Skip to content

Chapter 11

Chapter 11

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

Abin dariya ga wadanda Allah Ya yiwa falalar rayuwa. Ban san cewa ni 'yar talaka ba ce sai yanzu, tunda kuwa ban taba neman abin da zan ci na rasa ba, sai na dauka iyakarta ke nan. Ashe akwai masu shi fiye da ni, amma idan da ace ni ce a matsayin mai shi din, ba haka zan yi wa mara shi ba!". Mamakin kalaman karamar yarinya kamar wannan ya kama shi. Sai dai ya kula magana ta ke tun daga karkashin zuciyarta, ba wai tunaninta ba ne. Ya ce "Mariama!" Ta dago ta dube shi, amma ba ta amsa ba. Ya ce "Ina son ki sa wa ranki cewa, ba duka mutanen da kika tarar halinsu daya ne ba. Kowa da kika gani a duniya da irin halayyarsa. Wani yasan darajar kansa, yasan ta mutane, wani bai san darajar kansa ba, bai san ta mutane ba. Wani yasan darajar kansa bai san ta mutane ba.To wannan ba cikakken mutum ba ne, kuma shi ne wanda Allah Ubangiji Ya yi alkawarin dankafar da shi a duniya da lahira sabida girman kansa. Da zarar ka yi tunani ko ya ya cewa, kai wani ne, to kai ba kowa ba ne a wurin Ubangiji. Sabida haka a yadda kika dau kan naki a ba kowa ba, ci gaba da hakan. Amma kada ki yarda da cewa, sai wun fi ki ne. Ido biyu gare su, kunne biyu, kafafu biyu, hannaye biyu, ke ma su gare ki. To akan me za ki yi tunanin sun fi ki? Wanda ya fi ki kawai shi ne wanda ya fi ki tsoron Allah!”. Jikinta ya yi sanyi, ranta ya yi fari. Tana dubanshi da kyawawan idanunta, ta ce "Uncle kana nufin ni ba abun kyama ba ce?" Ya girgiza kai "Ko daya Maryama. Da za ki daure ki fidda su a gabanki ki yi karatu sosai ki dinga gyara kanki, sai kin fi su kyan gani. Ko a yanzu haka kin fi su, gyara suka fi ki. Ba kawa kika zo nema ba, ilimi kika zo nema, irin wanda suka zo nema. To akan me za ki damu da su? Ai abu daya za ki damu da shi, shi ne ki dage ki ga cewa ba su fi ki kokari ba". Ta yi murmushi ta ce "Uncle kana da kirki, sai na ke jinka kamar Yaya Habibu. Shi ma haka yake yi min irin maganganunka. Da zai zo ya ganni a makarantar nan, ban san irin farin cikin da zai yi ba". Ya ce "Yaya Habibu yana ina yanzun? Ni kuwa inje in gaya masa, ga ki a babbar makaranta". Ta washe baki ta ce "Ayyah, yana da nisa, yana karatu ne a kasar waje, amma komi nake yi sai in yi ta ganin kamar yana kallona, sabida shi ne ya dage, ya sani a makaranta". Ya ce "Ni kuwa gani na dage da yardar Allah sai kin yi karatun da Yaya Habibu zai dawo ya yi alfahari da ke, amma hakan ba zai yiwu ba sai da goyon bayanki Maryama, wanda ba komi ba ne da ya wuce perserbearance (jajircewa) da ba da himma". Ta sake yin murmushi har kumatunta suka lotsa, ta ce "Na gode Uncle, kuma na yi maka alkawarin I'll persebere". Ya yi mata tafi guda daya ya ce "Good Maryama, ina neman alfarmar ki rike ni a matsayin Yaya Habibu",. Wani farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta ce "Kenan ka yarda na rinka kiranka da Uncle Habibu?" Murmushi ya yi, "A'ah, UNCLE JUNAIDU. Sunana Junaidu Galadanchi". Ta ce "Galadanchi?" Ya ce "Eh, kin santa ne?" Ta ce "A'a, ban taba ji ba ne. Garinku ne Galadanchi ko sunan Babanka ne?" Da alama Maryama matambayiya ce, kuma matambayi ba ya bata. Hazakar yaro na da alaka da yawan tambayarsa (curiosity). Ya ce "Galadanchi karamar unguwa ce a cikin birnin Kano. Sai dai tarihinta mai girma ne ga Kanawa. Duk wani Ba-Kano ya san Galadanchi, sannan mu 'ya'yan cikinta muna alfahari da ita da kasancewarmu 'ya'yanta. A Galadanchi ne aka fara samun Dr. a ilimi a jihar Kano. Haka idan kika bi tarihin manyan 'yan bokon Kano, da mayan malaman Jami’ar Bayero, wadanda suka fito da jihar Kano a tsakanin jihohi 'yan uwanta, to duk 'yan Galadanchi ne. sannan gasu da kyau, ga Alkur’ani da Tajwidi a cikin kansu". Ta ce "Ina fatan wata rana, in ziyarci Galadanchi". Murmushi ya yi "Insha Allahu za ki je Galadanci Maryama. Yanzu dai jeki ci abinci kamar sauran dalibai, idan kun fito 'pref' da yamma sai ki rubuta aikin gobe ki kawo mani". Ba musu ta mike ta nufi kofar fita. Bai daina kallonta ba har sai da ta kule ya daina ganinta. Shi kam bai san dalilin da ya sa ya damu da yarinyar ba. Haka dan zaman da suka yi a yanzu ya kara sanya mishi jin son taimakonta. Mairo da ta fito 'pref' ta yagi takarda kamar da wasa, ta soma rubuta 'essay' dinta mai taken 'My first day in secondary school'. Da jagwalgwalallen turancinta mara 'tenses' har haduwarta da Uncle a aji ta rubuta, inda ta ce, ba ta taba haduwa da mutum mai kirkinsa ba. A karshe ta ce “shin ko mutum nawa ne masu jin kai irin UNCLE JUNAIDU? Ta ce, Uncle Junaidu ya sa mata burin son zama malamar makaranta, wanda a da ba ra'ayinta ke nan ba. Ta sake bin jagwalgwalonta ta yi dan gyaran da zata iya, ta sanya a tsakiyar littattafanta. Washegari da karfin gwiwarta ta shiga aji, to amma Uncle bai tambayi 'assignment' din shi ba sai da period dinsa ta shiga. Yana bi daya bayan daya yana marking har ya zo kan na Maryama Bedi. A zahiri duka 'yan ajin sun fi ta iya Turanci, da kula da 'tenses' sabida su sun sami kyakkyawan tushe daga makarantu masu tsada. To amma idea da ke cikin rubutun Maryam fasaha ce tsagwaronta. Ta yi rubutunta kamar da gasket, tana magana kamar akan idonsa abin ya faru. Ya kirata yana nuna mata kura-kuranta, tare da cewa "Matsalarki daya ce a Ingilishi (tenses), don haka darasinmu na yau tenses ne". Nan da nan ya fara darasi inda Mairo ta dauki dukkan hankalinta ta likawa Uncle. A yau da aka fita break ma ba ta yi saurin fita ba, ta zauna ne tana aikin lissafi (maths). Uncle Junaid ya kwankwasa desk dinta, ta yi hamzarin dagowa kamin ta yi murmushi ta ce "Uncle dama ba ka fita ba ne?" Ya ce "A'ah na fita, dawowa na yi. Tun daga staff room na hango ki kina rubutu, zuwa na yi na gaya miki ki daina zama cikin aji yayin da kowa ya fita. Komi na makarantar nan cikin tsari yake, yanzu lokaci ne na cin abinci ba na yin aiki ba. Idan wani bai ga abinsa ba yana iya cewa ke ce". Ta rufe littafin ta mike ba tare da ta ce dashi komi ba. Ta nufi hanyar fita, har ta kai bakin kofa ya ce, "Maryama". Ta juyo cikin damuwa, ya ce, "Ina fatan ba ranki ne ya baci ba?" Sai ta koma dariya, ta ce "A'ah Uncle". Ya ce "To mai yasa kika yi shiru?" Ta ce "Ka yi hakuri Uncle Junaidu". Ya yi murmushi ya bi

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66