Chapter 64
Chapter 64
gorar ruwa da tambulan cikin firij ya baiwa kowannen su. Aka rasa mai fara sha, aka rasa mai fara magana. Har shi kansa Baffan kuwa, kafin Junaid ya yi gyaran murya cike da tausayin Baban Amir da Habib da ya ke ratsa zuciyarsa. Da ganin wannan ‘giant’ kaga wanda ke fama da dingimemiyar soyayya, wadda ta rasa madafa. Yaran sun baibaye Uncle Junaidu sun kwanta a jikinsa. Ya ce, “Baffa na janye niyyata ta auren Maryama! Na hakura har ga Allah na barwa Baban Amir da Habib, ina bayan Maryama ta koma dakin mijinta uban ‘ya’yanta, don samun kwanciyar hankalin kowannen mu. Ba lallai sai na auri Mairo ba shi ne zan nuna ina kaunar ta, a’a, ni da Mairo mun wuce haka, Yaya ne da kanwarsa, alakarmu hadi ne daga Allah, ba don mu yi aure ba. Ina son ‘yan biyu su tashi gaban uwa da ubansu......kamar yadda Maryama ta tashi gaban Innarta da Babanta, ta san dadin iyaye, tasan amfanin su. Nikuma ina bukatar addu’arku Baffa, da fatan dorewar zumunci na har abada a tsakanin mu”. Baffa ya ce, “Allahu Akbar! Allahu akbar!! Wannan shi ne halin GIRMA, halin ‘yan aljannah!! Da gaske ne kai da Mairo kun fi karfin soyayyah!!! Sai ‘yan uwantaka, mun gode da wannan karamci Junaidu, Allah ya biya maka bukatunka na duniya da lahira, ya kara maka daukaka, ya baka duk abinda kakeso a duniya da lahira......”. Amiru ya cira kai ya tsura ma Junaid ido ya ce, “In aka yi hakan, ni kuma na so kaina.......”. Junaidu ya ce, “Ni kuma ba zan auri Mairo alhalin zuciyarta na ga tsohon mijinta ba”. Amiru yace “nayi rantsuwa da Allah! Mairo tayi maka son da ni bata yimin ba, na aure ta ba da son ranta ba, sai a hankali na koya mata soyayyata. Uncle Junaidu kana da matsayi mai girma a gun Mairo, wanda ni bani da shi.....” Junaid ya rausayar da kai cikin jin wani irin frin ciki a zuciyarsa, koda wannan ya tsira ya tabbata ya isheshi rayuwar duniya, yayi murmushi ya ce, “Kauna ce tsakanina da Mairo Amiru ba soyayyar aure ba tun daga ranar dana fara ganinta, a halin yanzu jin nauyin junanmu ya fi yawa, wanda da kyar za mu iya sakin jiki da juna mu yi rayuwar aure yadda ya kamata. Ka yarda ko kada ka yarda, kai Mairo take yiwa soyayyar aure....!” Amiru ya lumshe ido, ya ce, “Uncle Junaid, bani da bakin da zan gode maka....... bani da abin da zan biyaka wannan alfarmar da ka yi min.....” Uncle ya yi murmushi ya katseshi yace, “Kana dashi Amiru!. Mairo ta sha bani labarin soyayyar da kanwarka Amina take yi mata, wannan wadda suka zo mai kama da kai. Ta shaida min cewa maigidanta ya rasu. Ka bani Amina in aura Amiru, don wanzar da dauwamammen zumunci a tsakanin mu”. Cikin al’ajabi Amiru ya ce, “Amina is special a gare ni ko a cikin kannena goma sha biyu, lallai Amina is among the luckiest.... Na taba gayawa Habibu zan roke ka ka bar mini Mairo, ni kuma in baka kannena hudu ba lefe ba sadaki. Na fada ne kawai a fatar baki, ashe Mala’iku sun amsa. Uncle Allah ya kara GIRMA!”. Suka hade hannunsu suka cure kamar ba za su saki ba cike da wata shahararriyar kauna daga Allah, Baffa ya ja su doguwar addu’a suka shafa. Baffa ya ce, su barshi da Mairo, su ci gaba da shirye-shiryen su, yana so zai yi mata ba-zata ne. Suka yi murmushi. *** Kwana ta yi tana gwada lambar Uncle Junaid ba ta samu ba. Ta shiga damuwa sosai. Tsoron ta kada Allah yasa fushi ya yi saboda ganinta da ya yi tare da tsohon mijinta. Abu kamar wasa Uncle har kwana uku babu wayarshi babu kafarsa cikin gidanta, don haka ta yi tattaki har office amma ba ta same shi ba. Shima Amiru ko sallama bai zo ya yi mata ba, ya kwashe ‘ya’yansa ya tafi Abuja dasu ba ta kara jin duriyarsu ba. Da albishir mai dadi ya tari Alh. Abdurrahaman da Hajiya Aisha, ya kuma gaya musu bukatar V.C na auren Amina. Daddy da Hajiya suka yi ta hamdala tare da kara yawaita sadaka. Ko da Amir ya tuntubi Amina ya yi mamakin amincewar ta nan take. Bai san ita tunda ta dora ido a kan Junaidun ba ta kara gane kanta ba. Ya yiwa gidan Habibu tsinke a daren bakinshi ya kasa rufo, zumudin ya gaza boyuwa. Habibu ya dafa kafadarshi ya ce “Angon Harrit ya aka yi?” Ya harare shi ya ture hannunsa daga kafadunshi, ya ce, “Kai komi mai muhimmanci sai kasa iskanci da shakiyanci a cikinsa, to bani goro in baka albishir”. Ya ce, “To bari ina zuwa”. Ya fito jim kadan bayan shigarsa da kwalin ‘Aspen’ da ‘Lighter’, ya zari daya ya kunna ya manna mishi a baki. Da sauri ya ture ya bige hannunsa, tabar ta fadi, ya bi ya take da takalminsa, cikin takaici ya ce, “Wai don Allah Yaya Habibu, yaushe za ka girma ne?” Ya yi dariya ya ce, “Sai ranar da son Mairo ya daina kai ka hanyar lahira, ya daina kwantar da kai a asibiti, wato ranar da ka zama namijin duniya”. Dina ta yi dariya ta ce, “Rabu da shi Amiru, muna nan muna jiran nashi turn din, idan ya gano wata ‘yar kwailar. Irin su Habib ba ciwo suke a kan soyayya ba, rijiya suke fadawa dungurungum su kashe kansu in sun rasa samun wadda suke so....”. Ya ce, “Amma kin yanke ni ke da sirikinki bashi kuka ci, akwai ranar da zaku biya shi”. Amiru ya ce, “Na ma fasa baka albishir din, tunda da Taba za ka hadani, ka jawo min fushin Mairo, ban ji ba ban gani ba......”. Ya kamo hannunshi ya fizge, yana dariya ya ce, “Haba dear.... tuni na ji albishir din, ai Baffa ya gaya min komi yanzun nan, kun yiwa V.C Junaidu fin karfi kun toshe masa baki da Amina”. Ya yi dariya ya ce, “V.C mutum ne mai saukin kai, yadda na zaceshi ba haka yake ba, ya ji tausayinmu ya tallafi rayuwarmu shima Allah ya tallafesa. Bani da abin da zan biya shi wannan sadaukarwa da ya yi min koda na bashi my favourite sister. Wanda na san zai karba ne ba don so ba, sai don kulluwar zumunci a tsakaninmu”. **** Tana shirin fita office wayar Baffa ta shigo, da hanzari ta amsa cike da girmamawa. Bayan sun gaisa ya ce, “Kina gida ne yanzu?” Ta ce, “A’a, ina shirin fita ne zan ba da lacca 8-10”. Ya ce, “To in kin fito ki zo ina son ganin ki”. Ta ce, “Babu damuwa Baffa sai na iso”. Suka aje wayar a lokaci daya. Karfe goma na safe ta fito daga ‘twin-theater’ cikin rakiyar zugar dalibanta, wadanda suka riko mata jakar hannunta da takardunta har zuwa inda ta adana Terrain din ta, ta karbi kayan hannunsu suka yi sallama suka koma, ita kuma ta zaburo mota sai Yakasai gidan Alh. Abbas. Bayan sun gaisa da Habiba da Hajara da su Rahama, ta samu Baffa a falonsa, ya nuna mata waje ta zauna, ta zamo daga kujera ta dira gwiwoyinta a kasa ta gaida
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66