Chapter 18
Chapter 18
domin ba ki da wanda ya fi shi. Sannan Abbas mutum ne mai ZUMUNCI ki dubi yadda ya rayu yana kyautatawa mahaifinki. Ina da yakinin zai rike ki da amana tamkar mahaifinki, har zuwa sanda zai miki aure". Sai ta mike cikin karfin zuciya, ta yafa mayafinta ta sa takalminta. Karime ta rakata gidansu tana hada kayanta tana kuka. Ta tattara zannuwan Inna da kayayyakinta ta sa a wata tsohuwar akwatun karfe ta rufe, ta tura karkashin gadon bononta. Ta tattara 'yan kudaden Innar irin wanda Junaidu ke ba ta ne a duk zuwan da ya yi, da kudin motar da ta warewa kanta duka ta zuba cikin jakarta ta makaranta. Suka fito Karime ta datse dakin da kwado, tana tafe tana waiwayen dakunansu da madafinsu da ta ke jin tana yi masu kallon karshe ne, wasu hawayen suka zubo. Tana bayan motar Dagaci wata (mitsubishi) mai hayaniyar tsiya, in banda karar injina da salansa ba abin da kake ji, shi da Malam Tanimu suna gaba. Ta kama jikinta tsan-tsan sabida gwaruwar da kanta ke yi da jikin motar sabida rashin kyawun birjin Gurin Gawa. Shi da Malam Tanimu suna ta hirarsu ba abin da ya dame su, ita kuwa sake-saken da ta ke yi cikin ranta na abin da zata je ta tarar a gidan Baffanta da 'ya'yansa marasa adadi da rashin tarbiyya ta ke yi. Sai da suka hau titin gidan zoo sosai sannan motar ta daidaita, tafi-tafi har suka iso gidan Sarki suka billa Yakasai ta nan. Kugin karshe da kwarababbiyar motar ta yi a kofar gidan Alhaji Abbas Maigoro ne. Gida ne ginin siminti mai dakali hagu da dama da manyan zaure irin ginin masu kudin da. Yara kanana da samari suna ta shige da ficen su. Gabanta ne ya soma dukan uku-uku sabida haka ta yi hamzarin jan Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un har ta samu bugun zuciyarta ya yi dai-dai. Suka ce ta shiga cikin gidan ta turo musu Alhajin suka fito kan dakalin gidan suka zauna. Cikin sanyin jiki Mairo ta fito tana tafe tamkar macijiya sulu-sulu abin tausayi. Ta yi sallama a tsakar gidan, Uwargidan Hajiya Habiba ta amsa, wadda ke tukin tuwon dare a bakin murhu. Ta karasa inda ta ke ta tsugunna tana gaishe ta cikin nutsuwa. Ta amsa da alama ba ta gane ta ba, ta ce "Yammata daga ina? Ban gane fuskar ba". Ta dukar da kai ta ce, "Gurin-Gawa". Habiba ta kalle ta sosai na 'yan dakikai, nan da nan fara'ar da ke fuskarta ta bace. Ta juya ta ci gaba da tukin tuwonta. Cikin halin ko'in'kula ta ce "Auyo! Ce min zaki yi MAIRON HURE shalelen HURE, sai yau tasan mu mutane ne da ta turo ki ki gaishe mu? Ce nake har jinya kuka yi anan ta tsayin watanni ba ku san hanyar gidanmu ba, sai dai kullum mu tuka mu ba ku? Ince ko yanzun ma ba tasan kin zo ba kada mu moran mata ke?" Mairo ta share hawayen idanunta, ta ce "Tare muke da baki suna zaure, sun ce suna son ganin Alhajin ne". Sai da ta mula ta ce "Ba ya nan, yana kasuwa, amma yana gab da dawowa". Ta taso sumui-sumui ta fito dakalin gidan ta fadawa su Malam Tanimu sakon Hajiyar. Ta ci gaba da tsayuwa a zauren ba ta koma cikin gidan ba. Malam Tanimu ya ce "Bude motar ki kwaso kayanki mana ki shiga da su?" Jikinta ya yi sanyi lakwas ko numfashi da kyar ta ke shaka, ta ce "A'a, mu dai jira Baffan". Dagaci ya yi nazarinta yana taunar goronsa, ya ce "Mairo ki saki jikinki, nan fa gidanku ne, gidan ubanki ne". A ranta ta ce "Kayya Uba guda daya ne, na tabbata na rasa nawa". Suna nan zaune ita kuma tana tsaye daga cikin zauren kusan rabin awa, Ladidi diyar Alhaji Abbas wadda ta ke kusan tsararta ta dawo daga unguwa rike da hannun kanwarta Rahma ta ci kwalliya kamar me? Tana yafe da wani dan gyale mai kama da abin tatar koko, ta daga ido tana kallon Mairo kana ta kyabe baki ta ce "Ah! Yau wace rana?" Ta yi murmushi, ta ce "Ladidi ke nan, kuna lafiya?" Ta sake kyabe bakin (ga alama al'adarta ne yin hakan a duk sanda zata yi magana), wanda kwata-kwata ba ya mata kyau, don ko daya ba ta da kyawun fuska. Ta ce "Gidan namu ne bai ishe ki shiga ba da zaki tsaya a zaure, ko kuwa wani sabon salon gulmar ne Hure ta koya miki, ta ce idan kin zo ki yi mana, don Baba ya ce mun wulakanta ki?" Ta bude baki tana kallonta kawai cikin mamaki, ba ta ce komai ba, ta yi ciki sai ta danne zuciyarta ta bi ta a baya. Suna shiga Habiba ta ce "Ai na dauka tafiya ta yi babu sallama, saboda uban nata ba ya nan". Ta sake kyabe baki, ta ce "Can soro na ganta a tsaye, salon ta ja mana magana wajen Baba". Amarya Aunty Hajara ta yane labulenta jin cece kucensu, ta ce "Wa nake gani kamar 'yar gidan Hure?" Habiba ta ce "Ke ma dai kya fada, ai ni na dauka batan kai ta yo". Hajara ta saki labulenta tana cewa, "Allah Sarki! Alhajin yana kan hanya don nasan dai ba wajenmu kika zo ba". Mairo dai na tsaye tamkar mutum-mutumi. Tana mamakin rashin mutumci irin na matan Alhaji Abbas. Babban mamakinta daga Habiba har Hajara babu wadda ta ce ta shigo daki. Haka Ladidi ta shige dakinsu na 'yammata ba ta kara bi ta kan Mairo ba. Ta ci gaba da tsayuwa sororo! Wannan yaro ya shiga, wannan ya fita duk ba su santa ba. Wannan ita ce rayuwar da Innarta ta ke guje mata ke nan ta matan birni marasa karah da rayuwar kowa yai ta kansa, ko kuwa abin nan da Bahaushe ke cewa, kowa tasa ta fishshe shi. 7/29/21, 10:05 PM - Kawata: 0989 Ta dago idanunta jage-jage da hawaye, don ganin ko wane ne wannan? Da haka kawai zai zo ya dafata? Ko ta ce da wani tana neman taimako ne? Wa za ta gani? Yaya Habibu ne! Cikin matsanancin mamaki ya ce, "Mairo?" Ba ta amsa ba, illa ta bi shi da kallo, da jajayen, idanunta. Ya sake cewa "Me ya kawo ki nan? Ina za ki je?" Nan ma shiru ta yi masa, sai kallonsa ta ke kamar ta rufe shi da duka don haushi. Ya ishe ta da tambaya, ya barta ta ji da kukan zuci, da takaicin da ya dame ta. Don ji take kamar Amiru ya bula mata kura, ya ja motar rayuwarshi, ya barta. A nashi bangaren, shima Habibun, haushi ne ya kama shi, ya ce "Kina ji ina magana kin yi kunnen uwar shegu da ni? Na ce me ya kawo ki nan, kuma gurin wa kika zo? Ina zaki je?" Nan ma shiru ta yi masa, kamar da dutse yake magana, kuma ba ta dauke idanunta daga kanshi ba. Ta kafe shi dasu kurrrrr! Kamar shi ne ya kori Amirun. Iyakar fusata Habibu ya fusata, ya fizgi hannunta suka fito harabar adana motoci na airport din, yana baza ido don gano inda ta yi fakin. Daga can ya hango
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66