Skip to content

Chapter 19

Chapter 19

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

motar ta yi mata wani banzan fakin a inda aka rubuta no parking, Security ne cikin fararen kayan ma'ikatan gurin tsaye jikin motar, wato sun kamata. Ya yi tsaki, tsut…, suka doshi wajen, har yanzu yana rike da hannunta, sai janta yake kamar kayan wanki. Ya mika hannu ya zare makullin ya soma ba su hakuri ya nuna musu Mairo ya ce ga dukkan alamu ba cikin nutsuwarta ta ke ba, su yi mishi uzuri su ba shi motar. Abinka da malam bature da bai san cin hanci da rashawa ba, gami da bin ka'ida da dokar duk da aka shimfida masa, kememe sun ki yarda, sun dage dole su dangana da ofishinsu in har suna son motar su, don a ka'ida mai matsala a kwakwalwa, ba a yarda ya tuka abin hawa ba, ya ce lafiyarta kalau, tension ne kawai, suka ce idan haka ne ke nan tana sane ta karya musu doka? Don haka dole su dangana da ofishinsu, amma ba zasu bada motar ba. Cikin matsanancin fushi, Habibu ya dubi Mairo "Kin kyauta, kin ga abin da kika jawo min ko? Yau shekaruna goma cur cikin kasar America, ban taba zuwa ofishin 'yan sanda ba, don haka sai ki bi su ku je, ki yi musu bayanin dalilinki na karya dokarsu, tunda ni kin yi min banza, sai ki je ku karata.......” Ya cika hannunta zai tafi, ta riko bayan rigarsa tana kuka. Ya ce "Wallahi bazan je ofishin 'yan sanda ba, sai dai ki hakura da motar, ki bar musu mu tafi, kuma wallahi-wallahi ba zan sake siyan wata ba". Ta ce ta yarda, don haka suka bar motar a nan, suka nufi motar Habibun. Allah Sarki, dan uwa rabin jiki! Sun yi nisa sosai danja ta tsaida su, ya saci kallon Mairo da ke kujerar gefensa, ya ga har yanzu kuka ta ke mara sauti, ta rufe fuska da mayafinta. Sai ya hadiye fushinsa, ya soma lallashinta cikin dabara. "Ni dai idan don na tambaye ki inda za ki ne kike min wannan kukan, to ki yi hakuri. Mantawa na yi, ashe fa Amiru ya fada min ba kya son tambaya. Ban da abinki Mairo, idan wajen Junaid kike son zuwa, jirgi ya tashi ya barki, ai sai ki fada mini, na yi miki booking din wani, amma ba ki sunkuya cikin dubban mutane kina rafka kuka ba, kamar wata mai tabin hankali. Yana ina Junaid din? Nigeria ko Russia?" Cikin kuka ta ce "Ni fa tunda na yi maka wancan alkawarin, ban sake tuna zancen Uncle Junaid ba". Ya ce "To ina za ki? Ko AMIRU kika biyo?" Hantar cikinta ta karta, ta rasa me zata ce masa, don haka ta ja bakinta ta yi shiru. Habibu ya kuta ya ce "Hakan da kike yi, kina ganin mutumci za ki sayawa kanki? Shi wancan bai ce yana sonki ba, sabida neman gindin zama kika kwashi jiki kika je gidansu don rashin hankali da rashin mafadi. Shi wannan da ya ce yana sonki, kin ce ba kya sonshi, sabida kar ki ci amanar wanda bai ce yana sonki ba. Ya hakura ya bar miki kasar ma baki daya ba garin ba. To uban me kika biyo shi ki mishi? Da kin same shin me za ki ce masa? Yi hakuri na tuba, ka zo ka aure ni ko me? To ni bana son rashin hankali da rashin mutunta kai, aikin zubar da kima, da wulakanta kai. Kin riga kin ce ba kya sonshi, to a barshi a hakan. Allah Ya kawo miki wanda kike so. Don wanda ya ce ba ya sonka tun farko, daga baya ya dawo ya ce yana sonka, to akwai dalilinshi na yin hakan. Wato za ki yi A RASHIN UWA... akan yi UWAR DAKI...? To ba da abokina ba! Idan auren kike so ki yi, ki je ki nemo Junaidun, tunda ba kya son karatun da nake sonki da shi. Abu na dan lokaci kalilan, ba zaki maida hankali akai ba, mazan nan da kike gani, dukkansu matsala ne, shi kansa auren idan ba a tsaya anyi shi cikin nutsuwa ba, babu inda ya ke zuwa. Don haka yarinya, kama kanki. Wayar ma daga yau ba zaki sake rikewa ba, kamar yadda babu ke babu tukin mota. To kin ji". Dai-dai lokacin da ya yi fakin a harabar gidansu, ya juya bayan motar ya dauko falmaran din suit' dinshi da wayoyinshi ya fito, ita ma ta fita, ba tare da ta yarda sun kara hada ido ba. Dina ta tari mijinta kamar yadda ta saba a kullum, amma ya sakar mata harara. Ya fincike jikinsa daga jikinta ya juya ya kara hararar Mairon da ke shigowa sumui-sumui kai a kasa, kamar wata munafuka, ya dawo da dubansa ga Dina. "Da saninki Mairo ta dauki mota ta tafi airport?" Dina ta yi shiru, ya ce "Magana nake, ko ke ma sullutun za ki mayar da ni ku barni na yi ta magana ni kadai?" Ta ce "To me ya faru?" "Ya zan tambaye ki kema ki tambaye ni? Amsa nake son ji kawai, kina sane ta tafi ko a'ah? Yanzu na je kai Amiru zai tashi zuwa Najeriya na ganta tana kuka akan titi uban me ta je yi?" Dina ta hau kame-kame ganin yadda ya hasala sosai, ta ce "Am... Eh, ai sako zata kai wa Amirun". A fusace ya ce "Sakon me?" Ta ce "Ka ga Allah ban sani ba, can tsakaninsu". Ya yi dogon tsaki, ji kake 'tsiiittt!' Ya maida kallonshi ga Mairo "Ba ni wayarki". Ta soma dube-dube a falon inda ta cillar da ita, can ta ganota bayan room heater, ta dauko ta mika mishi. Ya kashe ta gaba daya ya jefa a aljihun wandonsa da sassarfa ya nufi bangarenshi ya barsu nan tsaye cirko-cirko kamar an dasa su a wurin. Dina ba ta yi gigin binsa ba, don tasan halin kayanta sarai, idan ya yi fushi yana bukatar a daga mishi kafa, har sai ya sauko don kansa, wanda ba ya daukar dogon lokaci yake yin hakan. Ba ya son aje ana wani lallashin shi ko ace za a ba shi hakuri. Ta kama hannun Mairo suka nufi dakin Mairon suka zauna a bakin gado. Ta ce "Kin same shi?" Ta girgiza kai, wasu hawayen suka zubo. Dina ta sa yatsunta tana share mata, "Kada ki yi kuka Mairo, mika dukkan lamurranki ga Allah. Amiru yana sonki, na kuma tabbata zai dawo. Shi ma Junaid yana sonki, ina tabbatar miki da shi ma akwai ranar da zai zo. Allah kadai Ya san mijin ki a cikinsu, don haka ki dukufa ga neman ZABIN ALLAH ba zabin zuciyarki ba". Don haka Mairo ta tattara shawarwarin iyayen rikonta, wato masoyan nan nata guda biyu, da ba ta da ya su a duniya: Yaya Habibu, da Maidakinsa, Dina. Ta karbi shawarwarin su da hannu bibbiyu, ta fuskanci jarrabawar karshen shekara da ta tunkarota, wadda daga ita zata shiga shekara ta uku, kuma ta karshe da zata hada digiri dinta. *** A yau suna da tutorial class, kan wani kwas da zasu fara jarrabawa a kanshi. Mairo ta fi duk 'yan ajin su fahimtar wannan darasin, don haka suka bukaceta da ta yi musu karin bayani. Maryam Muhammad Bedi,

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66