangar jiki ke so ba. In za’a bashi zabi gara mutuwa da rayuwa babu Mairo. Kasancewar Daddy da Habibu na kula da shan magungunan sa akan lokaci, ya sanya kullum sauki na kara samuwa. Daddy ya shigo falon da ‘ya’yan sa, Hajiya da Hanan ke zaune, kowanne kai a kasa. Jiki yayi la’asar babu laka. Ita kanta Hanan ta tsorata da ganin yadda Amiru ya koma cikin dan lokaci kalilan. Sau daya ta shiga part dinshi, tausayi bai barta ta kara komawa ba. Ko babu soyayya Amiru dan uwanta ne wanda take ji har cikin kashi da bTa kuma alkawartawa ranta fadiwa Daddy gaskiyar duk abinda ya tambayeta ba tareda shayin Hajiya ba, don Yaya Amiru ya samu lafiya, ya samu abinda yake so, ita tayi hakuri, ta auri Ramadan wanda ke son ta kamar ya kashe kan shi. Amina kadai ake jira a falon wadda bata karaso daga Switzerland ba har yanzu. Don haka ganin ana batawa ‘majority’ lokaci, akan mutum daya, Daddy ya yanke hukuncin ayi taron bada ita ba. Ya bude taron da cewa kowa yayiwa Annabi salati goma. Ya ja doguwar addu’a suka shafa. Yasa gilashi ya soma duban ‘ya’yanshi mata su goma sha daya da fuska mara walwala. Ya maida dubanshi ga Hajiya A’isha yace “Hajiya, keda Hanan kune a gidannan sanda abin ya faru, don haka ku zan fara tambaya. Yaya aka yi Amir ya saki matansa biyu duk a lokacin daya?” Hajiya tayi shiru, ta soma share ido da gefen mayafinta, abinda ya riga ya zame mata jiki tun ranar da aka dawo da Amiru wai yana fama da ciwon zuciyar data yi tsammanin yayi hannun riga da shi. Tararradinta shine idan ta rasa Amiru ina zata tsoma ranta? Mutumin da ke yi mata biyayyar da duk cikin ‘ya’yan ta babu mai yi mata kwatankwacinta? Mutumin da ya sadaukar da farin-cikinshi akanta. Bama wannan ba, ina zata kai hakkin Mairon da bata ci mata ba, bata sha mata ba, biyayya take yi mata tamkar tayi mata sujjada, kawai don Allah As-samadu bai bata haihuwar da bata isa ta baiwa kanta ba? Ta tabbatar ba komai ya kai ta yin umarnin data yi ba, bacin ran sakin da yayiwa Hanan ne. Wadda ita bata damu ba, kamar dama jira take, yana sakinta ta hada ya-nata-ya-nata tayi tafiyar ta, babu ko cikakkiyar sallama. Sai yau ta ganta cikin taron da bata zata ba. Amma ko waya Hanan bata kara yi mata ba. Gatanan da ranta da lafiyar ta ba abinda ya dameta. Sai nata dan data jefa cikin halin ha’u’la’i. zaiyi-ba zaiyi- ba Allah masani. Ta dubi Nina, kamar ta tsinka mata mari, domin dai ita ta kaita ga abinda bata taba tsammanin yi a rayuwarta ba. Wato bin malaman tsafi Yarbawan Lagos, haka-kawai zasu fidda ita a imanin ta. Kukanta ya tsananta ta kasa baiwa Daddy amsa. Don haka ya juya akalar tambayarsa ga Hanan. Ta sunkuyar da kai ta soma fada masa duk abinda ya faru, tun ranar da Hajiya ta aika ta zo, abubuwanda ta rinka bata wai tayiwa Amiru amfani dasu, har zuwa ranar daya saketa, da tirkeshi data yi ya saki Mairo. Daddy ya jinjina kai cikin al’ajabi da mamaki, yaushe Hajiya ta koma haka? Ya ce da Hanan ya gama da ita, kuma ya gode. Kuma menene ra’ayinta kan zama da Amiru? Tana so idan Allah Ya bashi lafiya zata dawo dakinta ne ko a’ah? Ta sunkuyar da kai tace “ka fahimce ni Daddy. Ba wai bana son Yaya Amiru ba, amma shi wallahi-wallahi baya so na. Matarshi kadai yake so Daddy. Kuyi kokari ku dawo mishi da abarshi cikin gaggawa in har kuna son lafiyar shi fakat. Nikam har ga Allah na hakura,

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66