Chapter 62
Chapter 62
ya ga fuskar Amir da Habib a fuskarta, ita kuma ta ji wani ‘magnet’ na jan zuciyarta a kan wannan mutum da ba ta sani ba, ba ta taba gani ba. Ya dago suka hada ido ta yi saurin sunkuyar da kanta. Mairo na son gabatar da Yaya Habibu ga Uncle amma kunyar su Daddy ta hana ta. Ya shiga mota ya tafi su Amir na ta kuka sai sun bishi. Hajiya ta kama hannun Mairo, Amina kuwa rungume ta tayi tana hawaye, a haka suka shiga dakin Habiba. Shi kuma Habibu da Daddy suka wuce falon bakin Baffa. Cikin dan lokaci Habiba da Hajara sun baibaye su Hajiya da cima ta girmamawa da ruwa da lemu, sun zauna ana ta gaggaisawa. Mairo da Amina dakin Hajara suka wuce suka bar Hajiya da su Habiba. A nan ne Amina take labartawa Mairo rasuwar Ghali (mijinta) watanni biyar da suka gabata. Ba tare da Allah ya basu haihuwa ba. Mairo har da hawaye na tausayawa Amina, don ita kanta shaida ce a kan matsananciyar soyayyar da suke yiwa juna. Mairo na so ta tambaye ta AMEERU ba ta so ta bada kanta. Amiru ya yi mata miki mai girma a zuciyarta. Tunda suka rabu bai taba nema ko sau daya ya ganta ba, sai ‘ya’yansa. To akan me ita zata nemeshi? Ta tabbata duk inda yake yanzu ya dade da shafe ta a babin rayuwarsa. Watakila ma ya kara aure bayan Hanan, ya sallamawa wata wannan gangar jikin da ada ta dauka mallakinta ne ita kadai. Don ta san Dan Abdurrahaman Gaya, ba zai iya kaiwa tsawon wannan lokacin ba tare da aure ba, in ta yi la’kari da halittarsa, na mutum mai tsananin yawan bukata. Sannan Hanan, bata da surar irin matar da yake son aure. Ko kuma watakila ya komawa banasariyar matarshi? Allah masani. Amina ta ce “Rayuwa tafe take tare da destiny (kaddara) kala-kala Aunty Mairo, kin manta da brother, kin bude sabuwar rayuwar da ta bani mamaki, kin kara kyau, kin kara kiba, kin kara haiba da kamala. Sabanin shi da a kullum yake kara lalacewa. Cikin shekaru ukun nan ban kara ganin dariyar Yaya Amiru ba, ki yafewa mai kaunarki wanda ya sadaukar da zuciyarsa ga soyayyarki. Ku tallafi juna, ku baiwa zuciyoyinku abin da suke so. Hajiyata da ‘yan uwana sun yi kuskure, sun kuma gane kuskuren su, sun yi nadama mai suna nadama amma ku, (keda Amiru), Daddy da Habibu har yau kun ki karbar tuban su, ban san me yasa ba”. Mairo ta yi murmushi wanda iyakacinsa fatar bakinta, ta ce, “Mun karbi tubansu man? Watakila dai iyakar zaman ke nan, babu saura, tunda aka kawo wannan lokacin. Shi ya gaya miki yana son komen? Yana da mace irin Hanan a gefe?” Mamaki ya kama Amina, ta tabbata Mairo ba ta san tare suka yi waje ita da Hanan ba. Ta ce, “A kan sakin Hanan aka yi naki, Allah sarki brother! Zurfin cikin shi na bani mamaki. A halin yanzu Hanan tana Porthercourt ‘ya’yanta biyu tare da mijinta Ramadan wani ma’aikacin kwastom”. Mairo ta yi shiru, kamar an zuke jinin jikinta. Tausayin Amiru ya kama ta, Allah kadai ya san halin da rayuwarshi ke ciki. Ta tura hannu cikin jakarta ta zaro wasu kananun katina da aka yiwa rubutu da kumfar golden, ta dorawa Amina a cinya. A kasalance Amina ta dauka, kati ne na gayyatar daurin auren PROF. JUNAID ATIKU GALADANCHI da DR. MARYAM MOHAMMAD BEDI, wanda za a gabatar kwanaki goma sha hudu masu zuwa. Ba ta kai karshen karanta katin bikin ba Amina ta rushe da kuka. Ashe masu kukan suna da yawa, domin a can falon Baffa ma Hajiya ce ke ta kuka tana rokon Alh. Abbas ya yi wa Amiru uziri, su ne da laifi ba shi ba. Su kuma ba su yi hakan da nufin A BARI YA HUCE...... ba, sai don a bawa Mairo dama ta sarara ta cika burin neman iliminta. Cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Daddy ya ce. “Idan da mai laifi to ni ne, don ni na hana Amiru yin wani yunkuri na dawo da iyalinsa har tsawon wannan lokacin. Ina so in koya masa jarumtaka, in nusar da shi cewa; “kallafa rai a kan abin da ake so, da amanna da cewa samuwar abin nan kadai shi ne samun lafiya da kwanciyar hankali ba shi ne ba”. Dauriya, hakuri da juriya da tawakkkali sune halayen da ake son namiji ya suffantu dasu. Kuma na gode Allah....... DUK WASU EXPERIMENTS DANA YIWA AMEERU BAI FADI KO DAYA BA..............!!!” Baffa ya jinjina kai ya ce. “Nima in son samu ne, na fi son Mairo ta koma wurin mijinta ta tarbiyanci ‘ya’yanta a gabanta. Amma Alh. Junaidu ya zarta duk yadda kuke tunani a wurin mu. Don haka bana cikin wannan magana..... Zabi yana ga Mairo, tunda ita Allah ya baiwa damar zaben mijin da za ta iya zama da shi a halin yanzu. Don haka ku bani kwana biyu zan tuntube ta”. Habibu bai ce komai ba, don ba shi da ta cewar, bai san me zai ce ba, bayan Allah ya yiwa Mairo zabin alheri, wannan karon ba zai yi shisshigi ba. *** SUNA tafe cikin jirgi amma Daddy baya cikin nutsuwa. Tausayin gudan ransa ya ishe shi, ko ma me ya faru ya tabbata shi ya jawo mishi. Shekaru uku ba kwana uku ba!!! Ya nesanta Amir da iyalinshi a kan laifin da ba nashi ba. A kan hujjojin sa da basu da karfi. Don haka suna sauka a jirgi ya bude waya ya kira Amiru yana nishi kamar mai ciwon asthma. Ya ce, “Ka bar duk abin da kake ka taho, ka wuce Kano ka nemi sasanci da iyalinka in har kana so. Na amince maka Amiru, da sanya albarkata.... saura kwana goma sha hudu a daurawa Mairo aure!!!” Ga mamakin Daddy sai ya yi murmushi, wanda har sautinsa ya ratso cikin wayar, ya ce. “Ka kwantar da hankalinka Daddy, na dade da sanyawa zuciyata salama, na yi amanna da cewa idan akwai sauran zama tsakanina da Mairo, to za ta dawo mini ko ba dade ko ba jima”. **** Lawan da Ahmad ‘ya’yan Baffa ne a harabar gidan Dr. Mairo, wanda ke a Area C cikin sabuwar jami’ar Bayero suna wasan kwallon kwando, ya yin da a gefensu Habib da Amir ne tare da wasu sa’o’insu ‘ya’yan makota suke wasan tsaren kekuna, yara masu ban sha’awa. Suna sanye da kayan sanyi masu laushi farare sol, an rubuta I LUV MUMMY, kafafunsu daure cikin farin cambas, sunyi kyau har sun gaji kamar ‘ya’yan South-Western. Daidai lokacin da motar kirar (Camero, 2 Door) ta yi parking and hankali a gefensu, matukin motar ya duba katin da ke hannunsa ya tabbatar lambar gidan ta yi daidai da wadda ya gani a rubuce. Sai ya kashe ya fito. Sanye yake da suwaitar ‘Dolce & Gabbana’ mai dogon hannu, da shudin wandon jeans. Ya yin da rigar ta kasance fari da ratshin ja da blue. Ga duk wanda ya san shi, ba zai yi gaggawar gane shi ba, saboda yadda fatar jikinshi ta kara kwanciya, tare da goguwa mai nuni da alamun hutu. Ya jawo bakin PRADA ya saya kwayar idanun shi. Daidai lokacin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66