Chapter 38
Chapter 38
bayan motar ya dauko falmaran din suit' dinshi da wayoyinshi ya fito, ita ma ta fita, ba tare da ta yarda sun kara hada ido ba. Dina ta tari mijinta kamar yadda ta saba a kullum, amma ya sakar mata harara. Ya fincike jikinsa daga jikinta ya juya ya kara hararar Mairon da ke shigowa sumui-sumui kai a kasa, kamar wata munafuka, ya dawo da dubansa ga Dina. "Da saninki Mairo ta dauki mota ta tafi airport?" Dina ta yi shiru, ya ce "Magana nake, ko ke ma sullutun za ki mayar da ni ku barni na yi ta magana ni kadai?" Ta ce "To me ya faru?" "Ya zan tambaye ki kema ki tambaye ni? Amsa nake son ji kawai, kina sane ta tafi ko a'ah? Yanzu na je kai Amiru zai tashi zuwa Najeriya na ganta tana kuka akan titi uban me ta je yi?" Dina ta hau kame-kame ganin yadda ya hasala sosai, ta ce "Am... Eh, ai sako zata kai wa Amirun". A fusace ya ce "Sakon me?" Ta ce "Ka ga Allah ban sani ba, can tsakaninsu". Ya yi dogon tsaki, ji kake 'tsiiittt!' Ya maida kallonshi ga Mairo "Ba ni wayarki". Ta soma dube-dube a falon inda ta cillar da ita, can ta ganota bayan room heater, ta dauko ta mika mishi. Ya kashe ta gaba daya ya jefa a aljihun wandonsa da sassarfa ya nufi bangarenshi ya barsu nan tsaye cirko-cirko kamar an dasa su a wurin. Dina ba ta yi gigin binsa ba, don tasan halin kayanta sarai, idan ya yi fushi yana bukatar a daga mishi kafa, har sai ya sauko don kansa, wanda ba ya daukar dogon lokaci yake yin hakan. Ba ya son aje ana wani lallashin shi ko ace za a ba shi hakuri. Ta kama hannun Mairo suka nufi dakin Mairon suka zauna a bakin gado. Ta ce "Kin same shi?" Ta girgiza kai, wasu hawayen suka zubo. Dina ta sa yatsunta tana share mata, "Kada ki yi kuka Mairo, mika dukkan lamurranki ga Allah. Amiru yana sonki, na kuma tabbata zai dawo. Shi ma Junaid yana sonki, ina tabbatar miki da shi ma akwai ranar da zai zo. Allah kadai Ya san mijin ki a cikinsu, don haka ki dukufa ga neman ZABIN ALLAH ba zabin zuciyarki ba". Don haka Mairo ta tattara shawarwarin iyayen rikonta, wato masoyan nan nata guda biyu, da ba ta da ya su a duniya: Yaya Habibu, da Maidakinsa, Dina. Ta karbi shawarwarin su da hannu bibbiyu, ta fuskanci jarrabawar karshen shekara da ta tunkarota, wadda daga ita zata shiga shekara ta uku, kuma ta karshe da zata hada digiri dinta. *** A yau suna da tutorial class, kan wani kwas da zasu fara jarrabawa a kanshi. Mairo ta fi duk 'yan ajin su fahimtar wannan darasin, don haka suka bukaceta da ta yi musu karin bayani. Maryam Muhammad Bedi, ta fito gaban ajinsu ta tsaya rike da takardu, domin wani abu ne da ta kware a kai, wanda Uncle Junaid ya koyar da ita, wato dabarun speech in public, ba tare da jin ko da dar a zuciyarta ba. Ta soma feso sassanyan Turanci daga makogaro zuwa harshe, sannan siraran labbanta su furta. Kai ka ce diya ce ga Herbert Spencer. Tana bayani ne akan Segmund Freud's stages of psycho-sexual development, tana farke theory tana yin kaca-kaca da ita tun daga phallic-stage... Anal stage... da 'yan uwansu. Sannan ta koma kan SOCIAL CLASSES; the BOURGEOISIE and the PROLETARIAT………. !!! Habibu da ke cikin 'yan ajin ya sanya mask (fuska) sai ya soma kuka. Sannan ya taso ya fito, zuciyarshi cike da alhinin ina ma ace... Malam Muhammad Bedi, zai dawo duniya yau ya ga Mairon shi na koyar da turawa, da sauran jinsin al'umma. Don haka Mairo yau da ta dawo gida ta ga sauyi sosai daga Yayan nata. Domin dai ya tabbatar ta tsaida hankalinta tana karatun, kamar yadda yake so. Yaje makarantar ne ya shiga cikin ‘yan ajinsu don yayi supervising hakan. Shi da Dina ne cikin three seater suna aiki cikin takardu da kwamfuta. Ya daga kai ya dube ta yana murmushi, a lokacin da tayi sallama ta shigo. "Mairo 'yan makaranta......Mairon Dina….. Mairon Yaya Habibu". Ta yi murmushi, har kumatun ya lotsa. Za ta wuce cikin daki ya ce. "Zo zauna, mota zan sake miki". Da hanzari ta dago ta dube shi. Ya daga mata gira (in affirmation) watau cikin tabbatarwa "Gaya min duk irin motar da kike so ni kuma na yi alkawarin zan yi kaffara in saya miki. Sannan ki mai da walwalarki kamar da, bana son ganin wannan shiru-shirun da kika koma. Sannan Dina ta fada min ko hira kin daina yi da ita, kullum sai karatu. A dinga rage karatun, a dinga baiwa zuciya da kwakwalwa dama su huta, sai karatun ya fi zaunawa sosai. Zan tafi Nigeria gobe, akwai muhimman al'amura da zamu gabatar ni da Amiru a Abuja, zan yi sati daya, me kike so in kawo miki? Dina ta rubuta min kayan abincinmu na gargajiya su kuka, daddawa, rogo, kubewa da sauransu. Ke kuma fa?" Ta yi murmushi kanta a kasa ta ce, "Ladidi nake son gani". Ya ce "Ai an yi mata aure. Kina ganin zan rabo mace da gidan aurenta ne na kawo ta? Ai mijinta ba zai so ba, ki yi hakuri ki kare karatun gida za mu koma gaba daya. Gobe sai ku je da Dina ki zabo motar da kike so, zan bar komai a hannunta". Ta yi godiya, ta kama hannun Little Mairo suka nufi dakinta. Dina da Habibu suka bita da kallo, dukkansu ba haka suke son ganinta ba. Gaba daya ta sauya, tun ranar da Amiru ya tafi, daga daki sai daki, daga littafi sai littafi na gaggan malaman sociology. Habibu na addu'ar Allah Ya sa ba sociology'n ne ya soma taba mata kwakwalwa ba. Shi yasa tun farko bai so ta zabi wannan kwas din ba, amma ta dage ita nan duniya shi ta ke so, ba don komai ba sai don ta zama Uncle Junaidu. Ita Dina da yake tasan dawan garin, wato Mairo ta soma kamuwa da matsananciyar soyayyar Amiru sai ba ta damu sosai ba. Habibu ya daga Nigeria a washegari, da tsarabar Baffa da iyalinshi rankatakaf! Da aiken Mairo ga Ladidi. Ita da Dina suka shiga gari suka yo cefanen kayan abinci da kayan amfanin gida da ya kare, sannan suka nufi wani kamfanin motocin (General Motors) dake nan cikin Michigan ta zabi mota irin tata ta da, watau GMC Terrain ruwan makuba, suka shirya payment Dina ta biya, ta karbo rasidi da takardun mota aka biyo su da ita gida. Duk a kokarinsa na son farantawa 'yar uwarshi, yana sauka a gidan Baffa ya kira wayar Dina, ko gaisawa ba su yi ba, ya ce ta hada shi da Mairo, ga Ladidi ga Baffa. Farin cikin da Mairo ta samu kanta da jin muryar Baffa da Ladidi ba zai fadu ba. Sun dade suna hira, inda Ladidi ke sanar da ita tsohon ciki ne da ita, ta yi mata fatan sauka lafiya, sannan ta baiwa Dina suka ci gaba da hira ita da Habibu. Washegari Dina ta kira shi don su gaisa, amma wayarshi a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66