Skip to content

Chapter 34

Chapter 34

Abari Ya Huce Book One Complete Hausa Novel 1,206 words 0 views Progress saved
Download Book

daga kicin ya ce "Wai Dina ina kanwarkin nan ne?" Ta murmusa ta ce "Tana aiki ne". Tsam! Ya mike, kanshi tsaye ya doshi kicin din. Ta juya baya tana yayyanka fruits cikin wata katuwar silba, daga bakin kofa ya tsaya ya tokare hannunshi a kofar. Ya shagala sosai a cikin kallonta har ya manta abin da yake yi, bai san kuma iyakacin mintunan da ya bata a tsayen ba. Dina ta dawo ta ce "Ba ni hanya malam". Ya matsa, ta wuce ciki tana murmushi kasa-kasa, a sannan ne ma Mairon tasan da mutum a tsaye. Ta cira kai ta dube shi, shi ma duban nata yake cikin lumsassun idanunsa. Bai san me zai ce mata ba ta fahimci masifar sonta da Allah Ya dora masa. Yana daga cikin mutanen da harshensu bai iya bayyana abin da ke karkashin zuciyarsu. Sai dai action da emotion dinsu ya nuna. Da Mairon zata daure ta dube shi, da ta gane yadda ya yi laga-laga cikin SOYAYYAH. To amma ta ki, kallo daya ta yi mishi ta dauke kanta, bata sake marmarin maimaitawa ba. Ya karaso ya karbi wukar da ke hannunta ya ci gaba da yanka mata gwanda (paw-paw). Dina ta dau abinda zata dauka ta fita. Ta mika hannuwa cikin sink ta wanke hannu ta juya zata fita. Ya dago a galabaice, muryarshi har ba ta fita sosai, ya ce "Idan kika fita zan yi miki Allah Ya isa ne…, tunda Manzo ma ya ce, "BAKONKA, ANNABINKA..." Idan kika fita kin wulakanta ni, shin ma mene ne gare ni da kike guduna? Na yi miki kama da dodon da zai cinye ki ne?" Ta ja turus, ta tsaya, ita ba ta fita ba, ita ba ta juyo ba. Ya ajiye gwandar ya sha gabanta sosai har tana jin hucin numfashinsa. Wanda ke sauka da sauri-da-sauri. Kwayar idanun sun rikide, sun haukace da soyayya. Ban da alkawarin da ya daukarwa Habibu, da wallahi rungumeta zai yi, sannan ne yake jin zai iya gaya mata ko mene ne ke cin ransa, zuciyarsa da gangar jikinsa a kanta. Amma a haka ba zai iya bata bakinsa ba, ba zai iya ce mata komi ba. Da kyar ya daure ya langabar da kai, ya ce "Yi min magana mana, don Allah, Mairo? Mairo ko ba kya SO na?" Nan ma shiru, kai ka ce da gunki yake magana. Don ita jin abin ta yi banbarakwai, wai namiji da suna Hajara, tunda dai babu wanda ya taba tararta da wannan kalmar, wai….. Ya katse tunaninta da cewa, "Mairo Allah Ya jarrabce ni da sonki, tun daga lokacin da Allah Ya dora idanuna a kanki. Duk wani saukar numfashina a yanzu da sunanki yake fita, duk wani tunanina a yanzu na yadda zan mallake ki ne a matsayin matata, uwar 'ya'yana. Sunana Ameeru Abdurrahman Gaya, ni kadai ne da namiji a wurin iyayena, ina da kanne mata goma sha biyu. Na yi dukkan karatuna tare da Habibu. Iyayena ‘yan Gaya ne suna zaune a Abuja, amma mu 'yan asalin garin Gaya ne da ke cikin jihar Kano, ina aiki a Washington, sai dai kwanan nan zan bari in koma gida. Ina da mace daya da 'ya'ya zero. Duk wani abu da kike son ji game da ni, ki tambayi Habibu, zan samu karbuwa Mairo? Mairo ko ba kya so na?" Ya tsare ta da wani irin kallo daga can karkashin kasan lumsassun idanunsa. Mairo ta rasa inda zata sa kanta. Ga kunya da ta baibaye ta, ga jin nauyi, don ganinshi ta ke kamar Yaya Habibu. Idan ta ce ba ta sonshi ta yaudari zuciyarta, haka idan ta ce tana sonshi ta yi karya. Mutum daya ta ke wa 'SO' na hakika, wato UNCLE JUNAIDU. To amma shi wannan jinsa ta ke har cikin kasusuwa da bargonta ba zuciya kadai ba, da wani al'amari mai ban mamaki da ba zata iya fassarawa ba. Tunaninta shi ne, ba zata iya hada rayuwarta da kowa ba, idan ba Uncle Junaid ba. Ta dauki al'amarin da ta ke ji akan Amiru da BURGEWA da SHA'AWA, wato yana burge ta, yana bata sha'awa, yana daukar hankalinta, yana bijiro mata da sha'awar tayi aure. Zata iya aurenshi don ta mallaki gangar jikinshi, amma ba don so ba. Idan aure ne kadai hanyar da zata samu mallakar abin da zuciyarta da gangar jikinta ke so daga gare shi, to zata iya aurenshi don ta samu, amma SO guda daya na UNCLE JUNAIDU ne! Wata irin kunya ta kamata, da ta yi wannan tunanin, don gani ta ke kamar ya hango abin da ta ke sakawa da warwarewa cikin zuciyarta. Tana tunanin idan ta yi hakan kuma ai ya zama yaudara. babbar yaudara kuwa, don haka ta soma tunanin yadda zata yi ta gudu, ba tare da ta ce da shi komai ba. Yadda Uncle Junaid ya yaudare ta, ta san ciwon hakan, ko ba don komi ba don amintarsu da Yaya Habibu da mutumcin da ke tsakaninsu kamar yadda Yaya Habibu ya gaya mata, mahaifin Amiru shi ya dauki nauyin karatunsa daga masters har PhD. Sabida haka ba yadda za a yi ta yaudari Amiru wata rana ta rabu da shi idan ta samu Uncle Junaidu. Haka nan idan ta ce ta yarda tana sonsa ita ma ta yi sallama da burinta na WATA RANA zata hadu da Uncle Junaid su yi aure a lokacin da Allah Ya nufa. Gara ta ci gaba da dakon soyayyarsa, don idan ta yi aure ya tabbata ita da Junaid kenan HAR ABADA! BURGEWA da SHA'AWA ba tubala ne na kwarai da za a gina aure a kansu ba. Idan aka yi hakan, ba da jimawa ba ginin zai rushe tamkar ba a taba ginawa ba. Don haka gara ta hakura da rudin zuciya don shaidaniya ce, ta fuskanci gaskiya. Ta yi aure don Allah, ba don kyale-kyalen Amiru da rayuwa bakidaya ba. Ta ci gaba da jiran Uncle ya gaya mata da bakinsa cewa ba sonta yake ba, sannan ne zata hakura, ta yi addu'ar Allah Ya kawo mata mijin da zata so da gaskiya, ta kaunata saboda Allah, kamar yadda ta ke yi wa Junaidu. Ta daga kai a hankali ta dubi Amiru, wanda har zuwa wannan lokacin bai dauke kyawawan idanunshi daga kanta ba, binta yake da ido, da zuciya. Idan Mairo ta ce ba ta sonshi, bai san inda zai sa kanshi ba. Ta ce (cikin kaskantacciyar murya) "Don Allah ka ba ni hanya in wuce". Ya ce "Ai ba ki ba ni amsa ba, ko na yi miki tsufa ne Mairo?" "Ni ban ce ba". "To mai kika ce?" "Cewa na yi ni ba sonka nake yi ba!". Wannan ita ce kalma mafi muni da wani ya taba gaya mishi a rayuwarshi. Ji ya yi kamar ta soka mishi mashi a kahon zucci. Hajijiya ta kamashi. Ta wani fannin kuma sai ta BURGE shi, sabida kai tsaye ta gaya mishi kalmar da babu wata diya mace da ta taba gaya mishi. Wannan ya tabbatar mishi da cewa, ita ta daban ce. Sai dai yadda ta yi maganar da yanayinta kadai zai nuna maka tsabar kuruciyarta karara. Don haka bai yi fushi ba, ance wai, 'Mai nema yana tare da samu'. Ya

Table of Contents

Chapters

66 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66